Namadi ya kaddamar da sabbin jiragen kasa a Legas
Gwamnatin tarayya ta kaddamar da jiragen kasa da taragai 60 masu na’ura mai sanyaya daki a Ikko, wadanda za su rika aiki cikin birnin da kuma wanda zai rika zuwa Kano.Da yake jawabi wajen kaddamar da jiragen, mataimakin shugaban kasa, Akitek Namadi Sambo ya ce yana fata nan ba da jimawa ba gwamnati za ta […]
Gwamnatin tarayya ta kaddamar da jiragen kasa da taragai 60 masu na’ura mai sanyaya daki a Ikko, wadanda za su rika aiki cikin birnin da kuma wanda zai rika zuwa Kano.
Da yake jawabi wajen kaddamar da jiragen, mataimakin shugaban kasa, Akitek Namadi Sambo ya ce yana fata nan ba da jimawa ba gwamnati za ta samu damar karo jiragen domin ingata harkokin sufuri a cikin kasa, lamarin da zai kara inganta hanyoyin motoci a duk fadin tarayyar Najeriya.
Mataikmakin shugaban kasa ya ce yana fata ’yan Najeriya za su kula da jiragen tamkar nasu kuma za a yi amfani da su ta yadda ya dace.
Shi ma ministan sufuri, Sanata Idris Umar ya ce baya ga jiragen, wadanda sun yi daidai da duk wani jirgin kasa da za a iya amfani duk duniya, gwamnati ta kusan kammala gyara daukacin hanyoyin jirgin kasa da ke fadin tarayyar Najeriya.
Shi ko manajan darekatan hukumar, Injiniya Sijuwade ya ce yana taya ’yan Najeriya murnar samun wadannan jiragen kuma fatarsa ita ce a samu a kara sawo wasu. Ya ba ’yan Najeriya tabbacin hukumarsa za ta kula da su yadda ya dace, kodayake ya bukaci taimakon ’yan Najeriya a kan haka.
Jim kadan da kaddamarwar, mataimakin shugaban kasa da minista da sauran manyan jami’an gwamnati sun shiga jirgi guda, wanda zai yi aiki cikin Legas daga tashar Iddo terminus zuwa Ikeja, inda daga nan ne mataimakin shugaban kasa ya koma Abuja.