Nasarorina taimako ne daga Allah – Dogara

Shugaban Majalisar Wakilai Honourabul Yakubu Dogara ya ce nasarorin da ya samu a harkokin siyasarsa taimako ne daga Allah, inda ya ce ya sadaukar da dukan nasarorin ga al’ummar mazabarsa domin amincewar da suka nuna masa ne suka sake zabensa. Da yake jawabi a wajen taron karramawar da al’ummar mazabarsa suka shirya masa don bikin […]

Nasarorina taimako ne daga Allah – Dogara

Shugaban Majalisar Wakilai Honourabul Yakubu Dogara ya ce nasarorin da ya samu a harkokin siyasarsa taimako ne daga Allah, inda ya ce ya sadaukar da dukan nasarorin ga al’ummar mazabarsa domin amincewar da suka nuna masa ne suka sake zabensa.

Da yake jawabi a wajen taron karramawar da al’ummar mazabarsa suka shirya masa don bikin cikarsa shekara 50 a ranar Asabar da ta gabata a garin Bogoro da ke Jihar Bauchi, Barista Yakubu Dogara ya ce, mutanen Bogoro da Dass da Tafawa Balewa ne suka share hanyar zamansa Shugaban Majalisar Wakilai saboda sake zabensa duk da kalubale da adawar da ya fuskanta, kuma wannan ne ya kai shi matsayin da zai iya yin tasiri wajen kawo musu ayyukan ci gaba da za su amfani mazabar da Jihar Bauchi da kuma yankin Arewa maso Gabas.

Shugaban Majalisar wanda ya yi godiya ga Allah kan yadda Ya ba shi damar cimma dimbin nasarorin da ya samu, ya ce ya fi damuwa ya samu damar yi wa jama’a hidima maimakon samun mukamin mulki. “Ba ni sha’awar mukami, ina sha’awar yi wa jama’a hidima ce. Mukami ba ya da wani amfani a wurina, abin da na fi so shi ne in yi wa jama’a hidima. Idan na kammala aikina na dan majalisa Ubangiji zai gusa da ni zuwa wani matsayi da zan kara yin hidima ga jama’ata. Ba domin taimakon Allah ba, ba zai yiwu in samu wadannan abubuwa ba, kuma wannan ne ya sa muke nan domin yin godiya ga Allah kan yin amfani da ni hakan ya samu, ba wai don murnar haihuwata ba, a’a don mu yin godiya ga Allah,” inji shi.