Nasiha zuwa ga maza (1)
Ba ni da masaniya a kan batun da take son mu tattauna. Ta Intanet ta turo da bayanan da take son mu yi magana a kan su, sa’annan ta nemi in sanar da ita me ya sa matan Hausawa rigunan da suke sanyawa ba su da yawa ko kuma suke sanya rigunan ba daidai ba. […]
Ba ni da masaniya a kan batun da take son mu tattauna. Ta Intanet ta turo da bayanan da take son mu yi magana a kan su, sa’annan ta nemi in sanar da ita me ya sa matan Hausawa rigunan da suke sanyawa ba su da yawa ko kuma suke sanya rigunan ba daidai ba. Ta kuma nemi da in kara mata haske game da yadda matan Hausawan za su iya bin matakin ganin sun sa rigunan nan kamar sauran matan duniya.
Da yake na saba haduwa da irin wadannan tambayoyin cikin shekara 4 da na yi a farfajiyar facebook abin bai dame ni ba, na yi watsi da shi, ganin ayyukan da ke gabana suna da yawan gaske a ranar. Kwanaki ta yi tana ta turo da sakonni, da na ki amsawa sai ta yi min abin da kila ta san cewa zai ja hankalina ko kuma ya tunzura ni in ba ta amsa. Abin da ta ce a sakonta na karshe shi ne, ‘Ko kai ma dai kana cikin mazajen nan da ke daukar mata ba mutane ba, shi ya sa ka ki cewa uffan. Na san a rina, da ma can bayanan da kake yi game da al’amurran yau da kullum kana zabi ne da son kai. Al’amurran mata ba su dame ka ba!’
Na so na sake yin watsi da ita, amma sai wata zuciya ta ce, shiru amincewa ce inji Hausawa. Saboda haka na koma ga bayanan nata na sake karantawa, domin kara fahimta sosai. Ga abin da take cewa a zahiri:
Daga cikin wadannan rigunan da matan duniya ke sawa, wadanne ne matan Hausawa ba su sawa ko ba su sawa yadda ya dace?
*Rigunan sawa ranar sunan da aka haife su
*Rigunan sawa ranar da suka shiga firamare da sakandare
*Rigunan sawa ranar da za su fara karatun jami’a
*Rigunan sawa ranar da suka kammala karatun jami’a
*Rigunan sawa ranar da za su fara hidimar kasa
*Rigunan sawa ranar da za su yi aure
*Rigunan sa wa ranar da suka haihu
A bayanin nata, ta ce da ni in lura da kyau, yadda ta zayyano su, haka ya kamata rigunan su kasance ana sanyawa, ‘wai’ bai dace matan Hausawa su tsallake daya domin zuwa ga wata rigar ba. Alal misali, bai dace matan Hausawa su sanya rigunan aure da zarar sun cire rigunan firamare ko sakandare ba, su bari har sai sun sanya rigunan gama karatun jami’a da yi wa kasa hidima. Ta kara da cewa idan kuma sai sun sa rigunan aure kafin lokacin, to su dage su ga ba su sa rigunan bikin sunan ’ya’yansu ba, har sai sun cire rigunan kammala karatun jami’a da hidimar kasa.
Nazarin wadannan bayanai ya sa ni cikin tunani na kwanaki. Ina son in binciki me ya sa take so mu tattauna wannan batu, shin da gaske akwai ta a farfajiyar facebook ko dai dodorido irin na basaja ne, amma wata zuciya ta ce da ni, ai wannan bai da muhimmanci, abin da ke da muhimmanci shi ne ‘gaskiyar’ irin sakon da ta turo. Shin abin da ta nemi bayani yana da muhimmancin da ya kamata mu tattauna ko kuwa? Wannan shi ya ja hankalina, na koma ga batun, ba ga wadda ta turo da batun ba.
Abu na farko da na aika mata da shi, shi ne, wa ya tsara cewa matan Hausawa sai sun bi wadannan matakai na sa rigunan a lokacin rayuwarsu, kuma me tsarin ke nuni? Shin in matan Hausawa ba su bi wannan tsarin ba, tasu ta gansu ne ko kuwa wani abu ne zai faru gare su, na musamman? Shin iyakar rigunan ke nan da matan Hausawa ya kamata su sanya a tsawon rayuwa ko kuwa akwai wasu rigunan na daban da ba ta bayyana ba? Ina batun rigunan shugabanci da aikin yi don ciyar da kai da iyali da raya al’umma, su matan Hausawa ba sa bukatar sa irin wadannan riguna?
Amsar da ta ba ni, ba ta taimaka wajen warware duguzum da rayuwata ta kasance ciki ba. Cewa ta yi, ni dai na yi nawa nazari na kuma fahimci cewa yawancin rigunan da matan Hausawa ke amfani da su a halin yanzu, in har sun samu damar, yagaggu ne, domin wai sun dade suna gurza su ta yadda dauda ta yi musu yawa, har ba a gane su. Ta ba ni misali da matan Hausawan da suka sa rigunan firamare aka yi musu aure bayan nan, suka shiga damawa da rigunan aure a jikinsu. Ba su kara sa wasu rigunan ba, shekara da shekaru ko dai ta Allah ta kasance, mijin ya rasu ko kuma bayan ya karo wadansu matan, su rabu da shi, su shiga rayuwar zawarci, cikin kunci da damuwa. Ta ce wadannan matan ba su da halin komawa ga rigunan shiga sakandare, ba hobbasa domin zuwa jami’a, balle a yi maganar hidima wa kasa. Ta karasa da cewa haka za ka gan su ba abin da suke tinkaho da shi face rigunan da suka rika sawa tun ranar da suka fara haihuwa; wadansu riguna 6, wadansu 7, wadansu har goma da doriya! Ta ce a cikin tasu arangamar da rigunan shiga firamare da na haihuwa sun dora nasu ’ya’yan mata bisa irin wannan tafarki, su kuma sun sa rigunan firamare da sakandare, shi ke nan suka shiga sa rigunan aure da haihuwa…jiya, i yau!
Duk da cewa batutuwan da muka tattauna da wannan mai turo sako cikin jirwaye da wuji-wuji ne, na fahimci inda ta sa gaba, ta kuma gane inda na nufa da nawa tambayoyin da hasashen. Magana daya ce, jazaman matan Hausawa na cikin ‘tasku!’ Rigunan da suke sanye da su ko dai sun yi musu ‘kadan’ ko sun ‘yayyage’ ko kuma sun mayar da hankali ga wasu rigunan, sun yi watsi da wasu, wanda ya kara jefa su cikin layin ‘bace hanya’ ko lalube ‘cikin duhu!’ Ina mafita? Me za a iya yi?
Za mu ci gaba