Nawa ’yan siyasa ke batarwa wajen dinka suturar yakin neman zabe?

Galibi a kan dinka suturar mataki-mataki.

Nawa ’yan siyasa ke batarwa wajen dinka suturar yakin neman zabe?

Buhari yayin yakin neman zaben Tinubu a Jihar Legas

Galibi ’yan siyasa sukan yi shiga mai dauke da alama ko kuma tambari na al’adar jama’ar kowacce jiha da suke je zawarcin kuri’unsu da sunan yakin neman zabe.

Alal misali, duk ’yan siyasar da za su kai ziyarar yakin neman zaben wani yanki na Arewa, to sukan sanya sutura gwargwadon al’adar mazauna wannan yanki. Haka kuma abin yake idan yankin ya kasance wani daban da ba wannan ba.

Idan aka yi duba a ziyarar yankin Arewa maso Gabashi irinsu jihohin Borno, Yobe, Adamawa, Gombe da Bauchi, mukarrabai da kuma ’yan takarar shugaban kasa musamman na manyan jam’iyyu biyu da ke kasar nan da suka hada da PDP ko APC, wato Atiku Abubakar da Asiwaju Bola Tinubu, sun yi shiga ta hula dara da kuma babbar riga wadda ta sha dinki na tsamiya ko kuma zubi na zabuni wadanda wasu madunkan sukan kira da aikin aska.

Buhari yayin yakin neman zaben Tinubu a Jihar Legas

Irin wannan shiga ta ta’allaka ne da mutanen wannan yanki, inda sukan yi malummalum da aka dinka da shadda samfurin Wagambari wadda ta sha aiki ko saka irin ta sarakunan gargajiya.

To haka abin yake idan ka duba irin shigar da ’yan siyasar ke zuwa da ita sauran jihohin na Arewa kamar Kano, Zamfara, Katsina, Sakkwato.

A irin wadannan wurare, babbar rigar takan bambanta da wadda suka sanya a yankin Arewa maso Gabashi, illa iyaka a nan tana kasancewa ce babbar riga ta kowacce irin shadda ko yadi wadda galibi aka san mazauna wadannan jihohin da su.

Kazalika, ’yan siyasar sukan yi shiga makamanciyar ta mazauna jihohin Kudancin kasar da zarar sun kai wa yankin ziyara.

Atiku yayin yakin neman zabensa a Jihar Delta.

A kwanakin da suka gabata, Atiku da sauran magiya bayann jam’iyyar PDP sun yi shiga ta atampa tun daga kan wando, shakwara har da jamfa ta wata atamfa mai launin rawaya da ratsi mai ruwan tsanwa da a makuba, yayin ziyarar yakin neman zaben da suka kai Jihar Delta, wato dai jihar da abokin takararsa, Ifeanyi Okowa, yake zaman gwamna.

Mene ne dalili?

Shin ko me ya sa ’yan siyasa ke wannan shiga?

Aminiya ta tattauna da wasu masu ruwa da tsaki a fagen siyasa, inda suka bayyana cewa ’yan siyasar sukan sanya sutura wadda ta yi daidai da al’adar mazauna yankin da suka je zawarcin kuri’unsu ne, domin hakan zai kara janyo hankalin mazaunan su ji cewa an karrama su ko kuma suna da muhimmancin da ba za a juya musu baya ba idan an samu mulki, koda kuwa masu neman takarar sun kasance ba daga wannan yanki ko al’ada suka fito ba.

Nawa ake kashewa wajen dinka irin wadannan sutura?

Aminiya ta tuntubi wani Alhaji Jamilu da ke Kano kuma mai goyon Jam’iyyar APC.

Alhaji Jamilu dai ya ce ba zai fayyace ko nawa yake kashewa ba wajen dunka wa ’yan siyasa suturar da suke sawa ba a wajen kamfe, sai dai ya ce yana yi ne a matsayin gudunmuwa domin idan an ci zabe shi ma a tuna da shi.

