Nasiha ga maza masu cutar da matansu
Ina yi wa masu bibiyar wannan shafi sallama irin ta addinin Musulunci, Assalamu alaikum. Da fatan kuna cikin koshin lafiya. Kamar kullum, nakan yi sharhi daga lokaci zuwa lokaci ne a kan al’amarrun da suka shafi rayuwa don mu gano wurin da aka samu matsala don a gyara, in kuma na bayar da shawara ce […]
Ina yi wa masu bibiyar wannan shafi sallama irin ta addinin Musulunci, Assalamu alaikum. Da fatan kuna cikin koshin lafiya. Kamar kullum, nakan yi sharhi daga lokaci zuwa lokaci ne a kan al’amarrun da suka shafi rayuwa don mu gano wurin da aka samu matsala don a gyara, in kuma na bayar da shawara ce sai a yi kokari a yi amfani da ita kamar yadda Bahaushe kan ce “gyara kayanka bai zamo sauke mu raba ba”. To a yau zan tabo wani muhimmin batu ne da ke ci wa al’ummarmu musamman ta Hausawa tuwo a kwarya, ba lallai sai Hausawa kadai ba, hakan ya shafi kowace irin kabila ba lallai Hausawa kawai ba. Abu mafi muhimmanci dai shi ne mu yi kokari mu rika yin koyi da darussan da ke cikin labarin da muke kawo wa don mu gudu tare mu kuma tsira tare.
Darasin da zan kawo mana a yau shi ne na yin nasiha ga maza masu cutar da matansu ta hanyoyi daban-daban. Irin haka na faruwa a gidajen aure inda wasu matan sukan fito fili su koka yayin da wasu kuma abin yana ci musu tuwo a kwarya sai dai su bar abin a zuciyarsu kawai ba tare da sun sanar da wani ko wasu ba.
Da farko zan fara ne da irin mazajen nan da suke barin matansu da daukacin iyalinsu cikin yunwa, inda za ka tarar ba sa wadata su da isasshen abinci mai dadi alhali Allah Ya hore musu abin da za su iya ciyar da iyalin. Irin wadannan mazaje za ta tarar in sun kasance a gida sukan nunawa matansu ba su da kudi wai sun buga amma ba su samu ba. Za ka iske suna ta marairaicewa matansu da kalamai na tausayi alhali aljuhunsu cike suke da makudan kudi. Idan matan suka nemi kudin cefane daga irin wadannan mazaje sai ka ji har rantsuwar karya suke yi, da hakan zai sa matan su dangana da Allah kuma su shiga tunanin hanyar da za su bi don a samu rufawa juna asiri. Hakan ke sanya matan su hakura su shiga tunanin irin dababar da za su yi don su ciyar da kansu da ’ya’yansu don a rufa wa juna asiri. Yayin da magidan da zarar ya fita za ka iske ya nufi teburin mai shayi. Abin zai ba ka mamaki irin hadin da zai sa a yi masa a teburin mai shayi inda zai take cikinsa ba tare da tunani ko tausayin halin da ya bar iyalinsa a gida ba. Hakan ta sa na tuno da wani labari, inda wani magidanci bayan ya yi wa matarsa karya bai ba ta ko sisin kwabo bayan ya fita bai zame ko’ina ba sai teburin mai shayi da ke bayan gidansu. An yi masa hadi mai kyau da suka hada da kwai hudu da rabin madara da katon burodi har ruwan leda (pure water) ya sayar inda da zarar ya kammala shan shayin zai kora. Hatta burodin ma sai da aka shafe masa shi da bota (butter), amma abin takaici ya bar iyalinsa cikin kunci da karyawa da abincin da ba shi da nagarta ko dadi.
Ashe bai sani ba, matarsa ta aiki daya daga cikin ’ya’yansu ya sayo mata burodi a wajen mai shayin. Bai ankara ba sai ya hango dansa ya nufo rumfar mai shayin, shi kuwa magidancin saboda rudewa sai ya yi wuf ya juye kwan da aka soya masa cikin hularsa ya mayar da ita kansa. Da dansa ya isa wajen sai ya rika ’yan kame-kame yayin da kwan ke kona masa kai. Allah-Allah yake dan nasa ya gama sayayyar ya wuce. Bayan ya wuce ne sai jama’a suka ga ya ciro hularsa ya juye kwan a cikin wata roba kuma ya ci gaba da ci ba kunya ba tsoron Allah. To irin wannan abu da wannan mutum ya yi da me ya yi kama? Ai duk inda aka ce azzalumi to wannan mutum ya kai, don ya nuna ba shi da tausayi da tsoron Allah. To a nan ka ga yana da kyau wannan magidanci ya ji tsoron Allah, ya sani in shi ne yau, ba shi ne gobe ba.
Haka kuma na samu labarin yadda wani magidanci, wanda ya yi sabon aure, an ce dududu bai wuce wata biyu zuwa uku da auren wata budurwa ba, ya sa kai ya tafi Legas neman kudi. An ce da farko ya fada wa amaryar tasa cewa ba zai wuce kwana 7 zuwa 10 ba zai koma gida amma sai da ya shafe shekaru biyu cur ba ta sake ganinsa ba sai dai aiko sako na kudi da na abinci daga lokaci zuwa lokaci da yake yi mata. Hakan ta sa iyayen amaryar suka ga ba za su iya jure wannan wulakanci na mijin ’yarsu ba inda suka shigar da kara sannan hukuma ta raba su. Bayan an raba auren ne sai ya koma kauyensu inda mahaifinsa ya turke shi ya rika yi masa fada a kan abin da ya aikata. Bude bakinsa ke da wuya sai ya nuna ai yana yi wa tsohuwar matarsa aiken kudi da na abinci da kuma na sauran bukatu a kan kari. Sai mahaifinsa ya ce lallai ya yarda cewa yana yi wa matar tasa aike amma tambayar da yake so dan nasa ya amsa masa ita ce buhunan mazakuta nawa ya ajiye wa matar kafin ya bar gidan? Ma’ana tun da ya ce yana yi matar aiken kudi da na abinci, to a bangaren kwanciyar aure fa? Ba ta da hakki ne a kai? Nan take dan ya gane kurensa kuma ya shiga ba mahaifinsa hakuri da niyyar ba zai sake aikata irin haka ba a nan gaba.
Za mu cigaba insha Allah
Za a iya samun Ahmed Garba Mohammed a 08028797883