Nasarawa: ’Yan Sanda Sun Gargadi Jam’iyyu Gabanin Hukuncin Kotun Daukaka Kara
Rundunar ’yan sanda a jihar Nassarawa ta hori jam’iyyun siyasa da magoya bayansu da su guji tayar da tarzoma gabanin zaman kotun daukaka kara kan zaben gwamnan jihar. Mukaddashin kwamishinan ’yan sandan jihar, Shettima Muhammad, shi ne ya yi wannan gargadi a wani taron manema labarai da ya kira jiya litinin a garin lafiya. “Rundunarmu […]
Rundunar ’yan sanda a jihar Nassarawa ta hori jam’iyyun siyasa da magoya bayansu da su guji tayar da tarzoma gabanin zaman kotun daukaka kara kan zaben gwamnan jihar.
Mukaddashin kwamishinan ’yan sandan jihar, Shettima Muhammad, shi ne ya yi wannan gargadi a wani taron manema labarai da ya kira jiya litinin a garin lafiya.
“Rundunarmu da sauran hukumomin tsaro za su tabbatar da jihar Nasarawa ta zauna lafiya, gabanin da lokacin yanke hukuncin, kuma za mu sa ido kan duk abubuwan da ka iya biyo baya.
“Duk wanda ya nemi tayar da tarzoma da sunan murna ko akasin haka, zai fuskanci fushin hukuma” inji mukaddashin kwamishinan.
- Ganduje ya yi alhinin rasuwar Darakta Aminu S. Bono
- Makiyan Kwankwaso ke neman a kwace kujerata —Abba
Haka zalika, ya ce an baiwa kowa a jihar damar ci gaba da harkokinsa kamar yadda aka saba.
A hukuncin baya da kotun karbar korafin zabe ta yanke, ta soke nasarar zaben Gwamna Abdullahi Sule, ta bayyana David Umbugadu na jam’iyyar PDP a matsayin wanda ya samu nasara.
Sai dai Gwamna Sule ya daukaka kara zuwa kotun gaba, inda yake nuna rashin gamsuwarsa da hukuncin da kotun farko ta yanke.