Nakan noma shinkafa buhu 6,000 a shekara —Sarauniyar Noman Taraba

Hajiya Adama Abubakar Sarauniyar Noman Taraba babbar manomiya ce a Jihar Taraba. Takan noma shinkafa fiye da buhu dubu shida duk shekara, baya ga wasu kayan amfanin gona da take nomawa. A tattaunawarta da Aminiya, ta bayyana yadda ta fara noma sama da shekara 28 da suka gabata da kuma yadda take samun nasara a […]

Nakan noma shinkafa buhu 6,000 a shekara —Sarauniyar Noman Taraba

Manoman shinkafa sun yi asara sakamakon ambaliya a gonakinsu

Hajiya Adama Abubakar Sarauniyar Noman Taraba babbar manomiya ce a Jihar Taraba. Takan noma shinkafa fiye da buhu dubu shida duk shekara, baya ga wasu kayan amfanin gona da take nomawa. A tattaunawarta da Aminiya, ta bayyana yadda ta fara noma sama da shekara 28 da suka gabata da kuma yadda take samun nasara a sana’ar.

 

Mene ne takaitaccen tarihinki?

Cikakken sunana Hajiya Adama Abubakar, kuma ana yi mini lakabi da ‘Matar Wata’.
Kuma an haife ni ne a nan garin Jalingo a 1955 – yanzu ina da shekara 65 a duniya.

 

A nan Jihar Taraba kusan dukkan manoma maza da mata ba wanda ya kama kafarki ta fuskar noma. Yaya aka yi kika shiga sana’ar noma?

Ni na fara sana’ar noma yau kimanin shekara 28 ke nan da suka gabata. Kuma na gaji mahaifina ne a wannan sana’a ta noma, domin kuwa mahaifina Abubakar Baban Ali; a zamaninsa ya kasance babban manomi a nan garin Jalingo. Kuma ni kadai ce daga cikin ’ya’yansa na gaje shi ta fuskar noma.

Na soma noma ne a wani kauye mai suna Goggo Ibi. Wani al’amari da na fuskanta, lokacin da na fara sana’ar noma sai da na kwashe shekara uku ina noma amma ban ci riba ba. Sai a shekara ta hudu ce na fara samun haske a wannan sana’a, wato na fara samun riba.

 

Ga shi ke matar aure ce amma kina noma, yaya kike hada zaman gidan aure da aikin gona, musamman da yake gonakinki a wajen gari suke?

Wannan abu ne mai sauki muddin akwai fahimta da yarda tsakanin miji da mata. Maigidana ya ba ni dukkan goyon bayan da nake bukata, wanda hakan ya taimaka mini matuka wajen gudanar da sana’ata ta noma.

Kamar yadda na fadi, shekara uku na farkon soma noma ban samu riba ba, sai a shekara ta hudu. Kuma da farko hayar gonar nake karba daga wurin masu filayen noma. Amma daga bisani da na soma samun haske sai na soma sayen gonaki, wato na soma mallakar gonakina na kaina.

 

A ina ne gonakin naki suke a yanzu?

Ina da babbar gona a Goggo Ibi, a hanyar Tau kusa da gonar Al-Illah. Kuma akwai wasu kananan gonakina, duk a wannan hanya ta zuwa Tau, a can Goggo Ibi. Wannan yankin a can baya yana karkashin Karamar Hukumar Jalingo ce amma yanzu yana karkashin Karamar Hukumar Ardo-Kola ce.

A babbar gonar tawa wadda take a Goggo Ibi, ina shuka buhun shinkafa 160 a lokaci daya. Kuma a cikin gonar ita kadai, ina samun buhu dubu biyar zuwa dubu shida na shinkafa a duk shekara.

Ka san a nan ba shuka shinkafa ake yi ba, yafawa ake yi wato bayan an yi kaftu, an yi haro sai a fesa maganin kwari. To bayan wannan sai a jira yankan shinkafar, domin maganin ciyawa da aka fesa shi ne zai kashe dukkan ciyawa; sai a bar shinkafa kawai a gonar.

 

Kina amfani da kayan noma na zamani kamar tarakta da injin shuka da girbi ne wajen ayyukanki ko a gargajiyance kike noman?

Ba na amfani da injin shuka ko na girbi amma ina amfani da tarakta. Sai dai kuma su ma taraktocin da suke yi mini aiki a gona ba nawa ba ne, haya nake dauka.

Ashekarun baya na mallaki taraktoci biyu amma saboda yawan matsalar gyara da halayen direbobin tarakta sai na sayar da su baki daya, na ci gaba da daukar haya, ana yi mini aiki ina biya.

Akwai leburori wato ’yan kwadogo sama da mutum 500, wadanda ke aiki a gonata, musamman masu aikin shuka da zuba taki a gonakin da suke bukatar taki. Sauran ayyukan sun hada da yankar shinkafa tare da tarawa da bugun shinkafar da durawa a buhu da sauran ayyuka daban-daban da ake bukata.

A cikin wadanda suke aiki a gonata akwai mata 30, wadanda aikinsu shi ne shika. Wato idan an buga shinkafar sai su sheke ta kafin a dura a buhuna.

