Nan gaba kadan za a gurfanar da Aliyu Madaki a kotu

Rundunar ’Yan Sandan Jihar Kano ta bayyana cewa cikin kankanin lokaci za ta gurfanar da zababben Dan Majalisar Tarayyar a gaban kotu

Nan gaba kadan za a gurfanar da Aliyu Madaki a kotu

Rundunar ’Yan Sandan Jihar Kano ta bayyana cewa cikin kankanin lokaci za ta gurfanar da zababben Dan Majalisar Tarayya mai wakiltar Karamar Hukumar Dala a karkarshin tutar Jam’iyar NNPP, Honorabil Aliyu Madaki.

Dan Majalisar dai ya shafe kawamaki biyu a hannun ’yan sanda kamar yadda kakakin rundunar ’yan sandan, SP Abdullahi Haruna Kiyawa, ya tabbatarwa Aminiya.

Ana dai zargin Honorabul Aliyu Madaki da laifin fito da makami a fili wanda zai iya zama barazanar ga zaman lafiyar al’ummar  jihar.

An tsare Aliyu Madaki ne washegarin da rundunar ta cafke Shugaban Masu Rinjaye na Majaslisar Tarayya, Honorabul Alhassan Ado Doguwa.

’Yan sanda sun cafek Doguwa ne kan zargin tayar da zaune tsaye da kuma harin da aka kai Ofishin Hukumar Zabe ta Kasa (INEC) a Karamar Hukumar Tudunwada ta Jihar Kano a lokacin da ake tattara sakamakon zaben shugaban kasa da na Majalisar Tarayya.

Ana kuma alakanta Doguwa da harin da aka kai ofishin yakin neman zaben jam’iyyar adawa ta NNPP da ke Tudun Wada, inda aka kona wasu mutum biyu da ransu.

Dan majalisar dai ya karyata zargin.

A ranar Laraba da yamma ne dai ’yan sanda suka tsare Doguwa a filin jirgin sama na Malam Aminu Kano da ke Kano, a hanyarsa ta zuwa kasar Saudiyya domin yin Umarah.

A wata 19 Tinubu ya ciyo bashin tiriliyan 50

Jami’an Sibil Difens sun kashe mayaƙan Boko Haram 50

Sojoji sun kashe ’yan Boko Haram 30 a Borno

DAGA LARABA: Hanyoyin Dawo Da Martabar Karatun Tsangaya