Nan da karshen wata zan kafa sabuwar Majalisar Zartarwa – Ajimobi
Gwamnan Jihar Oyo Cif Abiola Ajimobi ya bayar da tabbacin nada sabuwar Majalisar Zartarwar Jihar nan da karshen watan da muke ciki, inda ya ce ya rusa majalisar a watan jiya ne domin samar da wata kafar ci gaba ga jihar. Gwamnan wanda ya fadi haka ga ’yan jarida a gidan gwamnati bayan saukowa daga […]

Gwamnan Jihar Oyo Cif Abiola Ajimobi ya bayar da tabbacin nada sabuwar Majalisar Zartarwar Jihar nan da karshen watan da muke ciki, inda ya ce ya rusa majalisar a watan jiya ne domin samar da wata kafar ci gaba ga jihar.
Gwamnan wanda ya fadi haka ga ’yan jarida a gidan gwamnati bayan saukowa daga Idin Babbar Sallar a Ibadan a ranar Talata ya ce yanzu haka ana tattaunawa a kan wannan batu a tsakanin shugabannin jam’iyya domin shirya sabuwar majalisar.
Gwamna Ajimobi ya yi bayanin cewa, an rusa tsohuwar majalisar mai kunshe da kwamishinoni da manyan masu ba shi shawara ne domin kyautata ayyuka da samar da gurbi ga wasu ’ya’yan jam’iyya da za su ba da tasu gudunmawar ga ci gaban jihar. Ya ce, ya riga ya sanar da shugabannin jam’iyya da su aika masa da sunayen mutanen da suke bukata a nada bisa mukaman.
Dangane da batun kin cika alkawari da wasu ’yan siyasa da masu rike da mukamai suke yi wa jama’a, sai ya ce, “Ya kamata irin wadannan ’yan siyasa da masu rike da mukamai su rika cika alkawarin da suka yi ga jama’arsu domin nauyi ne a kansu da Allah zai tambaye su a gobe kiyama.”
Sai ya ce, “Mu dai sai godiya ga Allah domin dukkan alkawarin da na yi ga jama’ar Jihar Oyo, ga su muna cikawa. Ga irin ayyukanmu nan a bayyane mun kammala wasu muna ci gaba da gina wasu muhimman ayyuka domin cika alkawarin da muka yi a baya. Dole ne mu cusa tsoron Allah a zukatanmu wajen yin jagorancin jama’a da gaskiya da adalci.”
Tun da farko Gwamna Ajimobi da tawagarsa sun fara yada zango ane gidan Sarkin Musulmin kasar Yarbawa Alhaji Abdul-Azeez Arisekola Alao da ke Unguwar Ikolaba, Ibadan domin kai masa gaisuwar ban girma tare da taya shi murnar Babbar Sallar bana.
Babban limamin Ibadan, Sheikh Suara Haruna ne ya jagoranci dubban Musulmi maza da mata lokacin sallar mai raka’a biyu a filin Idi na Agodi a Ibadan.