Nasiha Zuwa Ga Maza (7)
“Don Allah Malam ina laifin Maryam a nan? Ina mijin nata yanzu? Yana can zaune da wadansu sababbin mata da ya aura bayan ya kori Maryam, duniya ta koma masa sabuwa! Nawa ne irin Maryam ke raye yanzu ko makamantan irinta da ba mu damu da halin da suke ciki ba?” A daidai lokacin da […]
“Don Allah Malam ina laifin Maryam a nan? Ina mijin nata yanzu? Yana can zaune da wadansu sababbin mata da ya aura bayan ya kori Maryam, duniya ta koma masa sabuwa! Nawa ne irin Maryam ke raye yanzu ko makamantan irinta da ba mu damu da halin da suke ciki ba?”
A daidai lokacin da na zo wannan gaba, sai na kara fahimtar inda wannan mata ta nufa, amma da yake abin da yawa, wai mutuwa ta shiga kasuwa, sai na ci gaba da yin bakam, domin kada in ga zare, balle na yi tsinkau. Da yake jawabin nata da dan tsawo sai na koma gonar da na baro, na ci gaba da yin noman karatu.
Ta ce da ni “Malam, ina yin wadannan tambayoyi ba wai a gare ka ba ne, gare mu ne baki daya da kuma hukuma da wadanda al’amuran kula da gyarawa ke hannunsu, su ji, su gani, kila a samu mafita, amma halin da irin su Maryam ke ciki kamar yadda na kyallaro, bai ma kai irin halin da ’yan uwansu, irin su Halima da Indo da A’i da Hajara da Kande da Lami, ke ciki ba, ni a nawa tunanin.
Ita dai Halima ba kamar Maryam ba, Allah Ya sa ba ta wadatu da rigunan nan da na lissafo ba da ya kamata matan Hausawa su rika sanyawa ba, domin rigarta iyakarta gwiwar firamare, ta shiga mu’amala da rigar aure da ta haihuwa zuwa wata haihuwa, zuwa wata haihuwar. Ajinmu guda da Halima Malam, amma a daidai lokacin da na dawo sanye da sabuwar riga daga hidimar kasa, Halima ’ya’yanta shida da guda biyar ta leko domin taya ni murnar kammala karatun jami’a da hidimar kasa. Da na tambaye ta ina iyayen wadannan yara da take ta godon yawo da su, sai ta ce da ni, ke dai bari, abin sai a hankali. Wallahi Malam, in ka ga halin da Halima take ciki a wannan lokaci, kai ka san timbir take, rigar firamare ba ta rufe ta da komi ba. Tun haihuwar Halima ta farko nake ta kokarin in jawo hankalinta da na mijinta in na je cin tara gidanta da su bar ta ta motsa zuwa gaba, amma abin ya faskara, ina wucewa gaba da sanya sababbin riguna, Halima na kara gaba da sanya rigunan jego, ta yadda yanzu ta kasance matar maza, aurenta hudu, saki, hudu, kai ka ce uwar makera ce da ta sha bugu.
A koyaushe muka hadu da Halima maganar ke nan daya, shin ko ta baro shiri tun rani? In ta yi min wannan tambaya sai in rasa amsar da zan ba ta, domin kuwa ni a lokacin ko rigar aure ban saka ba tukuna. Amma a cikin raina, na san ba a yi mata daidai ba, ba a kuma kyauta mata da irinta da dama ba a cikin al’ummarmu, amma ban da bakin magana.
