NAPTIP ta ceto mutum 285, ta kama masu safarar mutane 22 a 2024 a Kano

Hukumar ta ce ta gurfanar da mutum 15, waɗanda aka yanke wa hukunci bayan samun su da laifi.

NAPTIP ta ceto mutum 285, ta kama masu safarar mutane 22 a 2024 a Kano

Ofishin Hukumar NAPTIP mai yaki da safarar mutane a Najeriya

Hukumar Hana Safarar Mutane ta Ƙasa (NAPTIP), Shiyyar Kano, ta bayyana cewa ta ceto mutum 285 tare da kama masu safarar mutane 22 a shekarar 2024.

Kwamandan shiyyar, Abdullahi Babale ne, ya sanar da hakan a wata hira da ya yi da Kamfanin Dillancin Labaran Najeriya (NAN) a Kano, a ranar Alhamis.

Ya ce mutanen da aka ceto sun haɗa da maza 78, mata 97, da yara 110, masu shekaru daga bakwai zuwa 42.

Daga cikinsu, 53 na cikin hatsarin safarar mutane, yayin da 232 suka tsira daga cin zarafi daban-daban.

Babale ya ce: “Mun yi wa waɗanda abin ya shafa nasiha da shawarwari kafin haɗa su da iyalansu, kuma mun koyar da mutum 52 sana’o’i domin dogaro da kai.”

Ya ƙara da cewa, mutane 22 da aka kama sun haɗa da maza takwas da mata 14, kuma hukumar ta samu ƙararraki 211 da suka shafi fataucin mutane a cikin gida da waje.

Kwamandan ya kuma bayyana cewa an samu wasu ƙarar laifuka 15, ciki har da ɗan ƙasar waje guda ɗaya.

Waɗanda aka yanke wa hukunci sun haɗa da maza 13 da mata biyu, bisa laifukan cin zarafi da safarar mutane.