Namijin da mata suka fi so tsakanin miskili da mai surutu
Ra’ayoyin mata matasa game da maza masu miskilanci da masu surutu.
Zabin mutane ya bambanta a abubuwan da suke la’akari da su wajen zabar miji ko matar aure ko abokin zaman tare.
Wasu sun fi karkata ga dabi’a, tarbiya, kabila, yanayin kuruciya ko al’ummar da mutum ya taso da matakin karatunsa, wasu kuma hatta yananin magana, kamun kai da haba-haba da mutane ko shiru-shirunsa na da muhimmanci a wajensu saboda yau da gobe.
Aminiya ta zanta da wadansu mata ’yan bana bakwai, inda suka bayyana mata yanayin maganar irin namijin da suka fi so.
Daga cikinsu akwai wadanda suka ce in dai namiji mai shiru-shiru ne to sun hakura.
A kai kasuwa
Sun bayyana wa Aminiya cewa sun fi son namijin da kodayaushe zai fito ya bayyana ra’ayoyinsa ko abun da ke ransa.
Maryam Muhammad ta ce, “Ni dai na fi son namiji mai sakin jiki da haba-haba a soyayya, wanda zai rika fitowa ya bayyana miki abin da ke zuciyarsa.”
A ganin mata masu irin wannan ra’ayi namiji miskili na ba su haushi.
A cewarsu, yawan tattaunawa da juna da kuma mayar da hankali ga al’amuran juna yana karfafa soyayya, amma namiji miskili zai yi tsanani.
“Idan namiji ya cika shiru-shiru ba zai yi miki wasa ba, sai ka ce aikin soja. Ai tattaunawa da juna na da muhimmanci,” inji Maryam.
Ameerah Muhammad kuma ta ce, “Ba na son namiji mai yawan magana, wanda nake so shi ne mutumin da zai rika tattaunawa da ni.”
Miskilin namji ya yi
Matan da ke son miskili, sun ce sun fi son hulda da mutumin da bai cika magana ba sai dai idan yin maganar ta zama dole.
Sun bayyana mana cewa sun fi samun sakewa da namijin mai wannan dabi’a, saboda yawan magana yakan takura musu.
Faiza Muazu ta ce, “Maza masu surutu za su gunduri mace.”
Bugu da kari, “idan namiji ya cika shiga cikin al’amarin mace, wannan na matsa wa rayuwarta, wani lokaci ma har da danne mata hakki.”
Faiza ta ce, “Shiru-shiru kuma ba a kan komai yake magana ba, saboda yana ganin kin mallaki hankalinki kuma kin san abin da kike yi.
“Idan kuma akwai abin da ya kamata ya yi magana a kai, zai fito su yi magana idan ta kama,” inji ta.