Nana: Dattijo mai ’ya’ya 200 da mata mata 43
Ba a kirga yawancin ’ya’yansa ba mata saboda galibi suna gidan aure.
An gano wani mutum mai ’ya’ya sama da 200 da matan aure 43 a garin Tenzuku da ke Gabashin kasar Ghana.
Ma’aikatan sashin shirin Morning Show na gidan talabijin din Angel TB, ne suka yi tattaki zuwa kauyen Tenzuku inda suka gano dattijon mai suna Nana.
Sun kai ziyara garin mai nisan tafiyar awa 13 daga Accra, babban birnin kasar Ghana domin tattaunawa da wadansu daga cikin ’ya’yan Nana.
Duk da ba a samu ganin mutumin ba, mai magana da yawunsa ya ce, kawai an kiyasta yawan matan Nana da ’ya’yansa ne, amma sun wuce adadin da ake tsammani.
A cewarsa, ba a kirga yawancin ’ya’ya mata ba na Nana, saboda da zarar sun yi aure sai su koma gidajen mazansu.
Ya kuma ya yi ikirarin cewa da wuya a rasa dan asalin garin Tenzuku a kowane lungu da sako na kasar Ghana, saboda yawancinsu suna yin tafiye-tafiye zuwa sassa daban-daban na kasar.
Hakazalika, mutumin ya tabbatar da cewa, dukkan zuriyar Nana suna zaune lafiya, tare da matansu da ’ya’yansu, duk da yawansu da kuma yadda suke zaune a wuri guda.