A lokacin da na samu damar sanya rigar aure, na kuma sanyawa wa nawa ’ya’yan rigunan suna, na sanya rigar aikin banki, ina zaune a Legas da maigidana, duk lokacin da muka zo gida, sai Halima ta leko mu gaisa, ba kuma komai tare da ita sai takaici da damuwa da neman yin da-na-sanin da ni a tawa fahimta ba tata ba ce. A shekarar da muka yi haduwar karshe, Halima ta yi aurenta na bakwai, kuma tuni mijin ya sake ta, kamar yadda take gaya min, ‘wai ba zai iya kula da matar da ke kama da guzumar da ta haihu ba, uwa kwance, ’ya’ya kwance.’ Saboda ganin ya aure ta da ’ya’ya biye da ita rankyar, ga shi, shi ma ba wani karfi gare shi ba, balle ya ciyar da tasa tawagar, ya kuma hada da nata. Wannan ya kawo rabuwar auren, ta sake komawa gidan wanta, suka shiga gumurzu da matansa da nasa ’ya’yan. Kullum muka tsaya muna tattauna irin matsalolin da Halima ke ciki, sai in kara tabbatar da cewa sanya rigunan kammmala karatu ko na aikin yi ko wata kwakkwarar sana’ar yi ga mace ya zama jazaman, musamman a irin halin da muke ciki. Amma in na tuna ba abin da zan iya yi kan irin wannan lamari sai in ji kunci ya tokare ni a cikin ciki har zuwa ga makokona.
Na sha tufkawa a cikin raina ina warwarewa, kan yadda zan yi da halin da Halima ke ciki da irin yadda zan iya taimakawa ga kawo sauki ga rayuwarta, amma sai na fahimci cewa ita tata ta kare, domin kuwa ta auri zawarci, ya kuma yi mata adon nunawa. A halin yanzu ita ce shugabar zawarawar karamar hukumar da muka fito. Ita ce kullum kan gaba wajen bin ofisoshin gwamnati da hukumomi domin samo tallafi ga zawarawan da ke kimshe a cikin gidajen mazan Hausawa da kila ba a san adadinsu ba. Ita da ’yan kungiyar tata, ba su san hanyoyin cin yau ba, bare na gobe, gare su, balle kuma tarin ’ya’yan da ke makale da su a rayuwa, tunda yawancin mazan Hausawa ba sa daukar nauyin ’ya’yan da suka saki iyayensu mata, bare su samu wata mafita.
A halin da ake ciki, Halima na can na ta fafutikar neman na abinci da kula da tulin ’ya’yanta da iyayensu maza suka bar mata, tana kuma addu’ar Allah Ya kawo mata wani namijin da za ta aura ko ta samu inda za ta rage wasu daga cikin matsalolin rayuwa. Abin da kurum ke sanyaya mini zuciya shi ne na dauko ’yarta ’Yar Lele, mai shekara takwas da haihuwa na sa mata rigar Islamiyya da ta firamare, na kuma sha alwashin sai ta sanya rigar sakandare da ta jami’a da ta hidimar kasa kafin ta shiga gidan Bahaushe a matsayin matar aure, in na samu yadda nake so, sai ta sa rigar aikin banki ko malanta, ita ma. Na sha alwashin sai ’Yar Lele, ta share wa Halima hawayen da mazan Hausawa ke sa kullum suna zuba a kumatunta a duk rana ta Allah, ba tare da yarda da amincinta ba.”
Da ta kawo nan sai na ga ta rubuta…hmmmmmmmmmmmmmmmm! Ba ta ci gaba da zancenta ba, nan na gane ajiyar zuciya ce ke tattare da ita. Ban ba ta wani bahasi ba a wannan lokaci, saboda ban san ta inda zan kamo habar zanen ba. Bayan kamar kwana biyu da wannan zance, ran nan sai na ga sakonta tana mai neman afuwa, ta ce, “Na san Malam ya ji shiru daga gare ni, balaguro na yi na aikin ofis, ban samu sukunin lekowa ba, amma insha Allah zuwa gobe zan turo maka wata wasikar da na samu daga Indo A’i da kawarta Hajara, ka ji su kuma taskun da suka shiga daga hannun mazan Hausawa da kuma illar rashin samun sanya wadancan tufafi da na yi maka bayani tun a farkon gamuwa.
Za mu ci gaba