Nan gaba zan fasa kwai kan mutuwar Abacha – Al-mustapha
Dogarin tsohon Shugaban kasa Janar Sani Abacha, Hamza Al-musatapha ya shaida wa manema labarai a Legas cewa shugaban bai saci kuɗin kasar nan ba, hasali ma kuɗaɗen da ake iƙirarin karɓowa daga ƙasashen Turai Abacha bai kai ajiyarsu da sunansa ba. “Sai da Gwamnatin Abacha ta kira taron muƙarrabanta da sarakunan gargajiya ta sanar da su […]
Dogarin tsohon Shugaban kasa Janar Sani Abacha, Hamza Al-musatapha ya shaida wa manema labarai a Legas cewa shugaban bai saci kuɗin kasar nan ba, hasali ma kuɗaɗen da ake iƙirarin karɓowa daga ƙasashen Turai Abacha bai kai ajiyarsu da sunansa ba.
“Sai da Gwamnatin Abacha ta kira taron muƙarrabanta da sarakunan gargajiya ta sanar da su cewa za ta kai ajiyar kuɗaɗen kasar nan ƙasar Turai, domin shirin ko-ta-kwana, ganin irin takunkumin da ƙasashen yamman ke ƙoƙarin sanya wa kasar a wanccan lokacin. An yi shirin fitar da kuɗaɗen ne domin ko bayan an sanya wa ƙasar takunkumi ta samu zama da ƙafafunta kuma kudaɗen ba a ba da ajiyarsu da sunan Shugaba Abacha ba.” Inji shi.
Al-mustapha ya yaba da ƙoƙarin marigayi Janar Sani Abacha na ciyar da tattalin arzikin ƙasar nan gaba, ba tare da karbo bashi daga ƙasashen waje ba. Ya ce kadan daga ayyukan da ya yi shi ne kafa shirin PTF, wanda ya yi rawar gani a duk faɗin ƙasar nan. Kana ya yaba da dattako da riƙon amana na Shugaba Muhammadu Buhari. Ya ce kodayake a yanzu ba ya rike da katin wata jam’iyyar siyasa amma dole ne ya yaba da gaskiya da riƙon amanar Shugaba Buhari.
Dogarin na marigayi Abacha ya shaida cewa abin da ya kashe maigidansa shi ne ya kashe Cif MKO Abiola kuma da sannu zai fasa ƙwai a nan gaba.
A kwanaki ne iyalai da masoya Cif MKO Abiola suka shirya gangamin tunawa da zaben da ya lashe na 12 ga Yuni, wanda gwamnatin sojin wancan lokacin ta soke. Mataimakiyar Gwaman Jihar Ogun, Misis Yetunde Onanuga wacce ta wakilci gwamnan jihar a taron, ta bayyana marigayi Cif MKO Abiola a matsayin mutum mai dattako da son bauta wa jama’a, kana ɗan kishin ƙasa mai son ci gabanta. Ta jagoranci yi masa addu’a da fatan nema masa gafarar Ubangiji.