Nan gaba duk wanda ba shi da ilimin kwamfuta kamar bai yi karatu ba ne – Gidado
Is’haka Gidado na daya daga cikin matasan da Allah Ya ba baiwa kan ilimin kwamfuta da sanin yadda ake sarrafa yanar gizo, har ma ya bude makarantar koyar da ilimin kwamfuta a garin Jalingo Jihar Taraba. A hirarsu da wakilinmu ya bayyana yadda ya fara koyon ilmin kwamfuta kamar haka: Daga Magaji Isah, JalingoAminiya: Mene […]
Is’haka Gidado na daya daga cikin matasan da Allah Ya ba baiwa kan ilimin kwamfuta da sanin yadda ake sarrafa yanar gizo, har ma ya bude makarantar koyar da ilimin kwamfuta a garin Jalingo Jihar Taraba. A hirarsu da wakilinmu ya bayyana yadda ya fara koyon ilmin kwamfuta kamar haka:
Daga Magaji Isah, Jalingo
Aminiya: Mene ne takaitaccen tarihinka?
Is’haka Gidado: An haife ni a garin Jalingo a 1989 a garin na fara firamare a 1995, a Firamaren Muhammadu Nya da ke nan Jalingo. A shekarar 2001 bayan na kammala firamare sai na shiga Sakandaren Magami a nan Jalingo. Na kammala a shekara 2007, daga nan na wuce zuwa Kwalejin Ilimi (COE) ta Jalingo a shekarar 2008. Amma ina shekara ta biyu a kwalejin sai na bar ta a shekara ta 2011. A shekarar 2012 na samu shiga Jami’ar Jihar Taraba, a halin yanzu ina shekara ta uku a jami’ar inda nake karanta ilimin tattalin arziki (Economics).
Aminiya: A ina ne ka koyi ilimin kwamfuta kuma me ya ba ka sha’awa?
Is’haka Gidado: A shekarar 2005 lokacin da nake aji hudu a sakandare tunanin koyon ilimin kwamfuta ya zo mini. Sai na samu daya daga cikin yayyena mai suna Abdulmudallabi na ce masa ina son ya hada ni da wanda ya san harkar kwamfuta ya koya mini domin ina sha’awar ilimin kwamfuta ina son in koya.
An dan dauki lokaci kafin shi ya hada ni da wanda zai koya mini ilimin kwamfuta. Sai shi Yayan nawa ya dauke ni ya kai ni wurin wanda yake son ya hada ni da shi.Mutumin da ya hada ni da shi ana kiransa Yaya Lele, shi ne mutum na farko da ya fara koya min ilimin kwamfuta a Jalingo.Na kasance a karkashin Yaya Lele ina koyon ilimin kwamfuta har na tsawon wata takwas. Na koyi abubuwa da dama kuma masu muhimmaci dangane da ilimin kwamfuta da suka hada da yadda ake sarrafa ta sai kuma gyare-gyare kan matsalolin manhajar kwamfuta da kuma abubawan da suke da alaka da wutar da ke tafiyar da ita wato Computer electronics.
Zamana a wannan shago na koyon ilimin kwamfuta, na yi karatu sosai kan yadda ita kwamfuta take da kuma zamantakewa da mutane. Amma daga bisani na bar koyon ilimin kwamfuta don in fuskanci jarrabawa na kammala makarantar sakandare. Bayan na kammala a shekarar 2007 sai na ga ya kamata in sake ci gaba da koyon kwamfuta.Har wa yau kuma sai na sake tuntubar Yayana cewa ina bukatar sake ci gaba da koyon ilimin kwamfuta. A wannan karon sai ya shawarce ni in sayi takardar neman shiga wata makarantar koyar da ilimin kwamfuta wadda fitacciya ce a nan Jalingo, wato makarantar Taraba Online, sai na bi shawararsa na fara karatun satifiket a mataki na farko a makarantar daga watan Yuli zuwa Nuwamban shekarar 2007. A makarantar na koyi abubuwa da dama da suka hada da ayyuka da manhajojin ofis wato Microsoft Office kamar su Word edcel da PowerPoint da yadda za a yi amfani da yanar gizo. Bayan kammala karatu a Taraba Online a Nuwamban shekarar 2007 sai na ci gaba da zuwa makarantar saboda kasancewarta kusa da gidanmu kuma ga shi na kammala sakandare ba wani abu da nake yi.
