Nan ba da jimawa ba zan bayyana matsayina kan batun ficewa daga NNPP – Shekarau
Ya ce a cikin makon nan zai bayyana matsayinsa
Sanatan Kano ta Tsakiya, Malam Ibrahim Shekarau ya musanta duk wani labari da ake yadawa cewa zai fice daga Jam’iyyar NNPP zuwa Jam’iyyar PDP, inda ya ce nan gaba kadan zai bayyana matsayinsa a kan batun.
Mai magana da yawun Sanatan, Dokta Sule Ya’u Sule ne ya bayyana hakan a cikin wata takarda da ya fitar mai dauke da sa hannunsa ranar Talata.
- ’Yan bindiga sun sace Kwamishina a Nasarawa
- Yadda rusasshiyar gada tsakanin Kano da Jigawa ta zama tarkon mutuwa
Sule Ya’u Sule ya nemi al’umma su yi watsi da duk wani labari da ake yadawa game da siyasar gidan Sanata Ibrahim Shekarau.
Ya kara da cewa “A makon nan da muke ciki za mu sanar da jama’a game da halin da ake ciki saboda a wanke duk wani shakku a zukatan al’umma kan labaran da ake yadawa game da Siyasar Malam Ibrahim Shekarau.”
Da safiyar Talatar ce wata jaridar intaner ta rawaito cewa Sanatan yana niyyar ficewa daga jam’iyyar NNPP zuwa Jam’iyyar PDP sakamakon tayin da dan takarar Shugaban Kasa na jam’iyyar, Atiku Abubakar ya yi masa.
Ana zargin Atiku Abubakar ya yi wa Shekarau din tayin wasu makuden kudade don ya koma jam’iyyar ta PDP.
Malam Shekarau, wanda ke wakiltar Kano ta tsakiya a Majalisar Dattawa, ya fice daga jam’iyyar APC zuwa NNPP a hukumance a wata wasika da Shugaban majalisar, Ahmed Lawan ya karanta a zaman majalisar a ranar 29 ga watan Yunin 2022.