Nasarata daga Allah take – Injiniya Ahmed Manir
Injiniya Ahmed Manir na Jam’iyyar APC wanda ya lashe zaben kujerar Majalisar Wakilai Lere a Jihar Kaduna bayan ya kayar da Alhaji Muhammad Lawal Rabi’u na Jam’iyyar PDP da ke kan kujerar ya ce nasararsa daga Allah take. Da take bayyana sakamakon zaben a garin Saminaka, Babbar Jami’ar Hukumar Zabe, Farfesa Maryam Suleiman ta ce […]
Injiniya Ahmed Manir na Jam’iyyar APC wanda ya lashe zaben kujerar Majalisar Wakilai Lere a Jihar Kaduna bayan ya kayar da Alhaji Muhammad Lawal Rabi’u na Jam’iyyar PDP da ke kan kujerar ya ce nasararsa daga Allah take.
Da take bayyana sakamakon zaben a garin Saminaka, Babbar Jami’ar Hukumar Zabe, Farfesa Maryam Suleiman ta ce Ahmed Mannir na Jam’iyyar APC ya samu kuri’a dubu 64 da 442, yayin da Alhaji Muhammed Lawal Rabi’u na Jam’iyyar PDP ya samu kuri’a dubu 29 da 706. Don haka ta ce Ahmed Mannir ne ya lashe zaben.
Da yake zantawa da wakilinmu bayan sanar da sakamakon zaben, Injiniya Ahmed Mannir ya bayyana jin dadinsa bisa irin goyon baya da hadin kan da al’ummar Karamar Hukumar Lere suka ba shi. Sannan ya ce ya ji dadin yadda aka yi zaben cikin kwanciyar hankali kuma aka bar jama’a suka zabi abin da suke so.
‘’Babu abin da zan ce wa al’ummar Karamar Hukumar Lere sai dai in mika godiyata a gare ku. Kuma da yardar Allah zan rike wannan amana da kuka damka mini,” inji shi.
Ya ce dukan al’ummar karamar hukuma sun gane wa idanunsu irin ayyukan da ya fara tun kafin a zabe shi. Don haka ya yi kira a ci gaba da yi masa addu’a domin ya ci gaba da gudanar da ayyukan tallafa wa jama’a da kyautata rayuwarsu domin nasararsa daga Allah take.