Sai mai makarantar ya amince cewa in rika taimaka wa sababbin dalibai sakamakon fahimtar da ya yi cewa ina da matukar sha’awar koyon aikin kwamfuta. Sai na dauki aikin taimaka wa sababbin dalibai yadda za su gudanar da wasu abubuwa a duk lokacin da ya kasance ba malami a cikin aji. Na ci gaba da yin haka har zuwa watan Disamban shekarar ana cikin haka, sai Daraktan Makarantar Malam Yakubu Adamu ya kira ni ya tambaye ni cewa ko akwai wani aikin da nake yi bayan zuwa makarantarsa? Na ce ba ni da wani aiki, shi ya sa ma na nake zuwa ina taimaka wa sababbin dalibai. Sai ya nemi in rika zuwa ina taimaka masa da wasu ’yan aikace-aikace a makarantar na amince ba tare da bata lokaci ba.
Aminiya: Me ya sa ka yarda da bukatar duk da cewa ba daukarka aiki ya yi da za a rika biyanka albashi ba?
Is’haka Gidado: Haka ne bai ce zai rika biya na albashi ba, amma saboda sha’awar da nake da ita kan kwamfuta, shi ya sa na amince kuma na nuna jin dadin haka domin a fahimtata wannan zai ba ni damar koyon sababbin hikimomi na gyare-gyare da kuma tunawa da abubuwan da na koya amma na jima ban yi su ba.
Tun daga wannan lokaci na fara ayyukan gyare-gyaren kwamfuta kuma daga baya na shiga ayyukan hada yanar gizo daga wannan kwamfuta zuwa wancen wato Networking.
A watar Satumban shekarar 2008 wannan makaranta ta Taraba Online ta tura ni Legas don in koyi ayyukan hada na’urar internet. Bayan haka makarantar ta sake tura ni Legas a watan Nuwamban 2008 din domin koyo hikimomi kan na’urorin wireless wato wayar tafi-da-gidanka sunan wannan kwas shi ne ilimin kimiyyar wayar tafi-da-gidanka, wireless technology.
Daga bisani an sake tura ni Legas don koyon fasahar wayar tafi-da-gidanka a zangon karatu na biyu. Sai kuma a farkon shekarar 2009 na sake tafiya Legas don koyon ayyukan kyamarar leken asiri, wato CCTb da kuma IP Surbeillance.
To bayan na fahimci yanzu hannuna ya nuna kan lamarin aiki da kwamfuta tare da gyaranta sai ni da wani abokina da muke tare a Taraba Online a karkashin uban gidanmu Malam Yakubu Adamu muka fara tunanin mu bude wurin harkokin ayyukan kwamfuta wato Business Centre. Saboda ganin yadda mai gidanmu ya taimaka mana wajen koya mana sana’a, ni da wannan abokina mai suna Ahmed Baba muka ga ya kamata mu shaida wa mai gidanmu wannan buri namu. A shekarar 2010 ne wannan tunani ya zo mana sai muka fada wa mai gidanmu cewa muna son mu bude namu shagon harkokin kwamfuta.Mai gidanmu ya nuna matukan farin cikin wannan tunani namu.
Aminiya: Wane suna kuka sa wa kamfanin naku kuma yaya maganar kudi kun nemi bashi a banki ne ko wani ya ba ku bashin kudi kuka fara?
Is’haka Gidado: A’a mun yi amfani da dan abin da muke da shi, daga nan sai muka fara kokarin yadda za mu yi wa kamfanin rajista muka nemi shawara ta yadda za a yi mana rijista cikin ikon Allah ba mu samu wata matsala ba wajen samun rijistar.
Mun yi rijistar sabon kamfaninmu a watan Satumban 2010 da sunan WEB-TECH COMPUTER TRAINING AND CYBERCAFE mun kuma nuna wa maigidanmu wannan satifiket. Duk da haka na ci gaba da aiki a karkashin mai gidanmu domin ba mu gama hada jarin sayen kayan aiki ba, sai a watan Fabrairun shekarar 2012 na bar aiki da maigidana.
