Nasiha zuwa ga maza (10)

Saboda haka idan har kika ce kuna neman wadanda za ku taimakawa ne daga cikin masu rauni a cikinmu, sai in ce masu raunin ai ba mu ne ba, sai dai mazanmu, domin kuwa mu ne ginshikan da ke rike da gidajen da muke zaune, kila ma dukkan al’ummar da ke tattare da mu. Su […]

Nasiha zuwa ga maza (10)

Saboda haka idan har kika ce kuna neman wadanda za ku taimakawa ne daga cikin masu rauni a cikinmu, sai in ce masu raunin ai ba mu ne ba, sai dai mazanmu, domin kuwa mu ne ginshikan da ke rike da gidajen da muke zaune, kila ma dukkan al’ummar da ke tattare da mu. Su wa ke neman taimako ke nan?

Da na kawo nan, na numfasa, sannan na shiga cikin dogon tunani, ina kokarin kara fahimtar inda za mu kare da wannan mata a karshen wannan tattaunawa. Na shake da wannan tunani ne domin kuwa batutuwan sun wuce rigunan matan Hausawa kurum, sun koma ga rigunan maza da na hukuma da na addini da na al’ada da kuma zamantakewa, wanda a nawa tunanin sun wuce tunanin mutum daya ko samar da mafita daga mutum daya ko biyu. Na juya wasikar da wannan mata ta turo min, wadda ita kuma an aiko mata ita ce daga ’yan uwanta mata, daga cikin kungiyoyinsu na mata a karkara. Na bude shafi na gaba, inda wadancan mata ke cewa, ‘su wa ke neman taimako ke nan?’ Kafin in karanta wasikar a cikin raina na san inda suka nufa, amma sai suka bayar da ni. Sun ci gaba da cewa:

‘Mu kanmu ba za mu iya cewa ga wadanda ke neman taimako ba a cikin irin wannan badakala, sai dai muna da hasken da za mu iya badawa. Ki sani, dukkan misalan da muka ba ki game da sauran ’yan uwanmu mata, su ne ke fadi-tashin, amma ’yan uwansu maza, na karya musu kafafu ko kuma dora musu matsalolin da suke hana su sukuni da ci gaba. Mazan ne matsalarmu, ba kuma don suna so ba, yawanci, don su ma ba su da yadda za su yi, matsalolin sun yi musu wanka da sabulu ne, su ma. Amma inda matsalar ta fi fitowa fili ita ce, mazan Hausawan da ke yin yadda suka so domin su dakile mata, su hana mata motsawa, balle su kai ga shiga cikin rigunan da suka dace da su, DA GANGAN!

Ki sani cewa akwai daga cikin ’yan wannan kungiyar nan tamu da ba su iya zuwa taro irin namu, ba su da damar da za su tofa albakacin bakinsu game da halin da suke ko ’ya’yansu ke ciki, saboda matsuwa da damuwa da kunci. Irin wadannan ’yan uwa namu, suna cikin damuwa da kunci fiye da mu, saboda a kullum cewa suke, ai mu muna da damar da za mu yi sana’ar da za mu ciyar da kanmu da iyali, har da mazan namu, amma su ba su samu irin wannan dama ba, domin aure ya nemi ya gagare su. Kullum muka leka gidajensu domin tattauna matsalolin, batu daya ne kullum ke tashe, yaya za su yi da rayuwarsu, inda aure yake nema ya zama musu alakakai, saboda neman na rufin asirin kai? Za ki ce me suke nufi da wannan batu, bari in ba ki misali, kila ma samu haske daga nan.

