Nan da mako daya mazauna Ibadan za su samu ruwan famfo bayan shekara biyu babu

Shekara biyu da ruwan famfo ya yi layar zana a birnin Ibadan da kewaye saboda aikin tonon ramuka da aka binne tsofaffin bututun ruwa da suka shafe fiye da shekara 40, yanzu al’ummar birnin Ibadan, sun samu tabbacin samun ruwan famfo nan da mako daya.Janar Manajan Hukumar Ruwa ta Jihar Oyo, Mista Gabriel Oluseji Oguntola […]

Nan da mako daya mazauna Ibadan za su samu ruwan famfo bayan shekara biyu babu

Shekara biyu da ruwan famfo ya yi layar zana a birnin Ibadan da kewaye saboda aikin tonon ramuka da aka binne tsofaffin bututun ruwa da suka shafe fiye da shekara 40, yanzu al’ummar birnin Ibadan, sun samu tabbacin samun ruwan famfo nan da mako daya.
Janar Manajan Hukumar Ruwa ta Jihar Oyo, Mista Gabriel Oluseji Oguntola ne ya bayar da tabbacin, inda ya ce, “Al’ummar birni Ibadan za su yi mamaki a karshen wannan wata domin za su wayi gari da ruwan famfo a cikin gidajensu bayan shafe shekara biyu rabonsu da ganin haka.”
Mista Oguntola, wanda yake fadin haka ga ’yan jarida a ranar Talatar da ta gabata, lokacin da ya jagoranci tawagar injiniyoyi domin duba ayyukan da hukumar ta gudanar a Unguwar Mokola, Ibadan, ya ce, “Gwamna Abiola Ajimobi wanda ya amince da fara aiki tun lokacin da ya hau karagar mulki, yana sane da muhimmancin ruwa ga al’umma musamman irin wannan birni mafi girma a Nahiyar Afirka, kuma a dalilin haka ne ya tashi tsaye wajen mayar da hankali ga aikin da zai samar da tsabtataccen ruwa ga al’ummar jihar baki daya. Aikin samar da ruwan da za a fara rarrabawa ga jama’a a karshen watan da muke ciki zai shafi dukkan garuruwan Jihar Oyo ne.”
Janar Manajan, ya ce “Yanzu haka an yi nisa da ayyukan tono tsofaffin bututun ruwa domin maye gurbinsu da manyan sababbin bututu na zamani a unguwannin Basorun da Ikolaba da Bodija da Agbowo da Orogun bayan wanda ake kan yi a kusa da gadar sama ta Mokola, duk a birnin na Ibadan.”  Ya jinjina wa Gwamna Ajimobi wanda ya amince da kashe miliyoyin Naira domin gudanar da aikin. Ya ce wannan gwamnati ita ce ta farko da ta fara gudanar da irin wannan muhimmin aiki da zai taimaka wajen samar da wadataccen ruwan sha ga miliyoyin mazauna Ibadan da jihar baki daya.