Nan ba da jimawa ba za mu kama Bello Turji — Janar Musa

Bello Turji mutum ne kawai da ya sauka daga kan layi yake tunanin ya isa.

Nan ba da jimawa ba za mu kama Bello Turji — Janar Musa

Babban Hafsan Tsaron Najeriya, Janar Christopher Musa

Babban Hafsan Tsaro na Nijeriya, Janar Christopher Musa, ya sha alwashin kama ƙasurgumin dan fashin dajin nan Bello Turji nan ba da jimawa ba.

Da yake magana yayin wani taron manema labarai ranar Talata a Abuja, janar ɗin ya ce, “Saura ƙiris mu kama Turji.”

Dangane da wa’adin biyan kuɗin haraji da aka ce Turji ya bai wa mazauna yankunan Jihar Zamfara, Janar Musa ya ce sojoji na aiki da sauran hukumomin tsaro domin kare mazauna yankunan.

“Game da Turji, mutum ne kawai da ya sauka daga kan layi kuma yake tunanin ya isa, amma ina tabbatar muku za mu kamo shi kuma cikin ƙanƙanin lokaci,” in ji shi.

Shugaban sojojin ya kuma nemi mazauna yankunan da su bai wa sojoji haɗin kai.

“Kada ku taimaka musu, kada ku ba su wasu bayanai game da samamen da muke kaiwa saboda abin da yake faruwa yanzu kenan.”

Bayanai daga Jihar Zamfara na cewa yau Laraba ce ranar da Bello Turji ya bai wa al’ummar garin Moriki ta ƙaramar hukumar Shinkafi, kan su biya harajin Naira miliyan 50 ko kuma su bar garin.

To sai dai hakan na zuwa ne a yayin da Rundunar Sojin Nijeriya ta lashi takobin ganin ƙarshen taaddancinsa a wani matakin da ma’aikatar tsaron Nijeriya ta dauka na maida hankali ga jihohin Sokkwato, Kebbi da Zamfara domin kammala yakar ’yan ta’adda.