Namando bai san bihim ba
Tun a karshen makon da ya arce, na ga dimbin masu watsattsake da buda wagagen litttattafai na bai wa Haurobiyawa shawarar yin na-damo, don kada su tayar da yamutsi saboda takaicin kara wa’adin zabi-sonka, ni ma sai na ga ya dace in hori ’yan makaranta da ma gungun man kaza da ke wasan kasa a […]
Tun a karshen makon da ya arce, na ga dimbin masu watsattsake da buda wagagen litttattafai na bai wa Haurobiyawa shawarar yin na-damo, don kada su tayar da yamutsi saboda takaicin kara wa’adin zabi-sonka, ni ma sai na ga ya dace in hori ’yan makaranta da ma gungun man kaza da ke wasan kasa a bayan kangon GizBaba, kan lallai su tsaya su yi karatun wasikun jakin-dawa da na gida a cikin tsanaki. Ba ni da ko tantama, na san Haurobiyawa na bukatar sauyi a rayuwarsu, amma duk sa’adda na bijiro da irin wannan batu na kan ja na-zomon ’yan makaranta da cewa, ka da ku yarda da juyin wainar matar mai sana’ar na-duke; kada ku yarda ku ci na-aura, don haka sai ku yi aura, uwa-uba kada a karke a gadar adon-gari, don gudun kada a shiga gararin juyin aya takanda.
Farfesa Ja-gaban zabi-sonka, ’yan koren Shugaban Gudun-loko da Jona-tanti na yunkurin janye shi zuwa gaba. Sai dai wannan tufka da warwara kulle-kullen makirci da shagabanni ke yi wa Haurobiyawa sun hadu da tasgaro, inda dimbin matasa masu fuka-fukan tashi da jinni a jika suka himmatu wajen fasa kwayaye a shafukan fuskantar bokoko da ke mashakatar lilo da tsallake-tsallake. Kai saboda tsallen badake irin na matasa har lakaba wa watan zabi-soka suna suka yi, wato ‘Farin-Bahari,” yanzu kuma sun koma Marsar Bahari. Manufar masu fafutikar burinhuriyya da kawo sauyi a rayuwar Haurobiyawa ita ce, dakile wadaka da watandar Hauro da In-gwan-gwaje-in-wala ke yi wa Gwamnatin Shugaban Gudun-loko da Jona-tantin mulki, inda Mace-da-zane ke tsakuro musu dammai daga lalitar Kamfanin Tunkuza na kasa. Ga gungun manyan kwabo irin su tsohon Kilaki da ke nuna adawa karara ga al’ummar Arewatawan Haurobiya.
’Yan makaranta in har ba ku kakaba wa kurunku tagiyar Malam Mantau ba, kun san mun sha bijiro da darussa kan wadaka da wadatantar Hauro da jiga-jigan Jam’iyya mai dan boto da sanda jirge suka shafe shekaru sili da manuniyar sama suna tsuwurwurtawa a kasar nan. Kun dai san muna da tarin samarin kusu da ‘’yan matan jaba da gafiya, wadanda suka baibaye laliutar kasar Haurobiya suna ta yin zari-ruga. Don haka har yau kasar nan ta kasa fita daga cikin duhun-dundumdurundum, shi yasa ma aka kusa sake yi mata zanen suna zuwa “Jamhuriyar Ja-ni-ina-reto.”
Haurobiyawa, wasu gungun makirai da suka hada da rasa kunya beran tanka Asarar-dan-kwabo da Kansakalin-kuku, sun bayyana karara irin mugun nufinsu na tada zaune-tsaye matukar aka daina Jona-tantin mulki da gudu a cikin loko. Sai dia cikin ikon Mai-duka masu hankali a cikin kwanyarsu, ba masu hankali a hannun taguwa ba, sun fasko cewa miyagu irin su Samun-bom-da-sauki na kokarin tsunduma kasar nan cikin yamutsin Haramta Bobo da kwambon bokoko, don haka suka tursasa Farfesa Ja-gaban zabi-sonka dole ya kara musu wa’adi, don su ci gaba da yin batanci ga shugaban Fafutikar Burin-huriyya, dan takarar jam’iyyar tsintsiya madaurinki guda, mai maganin radadi da zogin ciwon kurungu. Bututun batutuwan zuyki-ta-malle kama-kare ka hada shi da zomo na jam’iyya mai dan boto da sanda jirge, wato Fuffuken-fankan-fayau, shi aka bai wa kantiragin far-far-da-ganda, amma tuni ganda ta kama shi, sai kame-kame ya keta yi dabaranbarama.
