Nasihar Ramadan ga mata iyayen giji

Uwar-gida kada ki takura mijinki wajen yin abin da ya fi karfinsa a watan azumi

Nasihar Ramadan ga mata iyayen giji

Yana da kyau ko wace mace ta fahimci yanayin da ake ciki na tsadar rayuwa, da kuma karancin samuwar kudi a hannun jama’a a yanzu, don haka ya zame mana wajibi mu saukaka bukatu da kuma burukanmu musamman a wajen abubuwan da za mu ci idan an yi buda-baki.

Ki sani ’yar uwa, watan azumi wata ne na ibada, wata ne na salama, wata ne mai dumbin darajoji, wanda ake son mu mayar da hankali wajen neman yafiya, albarka, dacewa, da kuma rahama daga mahaliccinmu, domin samun ribatuwa da samun lada kamar yadda Allah ya yi alkawarin bai wa mai azumi.

Kada ki kwallafawa ranki ke sai kin dafa abin da ki ka tabbatar ya fi karfin mijinki saboda kina azumi.

Kazaila kada ki matsawa mijinki sai ya yi abin da ki ka san ba shida halin yi, ko kuma sai kin kure kokarinsa saboda kuna azumi.

Ya kamata ki nutsu ki san me ya dace da ku, ki yi kokarin sarrafa duk abin da Allah ya yassare muku cikin sauki da hikima tare da kwarewa a matsayinki na mace, kar ki dinga kirkiro abin da ya fi karfinki ko kuma ki dinga ganin ire-iren girki ki dage kema sai kin yi irinsa.

Yana da kyau kada ki mayar da watan Ramadan watan cin dadi, idan kina da shi ki yi idan babu kiyi hakuri duba da yanayin da aka tsinci kai.

Kafin azumi, ta yiwu shinkafa ki ke dafawa, yanzu azumi ya zo sai ki ce dole ne ki dafa kwai, nama da kaza, alhalin kin san mijinki arzikin shinkafar ne da shi.

Da yawan abin da za ki ga wasu matan na sakawa a kafafen sada zumuntarsu, ba lallai ne su kasance gaskiya bane, wasu na yi ne don nuna isa ko karya da sauransu.

Don haka ’yar uwa ki dage da addu’a , ki nisanci buri da kwadayi domin hakan na iya kai ki ga halaka ba tare da kin farga ba.

Idan kunne ya ji, gangar jiki ta tsira.

Masu garkuwa da mutane na neman N10m kan manoma 6 a Taraba

Hotunan Gobarar Kasuwar Laranto da ke Jos

Kasuwar Laranto da ke Jos ta yi gobara

Ɗan shekara 60 ya rasu bayan faɗawa a rijiya a Kano