‘Nan da shekaru 2 za a nemi likitoci a rasa a Nijeriya’
Muna ganin yadda a shekarun bayan nan ake fifita lauyoyi da har aka yi musu ƙarin albashi da kusan fiye da kashi 300.
Shugabannin Asibitocin Koyarwa da Cibiyoyin Lafiya na Tarayya sun bayyana damuwa kan barazanar ƙarewar ma’aikatan lafiya a ƙasar saboda ƙarancin albashi.
Mahukuntan sun bayyana damuwar ce a yayin da ma’aikatan lafiya musamman likitoci ke tururuwar ƙaura zuwa ƙetare domin neman mafita mafi inganci.
- An tsinci gawar magidanci a rijiya a Kano
- ’Yan fashi sun hallaka mutum 7 a harin Kasuwar Ngalda da ke Yobe
Sun bayyana wannan koke a yayin da suke kare kasafin kuɗin shekarar 2025 da aka ware cibiyoyin lafiyar a gaban Kwamitin Majalisar Wakilai kan Harkokin Cibiyoyin Lafiya.
Sun ƙara da cewa duk da kuɗaɗen da gwamnatin tarayya ke zubawa a fannin gine-gine da kayan aiki na lafiya, likitoci na guduwa, wanda hakan yana shafar cibiyoyin.
Da yake jawabi, Babban Darektan Asibitin Koyarwa na Jami’ar Legas (LUTH), Farfesa Wasiu Adeyamo, ya ce la’akari da yadda ma’aikatan lafiyar ke ƙaura zuwa ƙetare, nan shekara ɗaya ko biyu asibitoci za su zama kufai.
Martanin Ƙungiyar Ma’aikatan Lafiya
Da yake nasa jawabin kan lamarin, Dokta Emeka Ayogu wanda shi ne shugaba Ƙungiyar Ma’aikatan Lafiya, ya tabbatar da matsalar da shugabannin cibiyoyin lafiyar suka zayyana.
Ya bayyana cewa Nijeriya ta rasa likitoci da dama waɗanda suka yi ƙaura zuwa wasu ƙasashe da suka fi samun ingancin walwala da jin daɗin aiki.
Ya bayyana cewa ƙaruwar adadin likitoci da ma’aikatan lafiya da ke ƙaura zuwa ƙetare na da nasaba ne da ƙarancin albashi, matsin tattalin arziki da kuma rashin ingancin kayan da kuma wuraren aiki a ƙasar.
Ya ce “albashin da ake biyan ma’aikatan lafiya a ƙasar ba zai wadatar da su ba.
“Kuma ko a shekarun bayan nan mun ga yadda ake fifita lauyoyi da a kwanan nan an yi musu ƙarin albashi da kusan fiye da kashi 300.”