Nasiha zuwa ga maza (3)

Shin ba ki ji Hausawa na cewa aure bautar Ubangiji ba? Shin ba ki ji Hausawa na cewa aure rabin addini ba ne? Shin ba ki ji Hausawa na cewa aure ibada ba ne? Shin ba ki ganin cewa Hausawa sun bi tafarkin da suke ganin shi ne na tsira da suke sanya wa matansu […]

Nasiha zuwa ga maza (3)
Nasiha zuwa ga maza (3)

Shin ba ki ji Hausawa na cewa aure bautar Ubangiji ba? Shin ba ki ji Hausawa na cewa aure rabin addini ba ne? Shin ba ki ji Hausawa na cewa aure ibada ba ne? Shin ba ki ganin cewa Hausawa sun bi tafarkin da suke ganin shi ne na tsira da suke sanya wa matansu rigunan aure da zarar sun gama firamre ko sakandare, ko ma su ki sa musu kowace irin riga in ba ta auren ba, sai kuma ta haihuwa? Shin ba ki son matan Hausawa su samu rabauta daga bautar aure?’

Na dauka daga nan mun rabu, domin kuwa ba wanda zai karyata cewa aure ba bauta ba ne ko cikon addini, sai dai kuma in da wata manufar a nata tunanin. Bayan kwana daya sai ta aiko da amsarta, wadda kuma ko alama ba ta ba ni mamaki ba. Da farko na dauka mawakiya ce ta koma, domin da baitoci ta bude zancen nata, kamar haka:

‘Iliminki babu aure shifci na,

Iliminki babu aure sharri na,

Shaidan ka tunguza ki cikin barna,

Ke ko kina fadin injoyin na.’

Malam, wannan baitin wakar sun dade suna yi min rawa a cikin raina, wani ne da nake so, yake kuma sona, ya aiko min da wakar da wani ya rubuta kan mata, mai taken ‘Da Ke Nake!” a lokacin da muka fara karatun jami’a. Shi a nasa tunanin sai na bar karatun jami’a mu yi aure domin auren ya fi karatun da na dage mawa. Ban saurare shi ba, domin kuwa aure da neman ilimi dukkansu addini ya aminta da su. Kowane da irin matsayin da aka ajiye shi a kai. Ban koma ta kansa ba, na ci gaba da karatuna, na kuma gama, na yi hidimar kasa, na yi aure, kuma ina da ’ya’ya hudu, ina kuma aikina na akanta a banki a halin yanzu. Har yau kuma ina nan kan bakana, ilimi ba ya hana aure, haka kuma aure ba ya hana ilimi.

Bari in dawo ga tambayoyinka Malam, Hausawa da ke cewa aure bautar Ubangiji ne, haka ne, yin sa bautar ce, don Allah Ya ce a yi. Su kuma  Hausawa da ke cewa aure rabin addini ne, ba su kallli batun da kyau ba ne, ai ba daga yin auren ake samun garabasar ba, sai an yi abubuwan da addini ya tanada domin cikar auren. Hausawa da ke cewa aure ibada ne, tamkar masu cewa bauta ne, dukkan abin da aka dora wa taliki, in har ya yi aikin kamar yadda aka umarta, za a sakanka. Da kuma ka ce shin ba ni ganin cewa Hausawa sun bi tafarkin da suke ganin shi ne na tsira da suke sanya wa matansu rigunan aure da zarar sun gama firamre ko sakandare, ko ma su ki sa musu kowace irin riga in ba ta auren ba, sai kuma ta haihuwa? Shin ba ni son matan Hausawa su samu rabauta daga bautar aure ne? Amsa daya zan bayar, ina so! Amma shin wace irin bautar matan Hausawa ke yi a halin da muke ciki?

Ka sani Malam, idan nazari za a yi na bin diddigi, yawancin matan Hausawa ‘aure’ kurum suke yi ba ‘bautar aure’ ba. Yawancin matan Hausawa da ke faman sanya rigunan aure,  rigunan kwalliya ne kawai. Su kuwa masu faman sanya rigunan haihuwa da zarar sun sha kwalliyar aure, sun dauka kamar itacen kuka ne da ’ya’yanta, an rika kakkaba ke nan, har sai sun kare, komai wahalar ruwan sama ko rana ko jifa da ake yi wa uwar. Wannan batu ne da ke a fili a cikin gidajen matan karkara da garuruwa da birane a kasar Hausa. Ina bautar ko ibadar take ga irin wannan rayuwar aure? Wannan shi ne abin tambaya a kullum.

Shin zaman auren da ba ilimi, kowane iri ga ’ya mace, shi ne bautar? Zaman auren da ’ya mace ke faman kai-kawo ta ciyar da kanta da iyali cikin kunci da damuwa da rashin walwala shi ne ibadar? Shin zaman auren da a kullum ana cikin zullumin yaya za a kare da rayuwar wannan mata da ke haihuwa ba ji ba gani, cikin rashin koshin lafiya da taraddadin me zai biyo bayan haihuwar shi ne bautar? Shin rayuwar auren da samar da ’ya’ya maza da mata da yawanci ba a iya kula da su, sai dai a tura su garuruwa ko birane domin bara da aikin hannu, ba a san halin da suke ciki ba, shi ne ibadar? Shin rayuwar auren da ake sanye da rigunan aure, a haifi wadansu ’ya’ya mata da za su kasance a matsayin kamfanin talla, su yi aure su ma su kafa nasu kamfanin talla ko na almajirai shi ne bautar ta aure?’

Ba ta jira na amsa mata tambayoyinta ba, sai ta ci gaba da bayaninta. ‘Abubuwa ne da yawa Malam da suke bukatar a tattauna a kuma yi matsaya ba wai a rika jefa kalamai na ba gaira, ba dalili ba da kila ba za su kai mu ko’ina ba. Ni na yi auren, Malam, na kuma san irin halin da nake ciki. Wadansu daga cikin ’yan uwana sun yi auren, na kuma san halin da suke ciki. Ba auren ne matsala ba, Malam, zaman auren ne a wannan zamani abin tunani. Idan har rigunan da yawancin matan Hausawa ke sa wa na shiga firamare ne da sakandare daga nan sai rigunan aure da na haihuwa, sa’annan ibadar auren na cikin wuji-wuji, ba ka ganin ya dace a samu wasu rigunan da za su kawo sauki ga rayuwar irin wadannan mata? Ba ka jin cewa a sanya wa matan Hausawa rigunan kamar yadda na tsaro za su iya kawo mafita? Misali, ina laifin matan Hausawa su hada riguna biyu, kwarara ko da ba su sanya kowace rigar da na zayyana ba? Mu yi tsari da zai sanya ’yan matan Hausawa su kasance da rigunan sakandare har su dire. Daga nan sai su sanya rigunan auren, shi ma sai a tsara ta yadda ko suna gidajen mazansu za su iya ci gaba da sanya rigunan karo ilimi ko aiki ko sana’a ko wani abu makamancin haka, ba wai a bar su kara zube ba.

Na tabbata in aka yi haka, to kila abin da ya faru ga irin su Maryam da Halima da Indo, A’i da Hajara da Kande da Lami da wadansu da dama da bai same su ba a tsawon rayuwa. Aure bautar Ubangiji ne ya kamata ya zama Malam, ba BAUTA ba!

Za mu ci gaba