Nakasasshen Ba’indiye ya samu tarin dukiya a wajen rawa
Wani nakasasshen Ba’indiye, dan shekara 23, mai suna binod Thakur, mai dungulmin kafa ya shahara a rawa har ta haifar masa da dimbin arzikin, inda ya zama miliyoniya, ya kuma samu matar aure. binod Thakur, ya bayyana wa manema labarai yadda rawa ta samar masa dukiya da soyayyar budurwa da farin cikin rayuwa, kamar yadda […]
Wani nakasasshen Ba’indiye, dan shekara 23, mai suna binod Thakur, mai dungulmin kafa ya shahara a rawa har ta haifar masa da dimbin arzikin, inda ya zama miliyoniya, ya kuma samu matar aure. binod Thakur, ya bayyana wa manema labarai yadda rawa ta samar masa dukiya da soyayyar budurwa da farin cikin rayuwa, kamar yadda jaridar Gulfnews ta ruwaito.
binod, wanda ke cike da fara’a da murmushi, yak an kaga hannuns ana dama, sannan ya tsaya akan daya hannu (na hagu), ya rika daga wa taron jama’ar da ke kallonsa hannu. Daga sai kawai a gay a fara taka rawar bam mamaki da juyi iri-iri, har ma ya kan taka matattakala, a lokacin da yake bin salon kida.
Irin wannan juyin rawa yana motsa taron jama’ar da ke kallonsa, har su rude da shewa. Duk da haka a wani lokaci irin wannan juyin da yakan yi wai duk somin tabi ne.
Har yanzu na kasa gaskata irin daukakar da na samu,” a cewar wannan mai dungulmin kafa, mazaunin birnin New Delhi, lokacin da ya kammala wani wasa a babban birnin Indiya. “al’amarin na da rikitarwa. Domin shkarun da suka gabata, na kasa mallakar Rupees dubu. A halin yanzu ni miloniya ne.”
binod ya yi tari a asusun ajiyarsa na banki. “Ina da gida mai ban sha’awa, na auri matar da nike kauna, sannan ina zagaya duniya,” inji shi.
A cewar binod, ya tashi a birnin Bihar, sannan ya koma Delhi tare da iyayensa, amma bai taba zaton zai taka rawa tare da shahararrun ’yan wasa ba, domin an haife sh ba tare da kafafuwa ba.
“Iyayena suna cikin dmauwa, don tunaninsu ba zan iya tabuka komai ba,” a cewarsa, tunda mahaifina Raj direban tirela ne, mahaifiyata kuwa Urmila, ’yar shekara 46, mai zaman gida ce, tare da ’yar uwata Reema ’yar shekara 17, duk muna cunkushe a gida mai daki guda a birnin Delhi. Don haka binod ya jajirce wajen fafatawa da mkatslaolin rayuwa.
A shekarar 2012, binod ya tara iosassun kudin bue makarantar rawa, wadda ya yi lakabi da ‘binod Thakur Dance Academy,’ wadda ya kafa a kusa da gidansu da ke Delhi. “Na auri harkar koyar da rawa. Domin ba ni da lokacin amce ko aure. Na jajirce wajen rawa da harkokin kasuwancina,” inji shi. Sai dai wanioa bin mamaki, bayan wata guda da furta waccan magana ta rashi kula mata, ko maganar aure, sai na hadu da wata yarinya ’yar shekara 19, mai suna Raksha Rathore, wadda muka yi soyayya da ita, har muka yi aure. Da farko iyayena sun ki amincewa, domin a tunaninsu, ko wannan budurwa za ta yi amfani da sunana ne, ta samu daukakar darajar,. Musamman ganin cewa ni ba ni da kafa.