Nasiha ga iyayen da ke barin tarbiyyar ’ya’yansu a wajen wasu (4)

Bayan Hassana ta rarrashe ta ne don ta fada mata idan ta debi kudin me take yi da su?  Sai ta nuna tana zuba su ne a bola a matsayin ba ta san darajar kudi ba.  Da Zuwaira ta ji hayaniya sai ta yi wuf ta shiga dakin don kare kanta, inda ta kare Amira […]

Nasiha ga iyayen da ke barin tarbiyyar ’ya’yansu a wajen wasu (4)

Nasiha ga iyayen da ke barin tarbiyyar ’ya’yansu a wajen wasu

Bayan Hassana ta rarrashe ta ne don ta fada mata idan ta debi kudin me take yi da su?  Sai ta nuna tana zuba su ne a bola a matsayin ba ta san darajar kudi ba.  Da Zuwaira ta ji hayaniya sai ta yi wuf ta shiga dakin don kare kanta, inda ta kare Amira da cewa watakila tana watsar da kudin ne tun da ba ta san darajarsu ba. Nan dai Hassana da Zuwaira suka hadu suka yi wa Amira fada da kada ta sake aikata irin haka.

Duk abin da ake yi Hassana ba ta san wainar da ake toyawa ba.  A lokacin dai asirin Zuwaira ne bai tonu ba.

Ba a jima ba sai Zuwaira ta shiga jibgar Amira bayan an daukota daga makaranta tana fadin za ta kashe ta, tun da ta daina satar kudi tana kai mata.  A lokacin da take jibgar Amira da tsakar rana ne, ba ta yi zaton wani daga cikin iyayen Amira zai iya komawa gida a lokacin ba.

A daidai lokacin, mijin Amira Likita Kabiru ya koma gidan don ya dauki wadansu muhimman takardu.  Tun a waje yake jin hayaniya, da alamar wani abu yana faruwa a cikin gidansa.  Ya sanya mabudi ya bude kofa daga waje ba tare da sanin Zuwaira da Amira ba.  Shigarsa falon ke da wuya sai ya tarar Zuwaira tana tattaka Amira, ta ji mata ciwo, jini sai kwarara yake yi daga bakinta.  Ta fara fita daga hayyacinta.  Nan take Kabiru ya dakawa Zuwaira tsawa.  Nan fa ido ya raina fata, don ta san asirinta ya tonu, sai ta ruga cikin dakinta a guje ta kulle kofa.

Da Kabiru ya ga haka sai ya yi wuf ya dauki Amira don kai ta asibiti, amma kafin ya fita sai ya kulle kofofin gidan daga waje, kuma ya umarci maigadi kada ya kuskura ya bar Zuwaira ta fita daga gidan har sai ya dawo.

Daga nan Kabiru ya kira matarsa Hassana a waya ya shaida mata halin da ake ciki, kuma ya bukaci ta komo gida don ta kama Zuwaira kafin su mikata hannun ’yan sanda.

A lokacin da Zuwaira ta yi kokarin tserewa  sai ta fahimci an kulleta daga waje, daga nan ne ta rika yin salati tana kiran saurainta a waya don ya ceceta, amma ya ce mata ba ya kusa, ya yi tafiya, alhali karya yake yi.

Nan dai ido ya raina fata, don ta san karya ta kare.  Ba a jima ba sai ga Hassana ta shigo gidan, inda ta yi amfani da mabudi ta bude kofar gidan ta baya.  Ta kuma nemi maigadi ya yi mata rakiya har cikin gidan.

Da Zuwaira ta ji tafiya sai ta shige dakin dafa abinci ta kulle kanta.  Nan dai Hassana da maigadi suka rika bi lungu da sako na gidan amma ba su ga Zuwaira ba.  Can sai Hassana ta ji a jikinta cewa Zuwaira ta shige cikin dakin dafa abinci ta boye.  Nan ta umarci maigadi ya dauko mata maganin kashe kwari inda ta feshe dakin dafa abincin ta taga sannan ta rufe.  Ai ba a yi minti daya ba sai ga Zuwaira ta yi wuf ta fito tana ta tari da kwalla.  Nan Hassana ta shiga jibgar Zuwaira kamar an aikota.

Daga baya mijinta Kabiru ya dawo daga asibiti inda ya shaida wa Hassana an kwantar da Amira amma tana samun sauki.

Nan dai suka mika Zuwaira ga jami’an ’yan sanda inda su kuma suka mikata gaban alkali inda aka yanke mata hukuncin daurin shekara biyu a gidan yari.

Da fatan iyaye za su dauki darasi daga wannan labari musamman wadanda ke barin tarbiyyar ’ya’yansu a wajen wasu.

Za a iya samun Ahmed Garba Mohammed a 08028797883