Nasarar Shugaba Buhari: Abubuwan da suka wajaba a kanmu
Daga Hudubar Injiniya Isma’il M. Cindo Gotomo Masallacin Juma’a na Haliru Abdu, Birnin Kebbi Huduba ta Farko Dukan yabo da godiya sun tabbata ga Allah, Ubangijin talikai. Shi ne Mai rinjaya bisa ga bayinSa, kuma Shi ne Mabuwayi, Mai hikima, Mai ji, Mai gani, Mai tausayawa ga bayinSa, kuma Mai karbar addu’o’insu! “Shin wane […]
Daga Hudubar Injiniya Isma’il M. Cindo Gotomo
Masallacin Juma’a na Haliru Abdu, Birnin Kebbi
Huduba ta Farko
Dukan yabo da godiya sun tabbata ga Allah, Ubangijin talikai. Shi ne Mai rinjaya bisa ga bayinSa, kuma Shi ne Mabuwayi, Mai hikima, Mai ji, Mai gani, Mai tausayawa ga bayinSa, kuma Mai karbar addu’o’insu! “Shin wane ne yake karba wa mai tsananin bukata idan ya roke shi, kuma Ya sanya ku mamaya a kasa? Shin akwai wani abin bautawa tare da Allah? Kadan kwarai kuke yin tunani.” (Namli: 62). Ya Allah, Ka yi salati da sallama ga wannan da Ka aiko shi yana rahama ga talikai – wato Annabinmu Muhammad (SAW) da jama’ar gidansa da sahabbansa baki daya.
Bayan haka, ya ku bayin Allah!Hakika ya wajaba mu gode wa Allah a kan ni’imominSa da Ya yi mana, wadanda ba su kidayuwa, ba su lissafuwa.”Kuma idan kun kidaya ni’imar Allah, ba ku iya lissafa ta. Lallai ne Allah, hakika, Mai gafara ne, Mai jinkai.” (Nahl: 18).
Ba shakka, daga cikin ni’imomin da Allah Ta’ala Ya yi mana a wannan kasa (Najeriya) akwai gudanar da zaben Shugaban Kasa da wakilan Majalisar Dokoki ta Kasa (na bana) lami lafiya a mafi yawan wurare illa dan abin da ba a rasa ba, alhamdu lillah.
Bayan haka, lallai ne mu gode wa Allah a kan nasarar mutumin da aka san shi cewa shi mai gaskiya ne, mai rikon amana, mai adalci, dattijo, jarumi, mai hakuri, mai kyakkyawan ra’ayi da hangen nesa. Mai bin abubuwa a hankali tare da tabbata a kan manufa, fitacce a cikin warinsa, kuma aminin al’ummarsa, wato Shugaba Muhammadu Buhari, wanda muke rokon Allah Ya dauwamar da kariyarSa gare shi. Ai da Allah Ya so da Ya jarrabe mu da wani shu’umin mutum, amma alhamdu lillah, Allah bai yi mana haka ba. Ya Allah mun gode! Ya Allah muna rokonKa (domin rahamarKa), har abada kada Ka danka shugabancinmu a hannun wanda ba ya jin tsoronKa game da mu, kuma ba zai tausaya mana ba!
Ku tuna fa, ya ’yan uwa ’yan Najeriya! Daga cikin ni’imomin da Allah Ya yi mana, akwai samar da mu da Ya yi a wannan kasa (Najeriya) wadda ake girmamawa kuma ake darajantawa a Nahiyar Afirka (da sassan duniya). Kasa ce makekiya mai yawan albarkatu daban-daban (irin su kasar noma da ruwan sama da ruwan kasa da itatuwa da sauransu), da yanayi mai kyau, wanda ya dace da sha’anin noma da sauran bukatun dan Adam da arzikin hasken rana da sauran arzukan kasa daban-daban, irin su ma’adinai wadanda ba zan iya lissafo su ba a yanzu! Ga kuma arzikin yawan jama’a, wadanda da yawansu masu basira ne, masha Allah!
To, bugu da kari kuma yanzu, ga shi Allah Ya kara mana da Shugaban Kasa haziki, mai mutunci kuma amintacce (ba maciyin amana ba, ba azzalumi ba). Ke nan, komai ake bukata na ci gaba Allah Ya ba mu. To, ko muna da wata hujjar rashin yunkurawa mu ci gaba a yanzu, kamar yadda wasu kasashe suka ci gaba a kan samun hazikai kuma amintattun shugabanni?
Ya ku ’yan uwa! Hakika idan Allah Ya yi maka ni’ima ka gode, Zai kara maka, idan kuwa ka butulce, za ka sha azaba mai tsanani, kamar yadda Ya fada a Alkur’aninSa cewa: “Kuma a lokacin da Ubangijinku Ya sanar; lallai ne idan kun gode (wa ni’imaTa), hakika ina kara muku, kuma lallai ne idan kun kafirta, hakika azabaTa, tabbas mai tsanani ce.” (Ibrahim: 7). Ya Allah! Ka kare mu daga azabarKa a duniya da Lahira. Ya Allah! Ka yi salati da sallama ga shugabanmu, bawanKa, AnnabinKa kuma ManzonKa Muhammad (SAW), wanda bai koyi karatu da rubutu daga wani mutum ba; tare da jama’ar gidansa da sahabbansa baki daya.
