NATO ta la’anci harin ramuwar gayyar Iran a kan Isra’ila
Iran ta kai wa Isra’ila harin ramuwar gayya a daren ranar Asabar.
Ƙungiyar Tsaro ta NATO ta yi Allah-wadai da harin da Iran ta kai wa Isra’ila, tare da yin kira na ganin an kiyayi kai ire-iren hare-haren domin guje wa zubar da jini.
NATO ta soki harin da Iran ta kai cikin dare, inda ta ce tana sanya ido kan abubuwan da ke faruwa domin daukar matakan da suka dace.
- Ma’aikatan wutar lantarki sun nemi a janye ƙarin kuɗin wuta
- Allah Ya yi wa Yariman masarautar Zazzau rasuwa
Mai magana da yawun NATO, Farah Dakhlallah, ya ce yana da matuƙar muhimmanci a kiyaye domin rikicin na iya dagula lamura a Gabas ta Tsakiya wanda hakan na barazana ga zaman lafiyar duniya.
Sai dai Iran ta yi barazanar duk ƙasar da taɓa sararin samaniyarta wajen kai mata hari to za ta ɗanɗana kuɗarta.
Iran dai ta kai harin ne, a matsayin wani martani kan harin da Isra’ila ta kai wa ofishin Jakadancinta da ke birnin Damascus.