Nasihohi zuwa ga masu azumi
21. Ka yi azumin RanarArfa, wato ranartara ga watan Zul-Hajji, domin wanda ya yi shi ana gafarta masa zunubin shekara biyu – shekarar da ta wuce da shekara mai zuwa. 22. Ka yi azumin Ranar Ashura, wato goma ga watan Muharram tare da Azumin Tasu’a wato tara ga Muharram, watan daya a Musulunci, domin in […]
21. Ka yi azumin RanarArfa, wato ranartara ga watan Zul-Hajji, domin wanda ya yi shi ana gafarta masa zunubin shekara biyu – shekarar da ta wuce da shekara mai zuwa.
22. Ka yi azumin Ranar Ashura, wato goma ga watan Muharram tare da Azumin Tasu’a wato tara ga Muharram, watan daya a Musulunci, domin in mutum ya yi ana gafarta masa zunubin shekara daya.
23. Ka cigaba da imani da tsoron Allah da aiki na gari da nisantar duk wani mummunar aiki bayan
Ramadan kamar yadda ka yi a Ramadan, domin Ubangijin Ramadan shi ne Ubangijin kowane wata, kuma ka ci gaba da tsare dokokin Allah har mutuwarka, domin Allah Yace, “Ka bautawa Ubangijinka har mutuwa ta zo maka.”
24. Ka bayyana alamomin ibada, ka yi Sallah tare da jama’a, ka yi kuma Zakka a sarari har ma ka tafi aikin Hajji, bayan haka ka bayyana tubarka ta hanyar barin miyagun al’adu da bidi’o’i da nesantar camfe-camfe da kuma nesantar shirka babba ko karama domin wadannan abubuwa ne da suka saba,wa shari’a.
25. Ka yawaita salati da taslimi ga Annabi (SAW) da iyalansa da sahabbansa da mabiyansa baki daya.
A karshe, muna rokon Allah Ya sanya mu cikin wadanda suka yi azumin watan Ramadan da kuma nafiifilin Ramadan- bisa imani da Allah da kyautatawa, muna rokonSa Ya gafarta mana abin da muka aikata na laifuffukanmu da abin da muka jinkirtar. Allah Ka sanya mu cikin wadanda suka yi azumin watan Ramadanada kuma alherin daren LailatuI Kadar, kuma ka sanya mu cikin wadanda suka rabauta da gafararKa, ya Mai girma da Daukaka, ya Ubangiji Kai ne Mai rangwame kumaKana son rangwame Ka yi mana rangwame, ya Ubangiji!Ka amsa mana ayyukanmu, hakika Kai Mai ji ne Masani.Ya Rayayye, Tsayayye da kanSa, Ya Ma’abucin Daukaka da Girma.
Tsira da amincin Allah su tabbata ga Annabi (SAW) da mutanen gidansa da sahabansa da sauran muminai baki daya.
Imam (SP) Ahmad Adam Kutubi na Rundunar ’Yan sanda Najeriya,
Za a iya tuntubarsa ta: 08036095723