An haramta aikin ’yan banga a Jihar Nasarawa

Gwamnatin Nasarawa ta haramtar ayyukan duk kungiyoyin ‘yan banga da ke aiki a faɗin ƙananan hukumomi 13 na jihar.

An haramta aikin ’yan banga a Jihar Nasarawa

Gwamnatin jihar Nasarawa ta dakatar  da duk wata Ƙungiyar ’yan banga da ke aiki a faɗin ƙananan hukumomi 13 na jihar.

Gwamnatin jihar ta kuma haramta duk wata ƙungiya, ko rukunin al’umma da ke da alaƙa da ƙungiyar da ke gudanar da ayyukanta a ƙarƙashin ’yan banga na ƙabila.

Hakan na zuwa ne bayan taron gaggawa kan harkar tsaro da Gwamna Abdullahi Sule ya kira.

Gwamnatin jihar ta kuma ba da wa’adin makonni biyu ga ɗaukacin ƙungiyoyin ’yan bangan su miƙa kakinsu da makamansu ga Kwamishinan ’yan sandan jihar, Shehu Nadada.

A kalamansa, “Irin wannan kungiyoyi sun haɗa da kowace kungiya, mai aiwatar da aiyuka ko ƙungiyar mutane ko jama’a ta kowace irin suna ko kafa, da manufar samar da tsaro a tsakanin wasu ƙabilun Jihar Nasarawa ta hanyar amfani da ƙarfi ko makamai da sauransu,” in ji shi.

A cewarsa, “Kungiyar Zaman Lafiya ta Nomad Vigilante, Bassa Vigilante, Eggon Vigilante da makamantansu daga yanzu an haramta su.”

Hamas da Isra’ila sun cimma yarjejeniyar tsagaita wuta a Gaza

HOTUNA: Yadda aka yi bikin tunawa da mazan jiya a faɗin Nijeriya

Sanusi zama daram kuma Sarki ɗaya tilo a Kano — Falana

An rantsar da Shugaban Mozambique Daniel Chapo