Akwai Maijidda, yarinya ce ’yar shekara 28 da haihuwa, an yi mata aure tana kammala karatun firamare, mijinta na farko shi ne rayuwarta, amma bai iya biya mata bukatar yau da kullum. dinkin Sallah ko zanen sawa domin kwalliya ko kayan shafa ko makamantan haka, sai dai ta gani a gidajen wadansu, ba ta da ikon ta roka, don ita ma ta dace da zamani. Da ta nuna masa cewa ai ta iya sana’ar kitso, ya ba ta dama ta rika yin sana’ar kitso a cikin gida, sai da ya jinjina kafin ya amince mata. Daga nan kuwa ta samu hanyar kwabon kamawa. Kan su yi shekara da yake hannunta mai kyau ne, ta fara samun na kanta. Ta fara canja zane. Ta fara kyautata wa iyayenta, ta fara sheki daga kayan kwalliya, ta kuma fara kumari. Wannan shi ne matsalarta, mijin nata ya nemi ta daina sana’ar in ba za ta rika taimakawa wajen ciyar da gidan ba, daga sana’ar kitson. Ta amince ta fara agazawa, garin tuwo da kayan miya, wata sa’a ma har da kashin miya. Duk da haka, wannan bai ishe shi ba. Ya ce sai ta koma ita ce ‘mijin,’ komai sai ta yi a gidan, shi bai kara sa ko kwabonsa ko ta bar sana’ar. Da ta ki ba da kai bori ya hau ne ya sake ta. Cikin murna ta amshi takardarta, ta koma gidan iyayenta, duka da ’ya’yan nasu da suka haifa.

Wallahi da yake sana’ar ta karbe ta, sai ta fara fita gidaje, kan ka ce kwabo labarinta ya kai ga matan manya, ta fara samun na rufin asiri. Wani namijin ya fito neman aurenta, ta amince, amma da sharadin ya bar ta ta ci gaba da sana’arta, ya amince. Ta tare, ta ci gaba da sana’arta. Duk Asabar da Lahadi tana gidan wadanda suka tada kai, tana yi wa matansu da ’ya’ya kitso, nan ta koma kamar kamfani, a cikin wata guda, tana samun kudin da matsakaicin ma’aikacin gwamnati, ke samu, daga gida! Harka ta bude musu ita da miji da ’ya’yanta. Me ya faru? Iyayen mijin suka sa ya sake ta, wai ta koma ‘miji,’ shi ya zama talasuru. Haka ta koma gida da saki uku. Yanzu haka tana gidanta na kashin danta, ita da ’ya’yanta. Kamfanin kitsonta kuma ya bunkasa. Idan mun kawo mata maganar aure, sai ta ce ba yanzu ba. Nan kuma laifin na wane ne?

Ba wannan ba ma, akwai Gambo Ta-Banki, haka muke kiranta, domin tun da muka tashi a banki muka santa. Ita ma aurenta biyar, ana sako ta saboda aikin banki, ba kuma don wani abu ba, sai don tana samu. Ita ba ta damu da jiran kyauta daga mijin ba, wanda sai a dade bai yi abin da ya dace ba, gare ta ko ’ya’yanta ko kuma iyayenta da sauran ’yan uwa. A kullum aurenta ya mutu, daga wannan matsala yake tasowa, ba ta taba damuwa ba, domin ta san cewa ba aikin Shaidan take yi ba, amma surutai dai ba su taba karewa ba. Ko dai a ce karuwanci take yi ko kuma a ce ita ce miji domin ba ta dawo wa gida in ta fita karfe 7 na safe sai 7 na dare ko fiye. Ko kuma masu cewa ai ta shanye shi, bai iya komai. Ita ke biyan kudin makarantar yara da hayar gidan da suke ciki kai wata sa’a ma shinkafa da tuwon da za a ci a gida, ita ce mai bayar da kudin, daga aikinta na banki.

Haka Gambo Ta-Banki ta rayu a gidajen mazan Hausawa, har biyar, amma ba ta saki aikinta ba, kamar yadda aka so. Mun tabbata da ta saki aikin nata da yanzu ta fi beran masallaci talauci. Da yanzu ta fi kowa kwarmato da shiga kuncin rayuwa. Banki ta ‘aura’ kuma shi ne mafita a wajen ta da ’ya’yanta daga mazajen Hausawa da take tare da su. Ita ma laifinta ne, ita ke neman taimako!

Za mu ci gaba

Davido zai bai wa marayu tallafin N300m a Najeriya

Ba mu yanke hukunci kan ƙudirin harajin Tinubu ba — Abbas

Masu garkuwa da mutane na neman N10m kan manoma 6 a Taraba

Hotunan Gobarar Kasuwar Laranto da ke Jos