Namadi ba zai gaje ni ba – Jonathan

Shugaban kasa Dokta Goodluck Jonathan ya yanke shawarar da ke nuna cewa ba zai yiwu Mataimakin Shugaba kasa Namadi Sambo ya gaje shi ba. Shugaba Jonathan ya bayyana cewa Shugaban kasa na gaba da Jam’iyyar PDP za ta fitar zai kasance ne dan kasa da shekara 60. Mataimakin Namadi Sambo dai ya riga ya haura […]

Namadi ba zai gaje ni ba – Jonathan
Namadi ba zai gaje ni ba – Jonathan

Shugaban kasa Dokta Goodluck Jonathan ya yanke shawarar da ke nuna cewa ba zai yiwu Mataimakin Shugaba kasa Namadi Sambo ya gaje shi ba.

Shugaba Jonathan ya bayyana cewa Shugaban kasa na gaba da Jam’iyyar PDP za ta fitar zai kasance ne dan kasa da shekara 60. Mataimakin Namadi Sambo dai ya riga ya haura shekar 60 a yanzu haka.
Idan za a iya tunawa batun wanda zai gaji Shugaban kasa na daga cikin abin da ya haddasa takaddama a tsakanin Shugaba Obasanjo da Mataimkinsa Atiku Abubakar a baya, lamarin da ya haifar da gaba a tsakaninsu na tsawon lokaci.
A ranar Talata ne Shugaba Jonathan ya yi wannan furuci; a daidai lokacin da jam’iyyarsa ke kokarin fuskantar kalubale daga babbar jam’iyyar adawa ta APC.
Jonathan wanda ke jawabi ga dimbin jama’a a filin wasa na Lafiya a Jihar Nasarawa wajen kamfe dinsa ya ce, gwamnatinsa tana da imani a kan matasa, kuma za ta yi duk abin da za ta iya wajen goya wa matasan baya.
Ya ce: “Obasanjo ya zama Shugaban kasa yana da shekara 70, ’Yar’aduwa kuma yana da shekara 60, ni kuma ina daf da kaiwa shekara 60, don haka Shugaban kasa na gaba wajibi ne ya zamo bai kai ni shekaru ba.”
Da wannan kalami ne ake ganin ya kulle kofar tsayawa takara ga Mataimakinsa Namadi Sambo wanda ya shiga shekara ta 61 a bana.
Shugaba Jonathan ya ce gwamnatin PDP za ta zuba jari kan matasa tare da tabbatar da an ba su dama a nan gaba. Ya bayyana cewa gwamnatinsa tana bayar da muhimmanci kan inganta ilimi wanda shi ne kashin bayan ci gaban matasa.
Shugaban kasar ya yi ta nanata batun karfafa wa matasa, inda ya cehakan zai zamo ginshikin gwamnatinsa idan aka sake zabarsa.