Nawa kake bukata ka iya rike aure?
A yanayin matsin da ake ciki a Najeriya, N70,000 za ta isa a rike mata?
Wai shin Naira nawa matashi yake bukata don iya rike matarsa idan ya yi aure?
Wannan ne maudu’in wata muhawara da wasu matasa suka tafka a shafin sada zumunta na Facebook.
- Kotu Ta Umarci Sarkin Dubai Ya Biya Tsohuwar Matarsa Dala Miliyan 500
- Dalilin Da Nake So A Soke Lefe Da Kayan Daki — Fauziyya D. Sulaiman
Muhawara game da abin da ake kashewa wajen neman aure da bukukuwan da suka shafi kulla shi dai ba bakon abu ba ne; sai dai ga alama hankalin matasa y afara karkata ga abin da ke biyo bayan nema da daura auren.
Aure dai wani muhimmin al’amari ne a rayuwar dan-Adam, kuma a galibin al’adun Afirka da addinan da mutanen nahiyar ke bi, miji ne ke daukar dawainiyar iyali – ma’ana, matarsa da duk ’ya’yan da za ta haifa.
Amma yanayin da ake ciki, musamman a Najeriya, na karancin aikin yi a tsakanin matasa, da tsadar kayan masarufi da sauransu ya sanya wasu ma’abota shafin na Facebook kiyasta cewa idan mutum ba ya samun kudi N300,000 ko N100,000 ko N70,000 a wata kada ya kuskura ya yi aure.
‘Kada ka kuskura’
Ismail Auwal, wani ma’abocin Facebook a Kano, shi ya rawaito cewa Abdulrazak Rogo ya ce, “Matukar mutum na samun kasa da N100,000 kada ya dauko ’yar wani ya mayar da ita matarsa.”
Sannan ya kara da cewa Bashir Aliyu Limanci kuma ya ce, “Ka kara adadin kudin zuwa N300,000.”
Shi ma Ismail din ya goyi bayansu, amma ya rage kudin zuwa N70,000 – a nashi ra’ayin matukar mutum na samun kasa da kudi N70,000 to kada ya auri ’yar mutane.
Kabiru Garba ma cewa ya yi “Tab, N70,000 a wata a dai wannan zamanin gaskiya ba za ta rike mace ba, sai dai kowa da tsarin shi.
“Amma rayuwa a cikin gari ba kauye ba da N70,000 sai a hankali.”
“Gaskiya N100,000 ba albashin da zai sa mutum fara tunanin tara iyali ba ne; a matsayina na gwauro ko N100,000 ba zan karba a matsayin albashi ba,” inji Harun Muhammed.
Sai da taimakon Allah
Sai dai wasu ma’abota shafin na Facebook suna da sabanin ra’ayi a kan wannan batu.
Misali, Aesha Isyaku ta yi tsokaci ne da cewa, “Ya danganta da wane ne mijin, ko [wace ce] matar.
“Wallahi tallahi Isma’il akwai wanda na sani a unguwarmu – yaro ne karami kuma ya janyo aure bayan ya gama NCE din shi – kuma ba shi da wata sana’a sai aikin gidan burodi.
“Suna kulla burodi a leda, ana ba su N700 a kullum…
“Cikin ikon Allah yanzu ya bar wanan aikin yana kasuwa ya zama mai rufin asiri.
“Abin sha’awa kamar ba shi ba; ga cima mai kyau a gidansa, ga sutura.
“Jan hankali: yanzu da ya ce sai ya samu irin wadannan kudaden da wadannan yaran watakila sai dai ya juye su a kwalta.”
Shi kuwa Sen Abba Madugu cewa ya yi, “Ni fa na dade da gane [cewa] wayo da lissafi ba [sa] rike aure.
“Taimakon Ubangiji shi ne ke rike aure.”
Abashen Kano Dan-Mamman ma ya bayyana nashi ra’ayin da cewa, “Ai shi lamarin rike mace ya danganta da yadda mutum ya tashi da kuma yadda ita matar ta tashi.
“Wani kasa da N50,000 ta ishe shi. Wani kuma N500,000 ma maleji zai ke yi da ita.”
Bayan sa’a 24 ana tafka muhawara a kan batun, Ismail Auwalya sauka daga kan matsayinsa.
A cewarsa, “Bayan tattaunawa da Ibrahim Sanyi-Sanyi a waya, na gamsu cewar kowa na da irin tsarin rayuwarsa… [don haka] na yanje ikirarina na baya da na wallafa”.
Ku kuma yaya kuke kallon wannan batu, kuma mene ne ra’ayinku a kai?
Ku garzaya shafukanmu na sada zumunta da muhawara ku fada mana tunaninku. Latsa tambarin Aminiya da ke kasa don zuwa shafinmu na Facebook.