Nasiha daga masu karatu
Assalamu alaikum, barkanmu da sake haduwa a wannan fili, da fatan Allah Ya amafanar da mu dukkan bayanan da za su zo cikinsa, amin. Ga gudummuwar karin bayani da nasihohi da masu karatu suka aiko: Assalamu alaikum. Ina jan hankali da nasiha ga matan aure da su yi wa kansu gata su rabu da bin […]
Assalamu alaikum, barkanmu da sake haduwa a wannan fili, da fatan Allah Ya amafanar da mu dukkan bayanan da za su zo cikinsa, amin. Ga gudummuwar karin bayani da nasihohi da masu karatu suka aiko:
Assalamu alaikum. Ina jan hankali da nasiha ga matan aure da su yi wa kansu gata su rabu da bin bokaye da ’yan tsibbu don samun soyayyar miji. Shi fa miji ba komai ba ne iyaka dan Adam ne kamarki; kowane irin asiri za ki yi, ba ki taba mallake shi gaba dayansa don ba wannan ne dalilin kasancewarsa a duniya ba. To wai in namiji bai so ki ba sai me? Ki yi kokari ki nemi Allah da Ya halicce ki Ya wadata ki da komai da kike bukata, har mijin da kike kokarin sayar da rabon Lahirarki saboda shi Allah ne Ya ba ki shi; in Allah Ya so ki dole mijinki Ya so ki kamar yadda Ya tabbata a Hadisi cewa in Allah Ya so mutum zai yi umarni ga Mala’ika Jibrilu Ya sa dukkan mutane su so wannan mutum; in dai kin rike Allah ko mijinki bai so ki ba, shi ya yi asara ke kuma har abada kin ci gaba. Akwai darasi a rayuwar aurena, mun zauna da mijina shekara 15 muna faman zaman gidan haya; mafi yawan lokuta ni nake biyan kudin haya saboda sana’a iri-iri da nake tabawa. Duk da haka ban taba nuna raini ga mijina ba. Har Allah Ya sa na samu gadon gona bayan rasuwar mahaifina, na sayar da gonar na saya mana gida dan karami muna zaune ina ta sana’a. Amma da yake namiji namiji ne, da ya samu kudin aje aikin masinjan da yake yi sai ya sayi sabon gida rin na zamani ya yi sabon auren budurwa tamkar ’yar cikinsa. Ciwo da kunar zuciya suka zurfafa saboda wulakancin da ya rika nuna mini da taimakon amaryarsa. Ya kasance ko ranar aikina can wajenta yake yini wata sa’ar har kwana yake yi, idan na tanka ya rufe ido ya zazzage ni. Labarina ya bazu cikin unguwa. ’Yan uwa mata aka yi ta kawo mini gudunmawar ban baki da tausan kirji, kowa nuna mini yake sai na tashi tsaye na shiga malamai in ba haka ba sai an raba ni da mijina. Na zauna na yi karatun ta-natsu na ce to da wannan aure ya haifar mini da wata cuta ko ya kai ni ga sabon Allah gara in hakura da shi; don haka na roki ya sawwake mini, nan da nan kuwa kamar yana jira. Cikin ikon Allah sana’o’ina suka kara bunkasa har na je Makka yarana kuma suka hadu suka gyara mini gidana ya koma ginin zamani. Shi kuma daga karshe sai da ya sayar da gidansa saboda bashi da ya rika ci yana saya wa matarsa kayan dadi. Yanzu soyayya ta kare kullum sai fada makwabta na jin su saboda auren ne ba saboda Allah aka yi shi ba. Yanzu kusan kullum sai ya zo gidana rokon na cefane; yaransa hudu kusan kullum a gidana suke cin abinci. Don haka ’yar uwa ki yi wa kanki gata kada ki hallakar da kanki saboda da namiji; ba komai ba ne shi illa mutum kamarki. Shi in bai nemi asirin neman soyayyarki ba ke don me za ki sayar da imaninki ga Shaidan wajen bin bokaye don ya so ki? Da fatan mata masu bin bokaye za ku yi wa kanku fada ku gane gaskiya ku tuba kafin mutuwa ta riske ku, ku yi biyu babu!
-Hajiya Baraka
Na karanta tambayar wanda ya kama matarsa ta yi masa asiri; to gaskiya ’yan uwa maza a yi hankali wajen zabar macen aure kuma a kula da tarbiyyar mata bayan aure; don irin haka ya taba faruwa ga wani dan uwa, mai kawo mata sihirin ba ta san yana dakin ya kudundune a gado ba ya da lafiya saboda tana cikin sauri da kuma dubunsu ta cika ta hau zayyana wa matar wannan a abinci za ki sa masa, wannan a fura, wannan a kaza ,wannan a kaza. Daga ranar bai kara yi mata magana ba, ba ya shiga dakinta, bai cin abincinta; ga shi sun tara iyali da yara kanana ba damar ya rabu da ita, sai ya zama garin neman soyayya an rasa wanda ake son gaba daya. Don haka mata ku ji tsoron Allah, ku kama kanku, ku daina cin amanar mazanku da yi musu asiri. Akwai mamaki yin asiri ga abin da kake ikirarin wai kana so domin shi asiri fa babban al’amari ne don haka ku yi hattara.
-Malam Isa Abdullahi
Ni kam al’amarin bin bokaye da mata ke yi ya sa nake tsoron yin auren ma; don yanzu ko ka samu ka auri salihar macen sai ka ga ta juye tana abin da wadda ba salihar ba ma ba za ta iya yi ba. Wadansu makwabtan juna sun kasance uztazai hijabi na jan kasa, ga nikabi kullum suna hanyar zuwa Islamiyyya ashe duk na banza ne da dubunsu ta cika Shaidan ya hada su fada suka yi ta tona wa juna asiri; don haka abin sai dai neman taimakon Allah.