Nasarata a harkar fim ta Shah Rukh Khan ce – Hrithik Roshan
Ya kasance daya daga cikin ’yan wasa masu tashe a Indiya, wanda ya kasance mafi harka, wanda a kullum cikin aikin shirya fim yake. Ana maganar jarumi Hrithik Roshan ke nan. Shi ne a kwanan nan ya cira wa Shah Rukh Khan hula, ya ce duk wata nasara da ya samu a harkar fim, ta […]

Ya kasance daya daga cikin ’yan wasa masu tashe a Indiya, wanda ya kasance mafi harka, wanda a kullum cikin aikin shirya fim yake. Ana maganar jarumi Hrithik Roshan ke nan. Shi ne a kwanan nan ya cira wa Shah Rukh Khan hula, ya ce duk wata nasara da ya samu a harkar fim, ta biyo bayan dan wasan ne.
Roshan, dan shekara 39 ya ce da ba domin tallafi da nunin da ya samu daga kamfanin Shah rukh Khan, ‘Red Chillies Production’ ba, da bai samu nasara gamsasshiya da fim dinsa na ‘Krrish 3’ ba.
Kamar yadda wata jarida ta ruwaito a Indiya, Hrithik ya yaba wa jarumin ne saboda yadda ya inganta fim din da mahaifinsa Rakesh Roshan ya shirya, wanda kuma yake kan hanyar fitowa a yanzu.
“Da baicin tunanin Shah Rukh Khan, da kamfaninsa na Red Chillies bai kasance ba, kuma da fim din nasa ‘Krrish 3 bai samu tagomashi da tarairayar da ya samu ba. Mun samu nasarar samun ingancin da muke son samu a fim din ne duk saboda hazakarsa.” Inji Hrithik.
Ya zuwa yanzu dai, Roshan ya takarkare, ba ji ba gani, yana aiki kan fim din, wanda ake tsammanin fitar da shi kasuwa, nan da watan Nuwamba mai gabatowa.
“Muna ta kokari ne mu ga cewa mun cin ma wani abu mai muhimmanci, muna son ganin mun fitar da wani abin al’ajabi, wanda a can baya za a yi tsammanin ba za a iya yi ba a fim a shekarun baya.” Inji jarumin.
A wannan sabon fim, Priyanka Chopra ce za ta maimata rawar da ta taka a kashin farko na ‘Krrish’ wanda ya fito a 2006. Sauran ’yan wasan da suka fito tare da Hrithik da Priyanka, sun hada da bibek Oberoi da Kangna Ranau da sauransu.