Aminiya ta tambaye shi, duk babbar riga daya za ta kai nawa?

Ya ce, “Gaskiya ba zan iya ce maka ga abin da duk babbar riga daya take ci ba, amma nakan bayar da gudunmuwa ta babbar riga ga ’yan takarar APC kuma duk wanda na kaiwa yakan ba ni shaida a rubuce cewa ya karba amma ko sisi ba na karba.

“Nakan dunka babbar riga guda dari biyu ko dari uku ko dari hudu na kai a matsayin gudunmuwa domin idan an ci zabe ni ma a tuna da ni.

“Ko a baya-bayan nan na kai wa Gwamnan Zamfara, Muhammad Bello Matawalle, kuma an ba ni takarda a rubuce ta godiya da tabbacin an karba da hannu biyu.

“Akwai wadanda na yi na bayar aka yi yakin neman zabe a Legas ga dan takarar Shugaban Kasa na APC, Bola Tinubu, na dinka babbar riga kusan 300 kuma babu ko sisin da na karba.

“Hasali ma ba sa ni ake yi ba, kwangila ce wadda na daukar wa kaina kuma ina sa ran zan ci moriyar hakan a gaba.

“Akwai babbar riga wadda nake yi a yanzu wadda da ita za a rufe yakin neman zaben Tinubun a Legas, to ina mai tabbatar maka cewa ta fi duk wadanda na yi a baya kyau da daraja.”

Mun tambaye shi, yadi nawa duk babbar riga take ci?

Amma ya ce, “Gaskiya ba zan ce ba, domin kuwa bandir-bandir na shadda kawai nake saye sai madunkan su rika yanka suna babbar riga babu wani awo da ake tsayawa a dauka.”

Teloli

Aminiya ta tattauna da telan daya daga cikin wasu kusoshin gwamnati a Jihar Kano don jin kiyasin kudin da ake kashewa wajen dinka suturar zuwa yakin neman zabe.

A cewarsa, galibi irin wannan babbar rigar hawa uku ce:

Akwai wadda ’yan takara da gwamnonin da ake je jiharsu yakin neman zaben suke sawa.

Akwai kuma wadda kusoshin gwamnati na wannan jiha suke sawa, sai kuma wadda aka tanada saboda sauran magoya masu uwa a gindin murhu da kuma makarraban gwamnati irin kwamishinoni ko wasu masu rike da mukamai na jam’iyyar da ke yakin neman zaben.

Telan wanda ya bukaci a sakaya sunansa ya ce, irin wadda ’yan takarar da gwamnoni ke sawa takan kai Naira dubu 30 zuwa 45 duk riga daya, domin kuwa akan sayi shadda ta naira dubu biyar duk yadi sannan kuma kowacce babbar riga daya tana cin yadi hudu.

Baya ga wannan, akwai kudin kwalliya da ake yi wa babbar riga mai dauke da alama ko tambarin jam’iyya, wadda sai an yi surfani a jikin duk babbar riga daya sannan ga kudin dinki.

Darajar hular yakin neman zabe — ’Yan kasuwa

Wakilin Aminiya ya tuntubi ’yan kasuwa da masu ruwa da tsaki kan darajar hular da ake sawa wajen yakin neman zabe.

A zantawarsa da wata matashiya mai saka huluna irin zanna bukar, tangaran, kindai da sauransu, ta ce ya danganta da irin darajar zare da kuma shimfidar hula.

Ta ce sukan dinka duk hula kan N8,000 har zuwa N30,000, gwargwadon bukata kuma iya kudinka iya shagalinka.

Wasu masu sayar da hula a kasuwar Kantin Kwari da ke Kano, sun ce duk hula dara guda daya a yanzu farashinta yakan kai naira dubu 14 zuwa sama.

Akwai kuma dara Tonak wadda ake sayarwa daga kan dubu 18 zuwa abin da ya sawwaka, ya danganta dai da yanayin ciniki.