Nasiha ga iyaye mata
Editan Aminiya ku mika sakona ga iyaye mata, ku nema wa kanku mafita a dimokuradiyya.Ku sani an sace ’ya’yanku yan’matan makarantar sakandiren Chibok fiye da 271, har yanzu babu wani yunkuri da gwamnati ke yi, don ceto rayuwarsu. Ga yan’uwanku mata wadanda suka rasa mazajen su a Jihohin Arewa, musamman Arewa maso Gabas da Filato […]
Editan Aminiya ku mika sakona ga iyaye mata, ku nema wa kanku mafita a dimokuradiyya.Ku sani an sace ’ya’yanku yan’matan makarantar sakandiren Chibok fiye da 271, har yanzu babu wani yunkuri da gwamnati ke yi, don ceto rayuwarsu. Ga yan’uwanku mata wadanda suka rasa mazajen su a Jihohin Arewa, musamman Arewa maso Gabas da Filato da Nasarawa da Taraba da Kaduna da Kano. Dubban mata a wadannan jihohin sun rasa mazajensu ta hanyar hare-hare a jihohin, mata da dama sun koma zawarawa. Kada ku zabi wadanda za su jefa ku cikin bala’i. Daga Mansoor Said PRP Kano. 07039215954.