Babban darasin d amuke son al’ummar Haurobiya su fasko shi ne, daukacin manyan kasar nan sun san cewa, Gudun-loko da Jona-tanti babu inda zai al’umma illa ga halaka, amma tunda bas u za a halaka ba, to ko oho, wai a ci gaba da gashi, suya kuwa sai ranar sallah. Kuma suna nuna adawa ga Shugaban Fafutikar Burin-huriyya ne saboda tsattsauran ra’ayinsa na hana kwashi-kwaraf da dukiyar al’umma. Saboda ganin ba za su kai ga gaci ba, sai suka bullo da cewa, mai dan boto da sanda jirge ta fi tsintsiya madaurinki guda yawan masu fuskantar alkibla, domin Usainin Babajo, ya gina dimbin majami’u, don haka kada a zabe shi, wai a zabi ubangidan Malam Namando, ashe Malam Namando bai san bihim ba.
A wajen yakin neman zabi-sonka, Malam Namando ya kasa karatun farali surar da ta zamo wjaibi ga mai ibada ya fuskanci Mahaliccinsa da ita. To, kun ga wanda duk ya ha’inci Mai-duka ai ba zai kai labari ba. Ni kuwa na tabbata Usainin Babajo yasan farillan aihini da na kifayar addininsa, don haka nike ganin ba zai ha’inci al’umma ba, ballantana Mahaliccinsa.
Inda za ku fasko cewa Malam Namando, mataimakin Shugaban Gudun-loko da Jona-tantin mulki bai san bihim ba, ai da ya tunkari Sallau-lado, tsohon Gwamnan Babbban Asusun Haurobiya wanda ya yi wa In-gwan-gwaje-in-wala tonon silili kan yadda ta bari aka salwantar da Hauro tiren-taliya kofar hanci da zagaye. Kai ko a jiharsa ta Bayan-kada yana kallo Malam Nasara el-Rusau zai rushe Man-kaza, domin shi ya hana shi katabus, har ya kare shekarun mulkinsa bai tabuka komai ba. Kuma wai ya zo yana yi wa Baharin Burin-huriyya da Usainin Banjo isgili wai kada su sake su ce za su tunkari mayakan haramta Bobo da kwambon bokoko. To ga Samun Bom da Sauki nan ya fesa zuki-ta-malle. Muna ji, muna gani, muna kuma saurare! Rana ba ta karya, si dai uwar diyya ta ji kunya,’ a cewar Malam Mai yaren Hau-hau wajen hawan sa, ba tare da sa-in-sa-ba.
Ramin zuki-ta-malle kurarre ne, kuma matukar mai kanannen na-mujiya ya jagoranci masu gani, to duka za su afka cikin rami. Haurobiyawka a nemi tsari daga mai dan boto da sanda jirge, ko roki Mai-duka yak are al’umma daga miyagun masu mulkin mulaka’u da kungurmin jahilin da bai san bihim ba. Mu yi fatan smaun makoma mai kyau a doron duniya da gobe kiyama. Wannan kuwa duk ba za ta samu ba, har sai mun tuntsurar da mai dan boto, mun dora Baharin Burin-huriyya da Usainin Babajo, lallai mu dauki nasihar Baba-ojo. Da zarar an kawar da mai dan boto, Haurobiyawa sun samuy sa’ida, to a yi ta raba goriyar marsa, don gudun kad amu yi marisa a cikin watan MArisa na shekara ta dubu karamin lauje d asili da babban lauje.