 

Bayan shinkafa wadanne kayan gona kike nomawa?

Ina noma masara da ridi da agushi da gyada da wake. Sai dai ba na noma wadannan da yawa, na fi noma shinkafa da yawa kuma ba na aikin noman rani domin akwai wahalar gaske.

 

Yaya kike adana kayan gonarki kafin ki kai kasuwa, ganin cewa kina noma shinkafa sama da buhu dubu shida?

Ina da dakunan ajiye amfanin gona kanana da manya kuma kwanan nan na sayi wani fili a garin Wuro Sanbe kan Naira miliyan hudu da rabi domin gina manyan dakunan ajiye amfanin gona, amma ban samu damar gina dakunan ba tukunna.

 

Kin taba karbar rancen kudi daga banki don aikinki na noma, kuma ko gwamnatin jiha ko ta tarayya ta taba ba ki wani taimako don bunkasa sana’arki?

Ban tava karbar rancen kudi ko kayan aikin gona daga banki ko hannun wani ba tun da na soma gudanar da wannan sana’a ta noma.

Na farko dalilin da ya hana ni karbar rance daga banki shi ne, mahaifina ya taba karbar rancen kudin noma da tarakta a lokacin mulkin marigayi Shugaban Kasa Alhaji Shehu Shagari amma daga baya abin ya zama matsala.

A wancan lokacin rancen da iyayenmu suka karba bai wuce Naira dubu shida zuwa goma ba, amma bayan mulkin Shagari dole suka biya daruruwan dubban Nairori. Wadansu wadanda ba su da kudi dole suka sayar da gidajensu ko gonakinsu a dalilin kudin ruwa da ke cikin rancen, wanda iyayenmu ba su da masaniya a kai.

Na biyu, ka san yanzu akwai sama da mata dubu goma wadanda ke gudanar da aikin noma a nan Jihar Taraba. Wadannan matan sai suka neme ni in tsaya musu a kan bashi na kungiyar masu noman shinkafa saboda matsayina na babbar mai noman shinkafa.

Sai aka amince aka ba su amma da lokacin biya ya yi sai wadanda suka karbi bashin suka noke, suka ki biya. Rashin biyan bashin da mata manoman shinkafa suka yi, wannan ya kara sa ni tsoron karba ko tsaya wa wani ya karbi bashin aikin noma.

 

A halin da ake ciki na rashin tsaro, kikan je gona don duba aiki?

Yanzu zuwa gona ba zai yiwu ba, akwai hadari. Tun lokacin da matsalar sace mutane ta yi yawa a jihar nan na daina kai-kawo a gonakina. Illa kawai na dogara ne ga masu yi mini aiki a gonakin kuma na yi sa’a suna rike mini amana, domin ba na samun wata matsala ta cin amana sai dai abin da ba a rasa ba.

 

Kin taba samun wata lambar girmamawa kan gudunmawar da kike bayarwa ta ciyar da kasa da abinci?

A can baya ba, wanda ya san matsayina cewa ina cikin manyan manoman shinkafa a wannan jihar. Sai a wata shekara da aka shirya taron manoman shinkafa na kasa a garin Minna a Jihar Neja.

A lokacin wannan taro an yi tambayoyi masu yawan gaske kan dabarun noman shinkafa amma saboda yadda na amsa tambayoyin sai wadanda suka shirya taron suka nemi su ziyarci gonata.

Jami’in noma na Gwamnatin Tarayya da wasu daga wata cibaya ta binciken noman shinkafa daga bisani sun zo Jalingo, suka je gonata.

Wadannan jami’an sun yi kwanaki sama da biyar suna ziyarar gonakina. Bayan komawarsu Abuja ne aka turo min wata takarda ta yabo kan kokarina na samar da abinci, musamman shinkafa.

Bayan wannan kuma an nada ni a matsayin Sauraniyar Noma ta Jihar Taraba, sannan kuma aka zabe ni a matsayin Shugabar Kungiyar Masu Sayar da Shinkafa.

 

Yaya kike sayar da shinkafar da kike nomawa?

Yanzu noman shinkafa yana da riba domin akwai masu neman shinkafa, musamman kamfanonin da suke sarrafa shinkafar. Akwai farashi mai kyau kuma saboda yawan shinkafar da ake nomawa a wannan jihar, masu sayen shinkafa daga ko’ina a kasar nan suna zuwa sayen shinkafa rani da damina.

 

Maganar iyali fa, ’ya’yanki nawa kuma ko suna sana’ar noma kamar yadda kike yi?

Ina da ’ya’ya shida, hudu maza biyu mata amma dukkansu suna makaranta kuma a yanzu ba wanda ya soma gudanar da sana’ar noma.

Ba mu yanke hukunci kan ƙudirin harajin Tinubu ba — Abbas

Masu garkuwa da mutane na neman N10m kan manoma 6 a Taraba

Hotunan Gobarar Kasuwar Laranto da ke Jos

Kasuwar Laranto da ke Jos ta yi gobara