Nas ta kashe mijinta don ta auri fursuna

Ana tuhumar wata Nas mai suna Amy Murray da ke aiki a gidan yarin Missouri a kasar Amurka da yunkurin auren wani fursuna da aka yanke wa hukunci kan kashe wanda ya lashe wata caca, bayan ta kashe mijinta ta hanyar zuba masa guba a abinci kafin ta banka wa gidansu wuta. Takardun kotu sun […]

Nas ta kashe mijinta don ta auri fursuna

Ana tuhumar wata Nas mai suna Amy Murray da ke aiki a gidan yarin Missouri a kasar Amurka da yunkurin auren wani fursuna da aka yanke wa hukunci kan kashe wanda ya lashe wata caca, bayan ta kashe mijinta ta hanyar zuba masa guba a abinci kafin ta banka wa gidansu wuta.

Takardun kotu sun ce Amy Murray mai shekara 40 tana fuskanta tuhumar kisan kai da haddasa gobara da ya jawo mutuwar mijinta Joshua Murray a ranar 11 ga Disamban bara.

Bincike ya ce an iske mijin ne a mace a dakinsu da ya kone a garin Iberiya, kuma matar tasa ta wa fursunan ta tarho cewa za su iya yin aure, saboda mijinta “ya gama yawo.”

Biniciken kwakwaf kan gawarsa ya nuna an sa masa gubar antifreeze a cikin abinci kuma ta yiwu ya rasu kafin a kone gidan.

A ranar Litinin aka ci gaba da tsare Amy Murray kan lamunin Dala dubu 750, sai dai lauyanta bai amsa sakon waya da aka tura masa ba daga kafar labarai ta AP.

Amy ta kai rahoton cewa tana dawowa da dansu mai shekara 11 da karnukansu biyu daga shagon McDonald ne ta iske gidansu yana cin wuta, inji wani mai bincike na ’yan sandan yankin.

Ta ce ta kasa shiga gidan saboda ya cika da hayaki.  Amma masu bincike sun gano abincin McDonald a dakin girkin gidan da ke da nisan kilomita 225 daga birnin Kansas.

Murray ta yi aiki na wani lokaci a gidan yarin inda suka rika lalata da furunan mai suna Eugene Claypool na wani lokacin kamar yadda mahukunta suka fadi. Claypool ya taba kashe wani tsoho ta hanyar daba masa wuka a shekarar 2000.

Amy Murray ta bayyana wa Eugene Claypool mai shekara 40, cewa ba ta son kasancewa da mijinta kuma tana shirin rabuwa da shi. A cewar ’yan sanda Amy Murray ta bayyana wa Claypool za su yi aure  saboda mijinta ya rasu.

Eugene da wani sun kashe Donald Harwick mai shekara 72 mai a gidansa ranar Kirsimetin  shekarar 2000. Hardwick bai iya tafiya sai da sanda ya lashe cacar Dala miliyan 1 da dubu 700 a 1998, kuma Claypool da abokin ta’asarsa sun yi kokarin kwace Dala dubu 10 ne daga gare shi.

 

 

 

Ambaliya: Binani ta bai wa Maiduguri tallafin 50m

An sallami sojar da ta zargi shugabanta da neman lalata da ita

CBN ya ƙara kason kuɗin ruwa zuwa 27.25 cikin 100

Hatsarin kwalekwale ya ci rayuka 4 a Borno