Nan da shekarar 2030 za a daina asarar rayuka sanadiyyar haɗurra a titi — FRSC

Muna fatan nan da shekarar 2030, ko an yi hatsarin mota, ba za a samu asarar rai ba.

Nan da shekarar 2030 za a daina asarar rayuka sanadiyyar haɗurra a titi — FRSC

Hukumar Kiyaye Haɗɗura ta Ƙasa (FRSC) ta bayyana fatanta na cewa nan da shekarar 2030 za a daina a samu mace-mace ba sakamakon hatsari a titunan Nijeriya.

Shugaban hukumar Kiyaye, Shehu Mohammed ne ya bayyana hakan a garin Makurdi a lokacin da yake gabatar da jawabi a matsayin babban baƙo a taron masu ruwa da tsaki mai taken: “Haɗin gwiwar masu ruwa da tsaki: Mahimmancin Kare Rayukan Al’umma.”

Mohammed, wanda ya samu wakilcin mataimakinsa, Yusuf Haruna, ya jaddada cewa mutane ke haddasa kashi 90 cikin 100 na haɗɗuran hanyoyin, sauran kashi 10 kuma ana alaƙanta su da matsalar na’ura ko wasu kurakurai.

Ya bayyana gudun wuce gona da iri a matsayin kan gaba wajen haddasa haɗurra masu muni.

Ya ce, “Muna fatan nan da shekarar 2030, ko an samu  hatsarin mota, ba za a samu mace-mace ba.

“Za mu ci gaba da wayar da kan jama’a cewa gudun wuce gona da iri yana haddasa mutuwa.

“Duk hatsarin da ya faru da a ke iya haddasa mutuwa, gudun wuce gona da iri ne sanadi.

“Idam direba na tafiya kilomita 20 zuwa 50 a cikin sa’a guda, ko da ya buge wani abu, zai iya lalata fitilar birki ne kawai, amma da wuya fasinjojin su samu rauni.

Amurka za ta dawo wa Najeriya N80bn da ta ƙwato daga Diezani

Yadda gwamnati ta yi sulhu da ’yan bindigar Kaduna

‘Da kuɗin yankan farce na je Hajji’

Zambar Intanet: EFCC ta kama ’yan China 4 da wasu 101 a Abuja