Nakasassu sun bukaci Buhari ya kula da su

An yi kira ga zababben Shugaban kasa Janar Muhammadu Buhari da ya bai wa bangaren nakasassun kasar nan kulawa. Wanann kira ya fito daga Shugaban Asusun Kula da samar wa Nakasassun Ilimi a Jihar Kano, Malam Abba Sarki Sharada. Abba Sarki ya bayyana cewa akwai bukatar Gwamnatin Tarayya ta bayar da muhimmanci ga harkar kulawa […]

Nakasassu sun bukaci Buhari ya kula da su
Nakasassu sun bukaci Buhari ya kula da su

An yi kira ga zababben Shugaban kasa Janar Muhammadu Buhari da ya bai wa bangaren nakasassun kasar nan kulawa. Wanann kira ya fito daga Shugaban Asusun Kula da samar wa Nakasassun Ilimi a Jihar Kano, Malam Abba Sarki Sharada.

Abba Sarki ya bayyana cewa akwai bukatar Gwamnatin Tarayya ta bayar da muhimmanci ga harkar kulawa da nakasassu: “Nakasassu suna neman kulawa ta musamman daga Gwamnatin Tarayya game da abin da ya shafi ilimi da lafiya da sana’o’i da sauran banagarorin rayuwa. Idan ma ba a ware wata ma’aikata ta musamamn don kulawa da su ba, to zai yi kyau a sama musu wani gurbi ko da a ofishin uwargidan Shuagaban kasa ne wanda zai kula da hakan. Kasancewar mata suna da zuciyar tausayi da taimakon mun tabbatar za a samu kulawa daga gare su. Daga nan kuma a dangana har zuwa sauran ofisoshin matan gwamnoni da ke fadin jihohin kasar nan,” inji shi.
Shugaban ya yaba wa kudurin dokar da ‘yan majalisa suka yi game da hana ware makarantun nakasassu daban . “Duk da cewa a kwanakin baya Majalisar Wakilai ta Tarayya ta yi doka cewa a daina ware wa nakasassu makarantun daban, amma akwai bukatar a duba wasu abubuwa kafin hakan ya tabbata, misali akwai bukatar a duba yanayin makarantun, domin za ka samu yanayin ajujuwansu a bene yake, to ka ga ta yaya za a yi a ce gurgu zai iya yin karatu a bene? Haka kuma akwai bukatar a yi doka game da yanayin daukar aiki kamar yadda Mjalisar dinkin Duniya ta yi kira cewa ya kamata nakasassu su sami kashi biyar na daukar aiki a dukkanin ma’aikatun gwamnati,” inji shi.
Har ila yau ya yi kira ga sabuwar gwamantin Jihar Kano da ta cika alkawuran da gwamnatin baya ta dauka na kyautata tare da inganta rayuwar nakasassu. “Lokacin da gwamnatin Jihar Kano ta kafa dokar hana bara ta yi alkawari da dama gare mu don kyautata rayuwarsu; alkawuran da suka hada da ba mu alawus na Naira dubu 10 da sama mana da sana’o’i don dogaro da kansu, sai dai har zuwa yanzu ba a samu tabbatuwar hakan ba. Don haka muna yi wa gwamnati tuni da ta taimaka ta dubi lamurarn nakasassu. Haka kuma idan an zo batun koya musu sana’ao’i a duba a sama musu sana’o’in da za su iya gudanarwa wanda za su kawo musu riba mai dan kauri. Yanzu idan ka dauki sayar da katin waya za ka ga babu wata ribar kirki a ciki,” inji shi.