Nan ba da jimawa za a ƙara kuɗin kiran waya da data — Gwamnati

Ministan ya tabbatar da cewa za a yi ƙarin kuɗin amma ba kamar yadda kamfanonin sadarwar suka nema ba.

Nan ba da jimawa za a ƙara kuɗin kiran waya da data — Gwamnati

Gwamnatin Tarayya ta tabbatar cewa za a ƙara kuɗin kiran waya da data, amma ba da kashi 100 kamar yadda kamfanonin sadarwa suka nema ba.

Ministan Sadarwa da Tattalin Arziƙi, Dokta Bosun Tijani ne, ya bayyana hakan bayan wata tattaunawa da kamfanonin sadarwa a Abuja.

Ya ce ana ci gaba da tattaunawa, kuma Hukumar Sadarwa ta Najeriya (NCC) za ta sanar da sabon tsarin kuɗin nan ba da jimawa ba.

“Mun fahimci buƙatar ƙarin kuɗin, amma ba za a ƙara zuwa kashi 100 ba.

“Burinmu shi ne kare masu amfani da sadarwa tare da tabbatar da cewa kamfanoni suna ci gaba da zuba jari a wannan fanni,” in ji Tijani.

Shugaban NCC na Ƙasa, Dokta Aminu Maida, ya jaddada cewa sabon tsarin zai mayar da hankali kan ɗorewar harkar sadarwa.

Ya ƙara da cewa NCC tana aiki don sauƙaƙa tsarin farashi tare da magance ƙorafe-ƙorafen masu amfani da sadarwa.

Kamfanonin sadarwa, ciki har da Airtel, sun bayyana cewa hauhawar farashi ne ya sa ake neman ƙarin kuɗi.

Sun kuma tabbatar wa masu kwastommi cewar za su ci gaba da samun ingantaccen sabis duk da ƙalubalen da ake fuskanta.