Natasha Hadiza Akpoti: Jagorar gwagwarmaya da kasuwanci

Natasha Hadiza Akpoti ta yi abubuwa da dama don kyautata rayuwar al’umma

Natasha Hadiza Akpoti: Jagorar gwagwarmaya da kasuwanci

Natasha Hadiza Akpoti

Barista Natasha Hadiza Akpoti lauya ce, ’yar gwagwarmaya, ’yar kasuwa, kuma ’yar siyasa.

Tana kan gaba wajen fafutukar ganin an farfado da kamfanin tama da karafa na Ajaokuta, wato Ajaokuta Steel Rolling Mill.

A watan Janairun 2016 ta jagoranci wani gagarumin tattaki da nufin jawo hankalin gwamnati ga halin ni-’ya-sun da kamfanin yake ciki; sannan a watan Maris na 2019 ta gabatar da wata makala a gaban Majalisar Dokoki ta Kasa.

Wannan jawabi na Barista Natasha Hadiza Akpoti ya yi matukar tasiri a kan ’yan majalisar, har ya kai ga kafa wani asusu na Naira biliyan daya don farfado da kamfanin.

Kyautata rayuwar al’umma

Saboda burinta na ganin ta kyautata rayuwar al’ummarta, Tauraruwar tamu ta kafa wata gidauniya mai daukar nauyin karantu yara masu rangwamen gata.

Zuwa yanzu, yara fiye da 1,000 daga sassa daban-daban na Najeriya ne suka amfana da wannan tallafi.

Haka kuma ta taba sadaukar da rijiyoyin burtsatse hudu ga wadansu al’ummomi masu fama da karancin ruwa a Jihar Kogi.

Sannan a lokacin da ake tsaka da zaman kulle sakamakon annobar COVID-19, Natasha Hadiza Akpoti ta bayar da gudunmawar na’urar numfashi ga Babban Asibitin Gwamnatin Tarayya (wato Federal Medical Centre) da ke Lakwaja a jihar ta Kogi.

Ta kuma samar da wani shiri na karfafa gwiwar mata da matasa 5,000 a yankunan karkara da abin yi don raba su da talauci.

A baya-bayan nan kuma, a karshen shekarar da ta gabata, ta gyara wani sashe da ya lalace a kan babbar hanyar da ta hada jihohin Kogi da Edo, wadda kuma ita ce ta hada Arewaci da Kudancin Najeriya.

Kafin gyaran, hanyar ta yi kaurin suna wajen satar mutane don neman kudin fansa da sauran ayyukan bata-gari.

Lambobin yabo

Natasha Hadiza Akpoti ta samu lambobin yabo da dama, ciki har da wadda kungiyar Nigerian Project Support Group ta ba ta ta Fitilar Haskaka Najeriya a 2018, da kuma girmamawa a matsayin daya daga ciki matan Najeriya 50 da Suka Fi Kowa Zama Ababen Koyi – a sahu guda da tsohuwar Ministar Kudi Ngozi Okonjo-Iweala da tsohuwar Ministar Ilimi Oby Ezekwesili – a 2021.

Bugu da kari, a watan Yulin 2017, Karamar Hukumar Kwaryar Binin Abuja ta rada wa daya daga cikin titunan gundumar Kado sunan Tauraruwar tamu.