Na’urar tantance katin zabe maganin magudi ce -Hukumar zaben Ghana
A sakamakon cece-kucen da batun amfani da na’urar tantance masu jefa kuri’a a wurin zabe ya jawo, wakilin Aminiya da ke kasar Ghana ya tattauna da Darektan zabe na kasar Mista Anthony Amedzakey inda ya yi masa bayanin irin nasarori da matsalolin da hukumarsu ta samu a yayin da ta yi amfani da irin wannan […]

A sakamakon cece-kucen da batun amfani da na’urar tantance masu jefa kuri’a a wurin zabe ya jawo, wakilin Aminiya da ke kasar Ghana ya tattauna da Darektan zabe na kasar Mista Anthony Amedzakey inda ya yi masa bayanin irin nasarori da matsalolin da hukumarsu ta samu a yayin da ta yi amfani da irin wannan na’urar a yayin gudanar da zabenta na shekarar 2012. Ga yadda hirar ta kasance:
Aminiya: Yallabai ko za ka yi mani bayyani kan abin da ake cewa na’urar Biometric da ke tantace mutum?
Anthony: Na’urar Biometric wata na’uara ce wadda za ta iya ganewa ko sarrafa halitar mutum,misali yatsar hannu ko idanuwa da yanayin fuska.Wadanan siffofi da na ambata ana iya amfani da su a gane mutum, kasancewa kowane mahaluki da irin halittarsa. Alal misali, yatsata ta sha bamban da na wani, ko da kuwa dan uwan tagwaicinka ne na’urar Biometric za ta iya tantance ku ta gane bambanci ku. Don haka ake amfani da ita a wurin yin zabe yadda za a bai wa duk wadanda suka yi rajista dama su jefa kuri’a. A takaice dai, abin da ake cewa na’urar Biometric ke nan a wurin jefa kuri’a.
Aminiya: Nau’ukan na’urar Biometric nawa ake da su?
Anthony: Ban iya cewa ga adadin na’urar Biometric da ake da su, domin akwai wadda ake amfani da ita wurin yin fasgo (passport) da takardar zama dan kasa da ishorar kiwon lafiya da ishora, da dai sauransu. Kamar yadda na ce ne, ita na’urar Biometric akwai wadda ke daukar hoton yatsu da hannu da fuska da idanu da sauransu.
Aminiya: Ko za ka iya bayanin yadda ake amfani da na’urar ba tare da ta samu tangarda ba?
Anthony: Wannan ya dogora ne da yanayin da ake amfani da na’urar, sai kuma irin horon da aka ba masu amfani da ita. Idan an ba su cikaken horo kan yadda za su nakalci na’urar hakan zai taimaka na’urar ta yi aiki ba tare da tangarda ba.
Aminiya: A zaben shekara ta 2012 an ce an samu matsala game da batirin na’urar, yaya gaskiyar wannan maganar?
Anthony: Matsalar da muka samu ita ce, an umurci masu sarrafa na’urar su rika canza batirin bayan wadansu lokuta na amfani da ita, amma sai suka ki bin umurni, inda muka samu matsala ke nan. Misali, an ce bayan kowane sa’’o’i hudu su canza batirin sai suka ki.Wannan ya sa na’urar ta kasa cigaba da aiki. Amma da aka fahimci inda kuskuren yake aka gyara na’urorin sun yi aiki yadda ake so. Saboda bayar horo sosai yana da muhimmanci tare da bin umurni,sai kuma la’akari da yanayin da ake amfani da na’urar.
Aminiya: Yaya ake amfani da na’urar wurin tantance mai zabe?
Anthony: Alal misali, ana bukatar alamun yatsu wurin gane mutum,kamar yadda ake amfani da na gane fuska. Idan an zo jefa kuri’a kuma za a bukaci duk wanda ya zo ya dangwala yatsarsa a cikin na’urar yadda za ta gane ko yana da rajistar yin zabe ko a’a. Idan ya yi rajista na’urar za ta amsa, idan kuwa bai da rajista na’urar zab ta nuna cewa wannan mutum bai da rajista.
Aminiya: Shin za ka iya cewa an yi nasara wurin amfani da na’urar Biometric a zaben shekarar 2012 da aka yi a kasar Ghana?
Anthony: kwarai kuwa mun samu gagarumar nasara.
Aminiya: Mene ne hujjarka na cewa kun samu nasara?
Anthony: Hujjata ita ce, farkon lokaci ke nan da muka yi amfani da na’urar kuma ta taimaka mana wurin hana wadanda ba su da rajista jefa kuri’a. Haka kuma ta taimaka mana wurin hana jefa kuri’a fiye da sau daya, wannan babbar nasara ce.
Aminiya: Ko akwai wata matsala da aka samu game da amfani da na’urar tantance masu jefa kuri’ar?
Anthony: Ai ba zance matsala a wurinmu. Wadanda za su yi maganar koma-baya su ne wadanda amfani da na’urar ya hana su yin aringizon zabe. Amma hakika yin amfani da na’urar na da matukar amfani. Za ka lura cewa yanzu masana’antu da ma’aikatu da dama na amfani da wannan na’uar ta Biometric, wannan zai tabbatar maka da irin amfanin da take tare ita.
Aminiya: Idan ka ce an samu nasara kuma yin amfani da na’urar Biometric na da amfani, me ya sa aka kai hukumar zaben Ghana kotu bayan ta bayyana sakamakon zaben 2012?
Anthony: Ban iya fada maka dalili.
Aminiya: Wacce irin shawara za ka ba kasashen da ke son su yi amfani da na’urar Biometric a zabensu, kamar Nijeriya?
Anthony: Da farko dai su san da cewa akwai na’urorin iri-iri, su zabi wadda suke so. Bayan haka su tabatar sun horar da mutanensu yadda za su yi amfani da na’urar yadda ba za su samu damuwa wurin amfani da na’urar ba.
Aminiya: Zan koma ga tambayar da ka ce ba za ka iya amsawa ba. Za a iya cewa yin amfani da na’urar Biometric ne ya yi sanadin a kai hukumar zabe kotu.?
Anthony: Ba amfani da na’’urar ce ya yi sanadin kai hukumar zabe kotu ba. Yadda ake tattara sakamakon zaben shi ne ya jawo haka. Misali, wadansu jam’iyyu sun tura wakilansu tashoshin zabe don sa musu ido a kan duk abin da ke gudana, am,a sai ba su ba su horo a kan yadda ake tattara bayanan sakamakon zabe ba,da kuma yadda ake tantance sakamakon da aka bayar. Matsalar da aka samu ke nan, amma ba domin na’urar tautance masu zabe ba.
Aminiya: Mene ne maganarka ta karshe?
Anthony: Maganata ta karshe ita ce, wannan sabuwar fasaha ce kuma tana bukatar mutane su yi taka-tsantsan, amma a karshe kowa zai yi hamdala.