Nasiha ga maza masu cutar da matansu (2)

A wani labari makamancin wannan, wani magidanci ne yana tare da matarsa da ’ya’ya bakwai, a daki daya suke kwana saboda talauci, domin ba ya da karfin kama ciki da falo.   Kamar yadda rahoton ya nuna, saboda tsananin rashin wadataccen wurin kwana, magidancin yakan sadu da matarsa ce a cikin ban-dakin da ke gidan tunda […]

Nasiha ga maza masu cutar da matansu (2)

A wani labari makamancin wannan, wani magidanci ne yana tare da matarsa da ’ya’ya bakwai, a daki daya suke kwana saboda talauci, domin ba ya da karfin kama ciki da falo.   Kamar yadda rahoton ya nuna, saboda tsananin rashin wadataccen wurin kwana, magidancin yakan sadu da matarsa ce a cikin ban-dakin da ke gidan tunda gidan haya ne mai dauke da mutane da yawa.  A duk lokacin da ya fahimci kafa ta dauke sai ya kai matarsa cikin ban-daki ya sadu da ita a can. Ashe mutanen gidan sun gane abin da ke faruwa inda suka rika kokawa. Abin mamaki suna cikin wannan hali ne sai Allah Ya hore masa wasu makudan kudi, amma magidancin bai yi wata-wata ba sai matarsa ta ji ya kara aure, hasali ma har ya kama gida yalwatacce a wata unguwa inda ya tare shi da amaryarsa. Sauran iyalinsa kuwa ya yi biris da su tamkar bai san halin da suke ciki ba.  Hakan bai yi wa matar dadi ba, da hakan ya yi sanadiyyar mutuwar aurensu.  Shi ma wannan magidanci ko ba a fada ba an san bai yi wa kansa da iyalinsa adalci ba, maimakon ya yi amfani da kudin wajen kama musu babban gida, sai ya bige da yin sabon aure don biyan bukatarsa.  Ko shakka babu wannan magidanci zai gamu da fushin Allah idan bai tuba ya gyara ba.

Haka kuma an samu labarin yadda wani magidanci ya kara aure kuma a lokacin da yake neman auren bai ma sanar da uwargidansa ba sai daga baya.  To abinka da uwargidan mai tausayi kuma Allah Ya hore mata kudi saboda sana’ar da take yi sai ta amince bayan ya lallashe ta.  Saboda tausayi, da shekara ta zagayo magidancin ya nuna ba ya da kudin da zai ci gaba da biyan kudin haya a gidan da ya kama shi da amaryarsa, uwargidan ce ta ci gaba da biya don su taru su rufawa juna asiri. An ce uwargidan ta dauki lokaci mai tsawo tana biyan kudin hayar sai daga baya ne ta gano ashe gidan mallakar mijinta ne, ba haya yake yi ba.  Hasali ma a duk lokacin da ta biya kudin hayar, magidanta ne yake karbe kudin ba tare da saninta ba. Daga baya ne ta gano kuma hakan ya yi matukar daga mata hankali.  Bayan ta turke shi ne da ya ga babu Sarki sai Allah sai ya fada mata gaskiyar magana cewa shi ya mallaki gidan. Da ta nemi dalilin da ya sa ya yi mata haka, sai ya kasa ba ta gamsasshiyar amsa.  Sai ta tilasta masa ya mayar mata da kudaden da ta dauki tsawon lokaci tana biya masa a matsayin kudin haya.  A karshe da ya ba babu yadda zai yi ne sai ya sayar da gidan ya ba ta kudinta kuma tun daga lokacin ta nuna ba za ta sake yarda da shi ba. To a nan ko ba a fada ba ka san wannan magidanci ya kira wa kansa ruwa, ko dai ba su rabu ba, da wuya ya sake samun zaman lafiya a gidan.  Labarin ya nuna a karshe ma ya rabu da amaryar da uwargidan ne, inda uwargidan ta nuna ba za ta iya ci gaba da zama da azzalumi ba, kamar yadda ita ma amaryar ta nuna akwai yiwuwar ya yaudare ta kamar yadda ya yaudari uwargidansa.  Nan ya yi biyu babu, ba shi ga tsuntsu ba shi ga tarko.  Ya rasa matansa biyu, sannan ya rasa gidansa.  Na san mata da yawa za su goyi bayan abin da uwargidansa ta aikata, na turke shi wajen sayar da gidan da kuma mayar mata da kudin hayar da ta dauki tsawon lokaci tana kashewa a kan mijinta da amaryarsa da sunan biya musu kudin haya.

Wadannan kadan ne daga cikin dubban misalai da wadansu maza ke cutar da matansu.  Ya kamata maza su rika jin tsoron Allah, su sani matansu da iyalansu amana ce Allah Ya ba su.  Matansu da iyalansu suna da hakki a kansu kamar yadda su ma suke da hakki a kan matansu da iyalansu.

Irin wannan hali ne ke sa wadansu mata ke ganin namiji ba dan goyo ba ne, kuma hakan ke sa ake yawan samun matsaloli a gidajen aure.  Zaman aure dai ibada ce kuma ya kamata dukan bangarorin biyu su ji tsoron Allah. Su sani duk bangaren da ya zalunci wani, to Allah Zai yi hukunci a kansa. Don haka ya kamata maza mu ji tsoron Allah, mu rike iyalanmu cikin adalci, duk da dai ba duka aka taru aka zama daya ba.

Za a iya samun Ahmed Garba Mohammed a 08028797883