Shahararren ɗan kasuwa Nasiru Ahali ya rasu a Kano

Marigayin wanda yake shahararren masanin masana’antu ne ya rasu yana da shekara 108.

Shahararren ɗan kasuwa Nasiru Ahali ya rasu a Kano

Allah Ya yi wa Alhaji Nasiru Ahali, Shugaban Kamfanin Mainasara & Sons, rasuwa.

Marigayin wanda yake shahararren masanin masana’antu ne ya rasu yana da shekara 108.

A cewar majiyoyin na kusa da iyalan marigayin ɗan kasuwar ya rasu ne a wani asibiti da ke Kano a daren ranar Alhamis.

Ana girmama Ahali a matsayin ɗaya daga cikin jiga-jigan masanin asalin masana’antu a Kano. Ya yi ƙoƙari ya kafa tsarin kasuwanci na yau da kullun.

A tattaunawarsa da Daily Trust a shekarar 2018, marigayi Ahli ya bayyana cewa sana’arsa ta haɗa da buga littattafai, bugu takardu, masana’antar bulo, sana’ar fasa dutse, shigo da kaya, kwangilar gama-gari, bunƙasa kadarorin rukunin gidaje, ayyukan ƙarafa da sauransu.

A saƙon ta’aziyyar da ya aike wa iyalan marigayin ta hannun Babban Daraktan Yaɗa Labarai na Gidan Gwamnatin Kano, Malam Sanusi Bature Dawakin Tofa, Gwamnan Jihar Kano Abba Kabir Yusuf, ya bayyana rasuwar a matsayin babban rashi ba ga iyalansa kaɗai ba, har da jiha da ƙasa da sauran al’ummar Musulmi baki ɗaya.

Ya bayyana marigayin a matsayin ɗaya daga cikin waɗanda suka kafa masana’antu, inda ya ce shi ne ya tsara tattalin arzikin jihar tare da taka muhimmiyar rawa a tsakanin ƙananan masana’antu da manyan masana’antu a jihar.