Nannaga giyar gida: dan Birtaniya zai fuskanci hukuncin bulala 360

Wani dddan kasar Birtaniya mai aiki a kasar Saudiyya an kama shi da giyar da aka nannaga a gida, saboda haka aka yanke masa hukuncin bulala 360. Mutumin mai suna Karl Andree,  dan shekara 74, an daure shi har tsawon shekara guda, bayan da ya saba wa dokar Saudiyya da ta haramta nannaga giya da […]

Nannaga giyar gida: dan Birtaniya zai fuskanci hukuncin bulala 360
Nannaga giyar gida: dan Birtaniya zai fuskanci hukuncin bulala 360

Wani dddan kasar Birtaniya mai aiki a kasar Saudiyya an kama shi da giyar da aka nannaga a gida, saboda haka aka yanke masa hukuncin bulala 360. Mutumin mai suna Karl Andree,  dan shekara 74, an daure shi har tsawon shekara guda, bayan da ya saba wa dokar Saudiyya da ta haramta nannaga giya da shanta, kuma jami’an ’yan sanda sun kama shi da giyar dumu-dumu.
Iyalan mai laifin sun koka, musamman sanin cewa ya yi fama da cutar daji, don haka suke ganin ba zai iya daukar wannan hukuncin ma in an yi la’akari da nisan shekarunsa. Firayiministan Birtaniya zai kai wa wannan tsoho dauki, tunda iyalansa sun ce hukuncin na iya halaka shi.
“Wannan hukunci ne mai tsananin damuwa,” a cewar matar da ke Magana da yawun Firayiminisat, a lokacin da ta gana da manema labarai. Domin a cewarta, “Firayiminista zai rubuta wa mahukuntan Saudiyya akan wannan matsalar,” injita. A cewartta Saudiyya kasa ce da ke kawancen kut da kut da kasar Birtaniya, inda suke da hadin gwiwar harkokin soja a yankin Gabbas ta Tsakiya.
“Tsoho ne, kuma ina jin tsoron kada hukuncin bulala ya halaka shi,” a cewar Simon Andree, kamar yadda ya bayyana wa gidan rediyon BBC. “Ofishin jakadancin Birtaniya, wand aya baza gargadi a shafin sadarwarsa kan matsanancin hukuncin da ke tattare da mallakar giya a kasar Saudiyya, ya bayyana cewa jami’ansa da ke Riyadh na kula da lafiyar Andree akai, akai.
Wannan takamma tsakanin kasashen biyu, ta haifar da matsala tsakanin hukumar shari’ar kasar Birtaniya da Saudiyya, inda aka yi watsi da kwangilar bayar da horo ga jami’an gidan kaso, da aka kiyasta kudoin aikin akan Fam miliyan biyar da dubu 900. Sai dai mai Magana da yawun Firamyinistan ta ce yin watsi da kwantiragin bayar d ahoron da kasarta ta yi ba shi da nasaba da wannan hukunci da aka yanke wa Andree.