Namadi Sambo ya yi rawar gani

Masu lura da harkokin yau da kullum masu yawa a kasar nan, sun amince da cewa mataimakin shugaban kasa, Alhaji Muhammadu Namadi Sambo, ya yi rawar gani wajen iya murza zaren mu’amala da zamansa da shugaban kasa, Dokta Ebele Goodluck Azikiwe Jonathan. Masu bin diddigin irin zaman da ake yi tsakanin shugaban kasar da mataimakinsa […]

Namadi Sambo ya yi rawar gani
Namadi Sambo ya yi rawar gani

Masu lura da harkokin yau da kullum masu yawa a kasar nan, sun amince da cewa mataimakin shugaban kasa, Alhaji Muhammadu Namadi Sambo, ya yi rawar gani wajen iya murza zaren mu’amala da zamansa da shugaban kasa, Dokta Ebele Goodluck Azikiwe Jonathan.
Masu bin diddigin irin zaman da ake yi tsakanin shugaban kasar da mataimakinsa kan yi nuni da cewa tun daga lokacin da aka rantsar da su domin jan ragamar mulkin kasar nan kawo ya zuwa yanzu, ba a ga alamun gintsirmi ko sabani a tsakaninsu ba.
Zaman lafiya da iya burminsu, ba tare da tangarda ba, ya sa yanzu haka wadansu gaggan ‘yan siyasa suke kwadayin kujerar mataimakin shugana kasar, watau suna yunkurin yin kutungwila da kafar ungulu da kulle-kulle iri-iri da nufin  shiga tsakanin shugaban da mataimakinsa.  Burin wadannan ‘yan siyasa shi ne, su aibanta mataimakin shugaban kasar a idon shugaba Goodluck Jonathan, domin a cire shi, a dauki daya daga cikinsu ya haye kujerarsa.
Masu yin wannan yankan baya sun mance da wasu muhimman abubuwa, ciki har da fadar Allah Mai girma da daukaka cewa mulki naSa ne, kuma Shi ke bada shi ga wanda Ya so, a sanda Ya so. A takaice dai, da sun yi cikakken imani da wannan, kuma sun tsaya a kan hakan, da ba su shiga neman bata sunan wani bawan Allah ba, domin kurum su raba shi da baiwar da Allah Ya yi masa.
Wani abin ban sha’awa shi ne, kowa ya san  shi dai Muhammadu Namadi Sambo bai bata sunan wani ba da nufin Shugaba Goodluck Jonathan ya kira shi, domin su yi wannan tafiya tare a mukamin mataimakinsa. Ya yaba halayen Muhamadu Namadin ne, domin sun saba, sun fahimci juna, kuma shi Goodluck Jonathan ya lura da nagartar Muhammadu Namdin ne tun lokacin da yake Gwamnan Jihar Kaduna.
Bayan ya zama mataimakin shugaban kasar, Alhaji Muhammadu Namadi Sambo ya kasance wakilin mutanen Arewa na gari, domin ya zama mai biyayya da kana’a da juriyar aiki da kwarewa wajen mu’amala da jama’ar kasar nan wadanda suka fito daga yankunanta daban-daban.
Masana tarihin siyasa a kasar nan kan ce rabon da a ga shugaban kasa da mataimakinsa suna aiki tare ba tare da wata tangarda ba kamar yanzu, tun lokacin zamanin shugaban kasa Alhaji Shehu Usman Aliyu Shagari da mataimakinsa  Dokta Aled Ekwueme. A wancan lokacin, watau tsakanin 1979 da 1983, ba a taba jin kansu ba, kome yana tafiya ba tare da bangon mulkinsu ya tsage ba, balle ‘yan bani-na-iya su sami kafar shirya musu makirci.  
A yanzun ma zaman lafiyar da ke tsakanin shugaban kasar da mataimakinsa na yanzu, ya kai ingancin da masu shirya wa Alhaji Muhammadu Namadi Sambo makirci da yarfen siyasa iri daban daban, ba za su ci nasara ba. Shi dai ya sami shaidar cewa ba ya bin kowa da mugun nufi.  Yana zaman lafiya da zuciya daya da kowa, kamar dai yadda aka san  dattawa a arewa.  Masu iya Magana a  kasar nan kan ce farar aniya laya. Farar aniyar Muhammadu Namadi Sambo ta zama abin misali. Wannan ne ma ya sa sharrin masu kwadayin kujerarsa ta mataimakin shugaban kasa, ba zai tauye masa kima ko daraja a idon shugaban kasa da sauran jama’ar kasar ba, balle har su ji kanshin biyan bukatarsu. Shugaba Goodluck Jonathan ya gamsu da biyayyar da yake yi masa a harkokin mulkin kasa, da kwazon da ya kan nuna wajen aikata  ayyukan da za su inganta rayuwar kowa da kowa.
Ganin yadda yake yi masa biyayya, sai shi kuma shugaba Goodluck Ebele Jonathan ya  tabbatar mataimakin nasa yana kula da aiwatar da wasu muhimman ayyukan raya kasa.  Misali, mataimakin shugaban kasar ne shugaban wani kwamiti da zai assasa dasa miliyoyin bishiyoyi a arewacin kasar domin rage kwararowar Hamada a jihohin Arewa. Jihohin su ne na Kebbi da Sakkwato da Zamfara da Katsina da Kano da Yobe da Borno da Adamawa da Taraba da Bauci da Kaduna da Jigawa.
Wani babban aiki da mataimakin shugaban kasa Alhaji Muhammadu Namadi Sambo ke kula da shi, shi ne na bunkasa makarantun allo.  Aikin ya hada da gina wa almajirai makarantun koyon ilmin addinin Musulunci, amma tare da kowa musu  sana’o’in da ke tafiya tare da ilmin boko.  Manufar haka shine wata rana irin wadannan almajirai su zama likitoci ko injinonyin da za su gina wa jama’armu hanyoyi da gadoji da gidajen ruwa da tuka jiragen sama da kera motoci da sauran fannonin kyautata rayuwa.  Ta haka za a  dama da su ke nan wajen raya kasa. A takaice dai, za su ci tudu biyu, ga ilmin ibada ga Allah da mu’amala mafi kyau da sauran talikai, ga kuma ilmin sana’o’I’n zamani.
Mataimakin shugaban kasa yana da damar ba shugaban kasa shawarwarin da za su kawo wa kasarmu zaman lafiya da kwanciyar hankali.  Kowa ya san shi ne ya kawo aikin tsaron nan mai suna  “Operations Yaki,” inda ya hana masu tada fitina da  sace-sace sakat a jihar Kaduna.
A takaice, zamansu wanda ke tafiya cikin  fahimtar juna da girmama juna ya sa duk masu kulle-kullen ganin an cire Alhaji Muhammadu Namadi Sambo daga aikinsa a maye gurbinsa da daya daga cikinsu, zai kare ne tamkar jiran gawon shanu.   
Fatana a nan shi ne, Allah Ya kara kare mataimakin shugaban kasa Muhammadu Namadi Sambo daga fitinu da makirci da yankan ciki da yankan baya irin na masu hassada da ganin kyashi.

Matsalar Tsaro: Dole mu faɗakar da mutane yadda za su kare kansu – ACF

Majalisa ta buƙaci sojoji su kawo ƙarshen Lakurawa

Ɗan Aljeriya ya shiga hannu kan safarar makamai a Zamfara

’Yan bindiga sun kashe ’yan banga sun sace mai unguwa a Kaduna