Nasarar Gwamna Gaidam a kotu ta al’ummar Yobe ce – Chilariye
Mataimakin Shugaban Jam’iyyar APC na Jihar Yobe Alhaji Adamu Abdu Chilariye ya ce nasarorin da Gwamnan Jihar Yobe Alhaji Ibrahim Gaidam da Jam’iyyar APC ke samu a kotunan sauraren kararrakin zabe a kan Jam’iyyar PDP da cewa nasara ce daga Allah a wurin al’ummar jihar baki xaya. Kuma ya warware zare da abawa game da […]
Mataimakin Shugaban Jam’iyyar APC na Jihar Yobe Alhaji Adamu Abdu Chilariye ya ce nasarorin da Gwamnan Jihar Yobe Alhaji Ibrahim Gaidam da Jam’iyyar APC ke samu a kotunan sauraren kararrakin zabe a kan Jam’iyyar PDP da cewa nasara ce daga Allah a wurin al’ummar jihar baki xaya. Kuma ya warware zare da abawa game da matakan da jam’iyyarsu ke shirin xauka a kan wasu ’ya’yan jam’iyyar da suka yi mata zagon kasa a zaben da ya gabata:
Aminiya: Me za ka ce game da nasarorin da jam’iyyarku ta APC da Gwamnan Jihar Yobe Alhaji Ibrahim Gaidam ke samu a kotunan sauraren kararrakin zabe?
Chilariye: To babu abin da zance sai gode wa Allah da Yake ba da nasara ko akasin haka ga duk wanda Ya so. Magana ta gaskiya duk nasarorin jam’iyyarmu ta APC da Gwamna Gaidam ke samu nasara ce daga Allah da ya bayar ga Jam’iyyar APC da illahirin al’ummar Jihar Yobe ba shi Gwamna Gaidam kaxai ba.
Da tun farko abokin karawar Gwamnan Alhaji Adamu Waziri ya rungumi kaddara kan abin da Allah Ya zartar da ba a yi ta kai ruwa-rana a kotuna ba, tunda a halin da Jihar Yobe ke ciki ga duk mai hangen nesa ya san cewa ba shari’a muke bukata ba, sai dai yadda za a yi mu samu xorewar zaman lafiya.
Aminiya: Kana ga bai yi wuri ba wajen nuna murnarku tunda akwai sauran tsallen da ke gabanku a Kotun koli idan xan takarar PDP ya kaukaka kara?
Chilariye: To ai batun murnar ta koma ciki game da haka da yardar Allah babu, domin in aka duba duk hujjojin da PDP da xan takararta guda bakwai da suka dogara da su kotunan sun yi watsi da su. To ai ka ga muna da karfin gwiwar samun nasara a Kotun kolin koda a ce ya ruga can. Domin kotun za ta dubi hukunce-hukuncen da kotunan baya suka zartar ne don xora nasu a kai. Don haka muna da kyakkyawar fatar sake samun nasara.
Aminiya: A zabubbukan baya jam’iyyarka ta APC ta gaza lashe zabe a shiyyar da ka fito, inda ake zargin waxansu ’ya’yan jam’iyyar da yi mata zagon kasa, mene ne gaskiyar lamarin?
Chilariye: Dangane da rashin samun nasara da Jam’iyyar APC ta yi a yankinmu na Zone B, kowa ya san wasu ’ya’yan jam’iyyar ne marasa kishi suka yi mata zagon kasa saboda son ransu.
Aminiya: Tunda kun gano haka wane mataki kuke shirin xauka a kai?
Chilariye: A yanzu haka mun zauna mu da masu da ruwa da tsaki na jam’iyyar, inda muka xauki matsaya a kan waxanda suka yi mana zagon kasa a kananan hukumomin Potiskum da Fune da Nangere da Fika da Bade da Nguru, mun yanke hukuncin za mu ladabtar da su domin zama darasi ga wasu.
Aminiya: Ko ka gamsu da irin hanyar da Gwamnatin Tarayya take bi wajen kula da yankin Arewa maso Gabas?
Chilariye: Hakika na gamsu da irin matakan da Gwamnatin Tarayya take xauka a wannan yanki namu da ke fama da tashin hankalin Boko Haram. Kuma mun gamsu da irin mukaman da aka ba mu tubarkallah!
Aminiya: Mece ce fatarka ga gwamnatin Gaidam?
Chilariye: Fatata ga gwamnatin Alhaji Ibrahim Gaidam ita ce, kwamishinoni da masu ba shi shawara kada su naxe hannunsu su zura wa Gwamna ido game da harkokin ma’aikatunsu, akwai bukatar su rika kokarin inganta ayyuka tare da nemo tallafi daga tarayya da hukumomi da cibiyoyi na kasashen waje da na Majalisar Xinkin Duniya.