Nas ta kashe majinyata 6 don ta rage wa kanta aiki

’Yan sanda a kasar Jamhuriyar Czech sun bayyana tsare wata ma’aikaciyar asibiti bisa zargin kashe wasu majinyata shida domin ta rage wa kanta aikin kulawa da su. Wadda ake tuhumar mai suna, bera Maresoba mai shekara 50, kuma ta kwashe shekara hudu tana aiki ne a wani asibiti a garin Rumburk na kasar Jamhuriyar Czech […]

Nas ta kashe majinyata 6 don ta rage wa kanta aiki
Nas ta kashe majinyata 6 don ta rage wa kanta aiki

’Yan sanda a kasar Jamhuriyar Czech sun bayyana tsare wata ma’aikaciyar asibiti bisa zargin kashe wasu majinyata shida domin ta rage wa kanta aikin kulawa da su.

Wadda ake tuhumar mai suna, bera Maresoba mai shekara 50, kuma ta kwashe shekara hudu tana aiki ne a wani asibiti a garin Rumburk na kasar Jamhuriyar Czech da ke nahiyar Turai. Ana zargin ta ne da bai wa majiyata mata biyar da wani namiji guda gubar sinadarin Potassium, kamar yadda kafar yada labarai ta Odd News Blog ya bayyana.
Da farko an fara tsare Nas din ce bayan mutuwar wata mata mai shekara 70, wadda bincike ya tabbatar da cewa gubar sinadarin Potassium ne ya yi ajalinta. Har ila yau, wadda ake tuhumar ta amsa laifin kisan mutane shidan a cikin shekara hudu. Kuma duka wadanda ta kashe tsofaffi ne wadanda suke bukatar kulawa sosai. bera ta kashe su ne ta hanyar ba su allurar guba saboda ta rage wa kanta aikin kulawa da su. Har ila yau, ma’aikaciyar jinyar za ta fuskanci hukuncin daurin rai-da-rai ne, idan kotu ta tabbatar da zargin.

Fintiri ya ƙirƙiro sabbin masarautu 7 a Adamawa

Arewacin Najeriya bai dogaro da wani yanki ba – Ndume

Jagoran Syria ya sha alwashin kwance ɗamarar ƙungiyoyin da ke rike da makamai

Sojojin ruwa sun gina wa al’ummar Zariya asibiti kyauta