Nasiha zuwa ga maza (2)
Duk da cewa batutuwan da muka tattauna da wannan mata mai turo sako cikin jirwaye da wuji-wuji… ne, na fahimci inda ta sa gaba, ta kuma gane inda na nufa da nawa tambayoyin da hasashen. Magana daya ce, jazaman matan Hausawa na cikin ‘tasku,’ rigunan da suke sanye da su ko dai sun yi musu […]
Duk da cewa batutuwan da muka tattauna da wannan mata mai turo sako cikin jirwaye da wuji-wuji… ne, na fahimci inda ta sa gaba, ta kuma gane inda na nufa da nawa tambayoyin da hasashen. Magana daya ce, jazaman matan Hausawa na cikin ‘tasku,’ rigunan da suke sanye da su ko dai sun yi musu ‘kadan’ ko sun ‘yayyage’ ko kuma sun mayar da hankali ga wasu rigunan, sun yi watsi da nasu, wanda ya kara jefa su cikin layin ‘bace hanya’ ko lalube ‘cikin duhu!’ Ina mafita? Me za a iya yi?
Ni dai ina da yakini cewa in na tambaye ta me za a iya yi domin kawo sauki ga irin wadannan mata da suke sanya riguna baibai ko suke fama da tsofaffi ko yagaggun riguna, bisa ga dukkan alamu ba amsar kwarai zan samu ba, domin kuwa ta riga ta yi matsaya kan batun. Sakon da ta turo na gaba ya kara tabbatar min da haka, ta ce da ni, in tsaida hankali waje daya in yi nazarin rayuwar matan Hausawa da ke zaune a karkara da kuma biranenmu, daga nan sai in yanke hukunci da kaina. Ta ce, matan Hausawa nawa ake damawa da su a cikin harkokin yau da kullum na ciyar da kasa gaba ko kuma al’amuran kula da iyali, wanda shi suke ta fama da shi, shekara da shekaru? Ta ce, wace gudunmawa matan Hausawa ke bayarwa wajen ciyar da tattalin arzikin kasa da siyasa gaba? Ta kara da cewa ina matan Hausawan suke a lamuran gudanar da kasa da mulki da zamantakewa? Ta ce, idan ta ci gaba da lissafo abubuwan da suke kunshe cikin ranta game da matan Hausawa ba zan samu damar da zan bayyana mata gaskiyar lamarin ba, domin abin da yawa, mutuwa ta leka kasuwa.
Daga wannan sakon nata ne na gane ainihin dajin da ta fito daga ciki da kuma birnin da take zaune a ciki. Amma domin kada in bayar da kai bori ya hau, sai na buge da yi mata wata tambayar, na ce da ita, ni ko sai na ga cewa ai kowa ya san inda matan Hausawa suke zaune da irin gudunmawar da suke bayarwa ga ci gaban kasa. Na kara da cewa su wane ne masu sana’ar kitso da surfe da sayar da man gyada da kuli-kuli da soya kosai da dan wake da waina da kasa wa ’ya’yansu maza da mata talla iri-iri domin su fita nema in ba matan Hausawa ba? Wannan gudunmawa da suke bayarwa ai gwamnati ba ta kididdige ba ne da ta fahimci cewa irin wadannan sana’o’i matan Hausawa na taimaka wa tattalin arzikin kasar nan, don dai kawai ba a mayar da hankali kansu ba ne.
Bayan tura mata wannan sako ta dade ba ta sake waigo ni ba, na dauka cewa ta hakura ke nan, ko ta samu makama daga tambayoyin da take ta faman yi. Bayan wajen kwana biyu sai ga sakonta can da tsakar dare….lokacin ina shirin kwantawa, amma da yake na shaku da abubuwan da take turowa, nan take na bude akwatin sakona domin in ga abin da take cewa wannan karon. Dogon zance ne ta turo, saboda haka na gyara kwanciya na shiga karantawa.
Ta ce da ni, ‘Allah Ya gafarta Malam, da alama ka dauka cewa tambayoyin da nake yi maka game da matan Hausawa kamar da gayya ko wasa nake yi maka su. Haka kuma amsoshin da kake ba ni sai na ga kamar ba da gaske kake yi ba, ka maida ni tamkar wadda ba ta san abin da take yi ba. Na san ka sani, daga cikin kididdigar matan Najeriya, matan Hausawa ke da kaso mafi yawa. Na san kuma ka sani yawancin wadannan matan da muke magana kansu, rigunan da suka fi tu’ammali da su a rayuwa su ne na firamare ko sakandare, sai ko rigunan aure. Na san ka sani daga cikin kashi 100 na matan Hausawa kusan kashi mafi tsoka ba su ma damu da sa wata riga da ta wuce ta aure ba, daga nan kuma sai rigunan haihuwa. Na san ka sani Malam wadannan sana’o’i da wasu irinsu da dama da ka lissafa ba sa fitar da A’i daga sana’ar rogo idan gaskiya za mu fada. Idan kuwa tallace-tallace da matan Hausawa ke dora wa ’ya’yansu hanya ce ta ciyar da tattalin arzikin kasa gaba, da kuwa ba wani sashe da zai ci gaba, face sashen da matan Hausawan ke zaune ciki. Amma me muke gani yanzu, babu inda talauci ya yi kaka-gida irin yawancin gidajen matan Hausawa, musamman a karkara. Ba sai na sake nanatawa ba Malam, ka sani, kamar yadda na sani rayuwar matan Hausawan da ke zaune a karkara ba aba ce da za a daga domin yabawa ba, rayuwa ce ta talauci da kunci da damuwa da kuma uwa-uba rashin wata riga da za su sa da za ta yi musu tasiri a rayuwa. Wadansu sun sa rigar firamare, wadansu ta sakandare, wadansu kuma rigar aure. Wannan tsarin kuma ni a tawa fahimta ya yi hannun riga da yadda rayuwar wannan karnin ta tanada ga mata. Sanya rigar aure ba laifi ba ne, sai dai kuma kin sanya rigunan karatu kowadanne iri ne ga mata, musamman na Hausawa, ni a tawa fahimtar, matsala ce.’
Karanta wannan dogon sharhi nata ya sa ni komawa cikin sabon tunani. Na dade ban ce da ita komai ba, ban kuma koma kan batun ba, sai da ta sake aiko da wani sakon, ta ce ‘Malam ko na fadi abin da ba shi ne ba? Ko tawa gaskiyar ita ma daci gare ta? Ko kuwa dai ni ce ban gane dawan garin ba? Ko ni ce ke ganin cewa rigunan aure da matan Hausawa ke jajiba, suna sanyawa ba tare da kula ba na iya zama matsala?’
Maimakon in bayar da amsa kai-tsaye sai na yi abin nan da aka sanmu da shi, amsa tambaya da wata tambaya, na ce, ‘na ga dukkan zancenki, na kuma fahimce ki, amsar ce ke da kamar wuya. Shin ba ki ji Hausawa na cewa aure bautar Ubangiji ba? Shin ba ki ji Hausawa na cewa aure rabin addini ba ne? Shin ba ki ji Hausawa na cewa aure ibada ba ne? Shin ba ki ganin cewa matan Hausawa sun bi tafarkin da suke ganin shi ne na tsira da suke sanya wa matansu rigunan aure da zarar sun gama firamre ko sakandare, ko ma su ki sa musu kowace irin riga in ba ta auren ba, sai kuma ta haihuwa? Shin ba ki son matan Hausawa su samu rabauta daga bautar aure?’
Za mu ci gaba