Huduba ta Biyu
Dukan yabo da godiya sun tabbata ga Allah Ubangijin talikai. Tsira da aminci su tabbata ga Annabinmu Muhammad (SAW) mai karimci.
Bayan haka, ya ku ’yan uwa! Hakika, muna fahimtar cewa daga cikin darussan da za mu iya fa’idanta da su daga sakamakon wannan zabe (na Shugaban Kasa da Majalisar Dokoki ta Kasa) akwai:
- Muhimmancin dogaro ga Allah:
Ba shakka, duk wanda ya amince wa Allah, ya dogara gare Shi ga duk abin da ya same shi (ko ya dame shi), to lallai Allah Zai isar masa. Da ma Ya ce: “Kuma wanda ya dogara ga Allah, to Allah ne Ma’ishinsa.” (Dalak: 3). Don haka, sai ka tarar duk makircin masu makirci ya kare a wofi; karshenta ma ya kasance karin bakin ciki ga masu kulla shi; da yake Allah Yake shigar wa muminai yaki, kuma da ma Allah Mai karfi ne, Mabuwayi!
- Muhimmanci da kuma karfin addu’a a komai:
Alhamdu lillah, bayin Allah sun roki Allah. Kuma Allah Ya karba! Da ma addu’a ce makamin mumini, kuma tana daga cikin mabudan yaye damuwa. Kuma hakika Allah Ya ce: “Ku roke Ni In karba muku….” (Ghafir: 60).
- Muhimmancin yawan jama’a da samun hadin kansu:
Dayake a gasar kokawar dimokuradiyya, wanda duk ya fi yawan jama’a shi zai yi kaye; to hakika mun ga amfanin yawan al’ummarmu da kuma hadin kansu a Arewacin kasar nan da ma Kudacinta! Alhamdu lillah, Allah Ya kara wa yawanmu albarka, kuma Ya kara mana hadin kai. Wannan wani babban makami ne da Allah Ya ba mu, wanda bai kamata mu yi sake da shi ba, kuma bai kamata mu bari wadansu na daban su sace mana ko su lalata mana shi ba! An ce: “Hadin-kanku shi ne karfinku!” Wato kamar yadda ake cewa da Ingilishi: “United we stand, dibided we fall!”
Bayan haka, ya ’yan uwa! A matsayinmu na masu imani kuma ’yan kasa, ya kamata (ko ya wajaba) mu himmatu da wadannan abubuwa daga yanzu, domin kyautatuwar al’amurranmu da na kasa baki daya, ta yadda za mu samu ci gaba insha Allah:
- Dogewa da imani da Allah da biyayya gare Shi. Wannan shi ne mabudin dukan alheri.
- Siffantuwa da kyawawan dabi’u ko halaye irin su gaskiya da rikon amana da adalci da sauransu.
- Yarda da halal (wato mu yi hakuri mu tsaya a kan abin da yake halalinmu kawai), da kokarin nemanta da kuma nisantar zama cima-zaune.
- Mu zama masu bin doka da oda, sai fa abin da ya saba wa dokar Allah.
- Mu lizimci hakuri da kuma addu’ar alheri ga kawunanmu da shugabanninmu da kasarmu da sauran kasashen Musulmi. Kuma mu zama masu himmar gaske ga ayukkanmu na yau-da-kullum (na alheri da), na neman abin masarufi.
- Yi wa shugabanni nasiha a cikin tausasawa.
- Sanar da su (shugabanni) abin da saninsu bai kai gare shi ba na hakkokin jama’arsu.
- Taimaka musu ga zartar da ayyukan alheri da kuma kawo gyara.
- Kada a rude su da yabon karya (na fadanci kawai).
- Su kuma shugabanni, a takaice, ya wajaba su ji tsoron Allah, su kiyaye amanar bayinSa. Hakika, Allah Zai tsayar da su a gabanSa a Ranar Kiyama, Ya tambaye su! An ambata a litaffen Shehu Usmanu mai suna Usulul – Adli Li Wullatil Umuri Wa Ahlil Fadli cewa: “Daga cikin abin da ke nuna girman darajar shugabanci tare da girman hadarinsa, akwai zancensa (Annabi) Mai tsira da amincin Allah cewa: “Mafi soyuwar mutane zuwa ga Allah, kuma wanda ya fi su kusanci zuwa gare Shi, shi ne shugaba adali. Kuma wanda Allah Ya fi kyama, kuma Ya fi nisa gare Shi daga cikin mutane, shi ne azzalumin shugaba.”
Allah Ya amfanar da ni da ku da abin da muka saurara. Ya Allah, Ka ba mu abu mai kyau a duniya, kuma Ka ba mu mai kyau a Lahira, kuma Ka kare mu daga azabar wuta! Ya Allah! Ka saukar da zaman lafiya da aminci a kasarmu da dukan kasashen Musulmi. Ya Allah! Ka aza Shugaban Kasarmu Muhammadu Buhari ga abin da yake nan ne maslahar kasa da ’yan kasa take. Ya Allah! Ka taimake shi da abokan shawara nagari. Ya Allah! Kada Ka sake bari ashararan mutane su shugabance mu har a nade kasa, domin rahamarKa.
Tsira da Amincin Allah su tabbata a Annabinmu Muhammad da jama’ar gidansa da sahabbansa baki daya.
Wassalamu ‘alaikum wa rahmatullah.
Za a iya samun Injiniya Isma’il M. Cindo Gotomo (MNSE, MNIAE) ta tarho: (08036049452, ko imel: [email protected])