Nau’ukan abinci da ya kamata masu cutar sankara su daina ci
Ta kuma shawarce su da su rage yawan amfani da sukari, gishiri, giya da kuma sinadarin caffeine.
Kowacce ranar 4 ga watan Fabrairu rana ce da aka kebe domin bikin ranar cutar sankara ta duniya.
A cewar Asusun Bincike Kan Yaki da Cutar Sankara na Duniya, akwai kimanin mutum miliyan 18 da ke dauke da cutar zuwa shekarar 2008.
- COVID-19 ta sake kama mutum 1,005, ta kashe 24 a Najeriya
- Mutum 3 sun mutu sakamakon fadan kabilanci a Ibadan
Daga cikin adadin, mutum miliyan tara da rabi maza ne, yayin da miliyan takwas da rabi kuma suka kasance mata.
Idan mutum yana so ya ci gaba da rayuwa da cutar, dole ne ya rika cin lafiyayyen abinci yayin da yake dauke da ita da kuma bayan an yi masa aiki a kanta.
Cibiyar Bincike kan Cutar Sankara ta Kasa ta yi bayanin illar cutar da kuma abubuwan da ke sa masu dauke da ita su kasa cin abinci yadda ya kamata.
Hakan a cewarta kan sa mutum ya fara fama da rashin wadataccen abinci wanda daga karshe kan kai ga raunin jiki, kasala da kuma gazawar garkuwar jikinsa wajen yakar sauran cututtuka.
Cin abincin mai dauke da isasshen sinadarin Furotin da kuma kitse na taka muhimmiyar rawa wajen yakar cutar da kuma bunkasa garkuwar jiki.
Cibiyar ta kuma yi bayanin cewa cin abincin da ya kamata yana taimaka wa masu dauke da cutar su zauna lafiya, da karfin jiki sannan kuma su takaita illolinta a jikinsu.
Hakan na da matukar muhimmanci ne saboda cutar kan shafi dandano, tantance kamshi da wari, gamsuwa da kuma damar sarrafa sinadaran cikin abinci.
WebMD.com ta shawarci masu cutar da su nace wa cin abinci mai gina jiki, musamman mai dauke da sinadarin furotin, ’ya’yan itatuwa, ganyayyaki, hatsi da kuma abinci mai karancin kitse.
Ta kuma shawarce su da su rage yawan amfani da sukari, gishiri, giya da kuma sinadarin caffeine.
Kazalika, shafin www.nm.org ya jaddada muhimmancin amfani da ganyakai saboda suna dauke da sinadaran Vitamin C da Potassium da Fibre da Magnesium da kuma Beta Carotene.
Bugu da kari, ana bukatar masu dauke da cutar da su dimanci amfani da tumatir saboda shi ma yana kunshe da sinadaran Vitamin A da Potassium da kuma Lycopene.
WebMD ta kuma jaddada cewa ana bukatar masu cutar su yawaita cin nama mai laushi, naman kaza da kifi da kwai da wake da gyada da madara da kuma yogot.
“Ku daure ku rika shan akalla rabin kofi na ‘ya’ayn itatuwa da kuma ganyakai a kullum. Nau’ukan abinci irin wadannan suna da matukar tasiri ga lafiya, kawai dai a tabbatar an wanke su yadda ya kamata kafin a yi amfani da su. Ku sha ruwa da sauran abubuwa masu ruwa-ruwa da yawa. Kada ku ci naman kaza ko kifin da bai dahu ba sosai.”
Maza da mata da suka kamu da wannan cuta ana shawartarsu da su kaucewa amfani da madara ko nau’inta wacce ba a tace ba.
Gidauniyar Arizona dake Amurka ta jaddada muhimmancin gujewa amfani da abincin da aka soya, ko naman da aka gasa, abinci mai gishiri, mai sukari ko kuma mai maiko.
Kazalika, kayan shaye-shaye masu dauke da giya a cikinsu, abincin da ya soyu sosai da kuma abincin da aka sanya masa sinadaran ajiya duk ya kamata a guje su.