Nauyin kilo 610 ya hana dan Saudiyya fita daga gida shekara biyu da rabi
Wani mutum dan Saudiyya mai nauyin kilo 610 ya kasa fitowa daga dakin kwanansa har tsawon shekara biyu da rabi, yana kwance a hawa na biyu da ke gidansa. Sarkin Saudiyya, Abdullah ya bayar da umarni ga ma’aikatar lafiya ta kasar ta kai shi asibiti a birnin Riyadh don a yi masa amgnai ya rage […]
Wani mutum dan Saudiyya mai nauyin kilo 610 ya kasa fitowa daga dakin kwanansa har tsawon shekara biyu da rabi, yana kwance a hawa na biyu da ke gidansa. Sarkin Saudiyya, Abdullah ya bayar da umarni ga ma’aikatar lafiya ta kasar ta kai shi asibiti a birnin Riyadh don a yi masa amgnai ya rage nauyi da teba.
Khalid Mohsin Shaeri dan shekara 20 ne, an kai Cibiyar Kula da Lafiya ta Sarki Fahd da ke Riyadh. Hukumomin Gwamnatin Saudiyya da dama suka hada karfi wajen fitar da Shaeri daga gidansa, musamman ma sai da aka jira wani gado da aka kera masa a kasar Amurka, kamar yadda Kamfanin Dillancin Labarai na Reuters ya bayyana.
Khaled Mohsin Shaeri, an dauke a jirgin sama daga garin Jizan da ke Kudu maso yammacin birnin Riyadh, a cikin wani jirgin sama na musamman da ke dauke da na’urori, kamar yadda Kamfanin Dillancin Labarai na SPA ya ruwaito.
An baza hotunan wannan mutum mai nauyin gaske, a daidai lokacin da motar daga kaya masu nauyi ta forklift ke fito da shi daga cikin jirgin sama, a daidai lokacin da aka kawo babban birnin kasar.
Sarki Abdullah ne ya bai wa ma’aikatar lafiya umarni daukar mutumin don kai shi asibiti, don haka aka samo masa gado na musamman, bayan da aka yi amfani da na’ura, wajen fito da shi daga gidan da ke a hawa na biyu.
A cewar Reuter, Shaeri yana da dan uwa da ’yar uwa masu kiba da nauyin gaske, amma suna iya tafiya da kafafunsu.