Aminiya: Ga shi kun bude makarantar koyar da kwamfuta yaya ka fara kuma dalibai nawa kake tare da su?
Ishak Gidado: Bayan mun samu rijistar a Satumban shekara 2010, daya daga cikin abubuwan da muke so mu yi sun hada da koyar da kwamfuta ga matasa da samar da internet ga ma’aikatun gwamnati da na ’yan kasuwa. Cikin ikon Allah mun fara samun kwangila a Jalingo a shekarar 2012 kuma mun kara samun wasu a shekarar 2013. Saboda irin kyakyawan horo da muka samu kan kwamfuta a wurare daban-daban musamman a Taraba Online ya ba mu damar fahimtar kwamfuta da iya gyaranta.
Koda yake na halraci karatun aikin kwamfuta da gyaransu a lokuta daban-daban a Legas suma wurare ne masu zaman kansu.Wannan ya sa duk inda muka yi gyaran kwamfuta ko yanar gizo muna samun sa’a inda ma’aikatun gwamnati da na ’yan kasuwa suke nemanmu don yin musu gyara in sun samu matsala da na’urorinsu. Duk ribar da muka samu daga wadannan kwangiloli mun yi amfani da su ne wurin sayen kwamfitoci da kujeru da tebura da kayayyakin yanar gizo da sauransu. To da muka ga mun hada kayan aiki tare da ’yan kudin soma aiki sai muka kama hayar ofis muka fara aiki a watan Yulin 2013.
Aminiya: Yanzu kuna da dalibai nawa kuma wadanne fannoni kuke koya wa dalibanku?
Is’haka Gidado: Mun fara koyarwa ta wurin da jama’a ke yin amfani da yanar gizo da sauran ayyukan kwamfuta da dalibai kadan. Amma a yanzu ba ma rasa dalibai 50 ko fi a kowane lokaci wadanda suke daukar darussa ka ilimi da fasahar kwamfuta a makarantar. Tun fara gudanar da makarantar mun koyar da dalibai kimanin 200. Kuma bayan cibiyar wannan makaranta da ke kusa da Babbar Kotun Jihar Taraba a titin Sabon Gari, mun kuma bude reshe a dab da kofar shiga jam’ar Jihar Taraba .A sabuwar reshen ma muna sa ran za mu fara koyar da ilimin kwamfuta saboda bukatar da dalibai ke da ita ta koyon kwamfuta.
Aminiya: Wane amfani matasa za su samu dangane da koyon ilimin kwamfuta da yanar gizo?
Is’haka Gidado: Ganin cewa kwamfuta na’ura ce da ake amfani da ita a wuraren daban-daban kamar mai’aikatu da bankuna da makarantu da asibitoci da sauransu, ya zama wajibi a wurin duk wani matashi da ke da niyyar shiga makaranta ko yin aiki da wuraren ya samu ilimin amfani da kwamfuta. Bayan haka akwai matasa da dama da muke koya wa sana’a da kwamfutar wanda hakan zai taimaka musu su dogara da kansu kamar yadda nake yi a yanzu.
Aminiya: Yaya kake ganin matasa da iyayensu wajen rungumar koyon kwamfuta a nan Jalingo?
Is’haka Gidado: Matasa da iyaye sun fahimci amfanin kwamfuta domin muna samun iyaye da yawa suna kawo ’ya’yansu nan makaratar don su koyi ilimin kwamfuta. Kuma akwai mutane masu yawa wasu ma’akata da sukan zo su yi rijista a nan makarantar don koyon kwamfuta. Dole mu gode wa maigidanmu domin a dalilinsa matasa masu yawan gaske sun koyi aiki da gyaran kwamfuta inda a yanzu ta wannan hanya ce suke ci su sha har ma su biya kudin makaranta. Ni kaina a yanzu dalibi ne a Jami’ar Jihar Taraba ina shekarar karatu ta uku, duk ta wannan hanya nake samun kudin makaranta da sauran bukatuna, na yau da kullum.